Sashe 88
Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Love You too Takawa, Sarki Dr Ibrahimul-khalil" Ya saketa yana buɗe idanunsa ya zubawa lip's ɗinta idanu a hankali ya ɗan yi murmushin gefen baki cikin firgitaccen yanayi ya suɗe gefen bakinsa wasu maganaɗisun abubuwa suka shiga motsawa a duka jijiyoyin jikinsa, magana yake son furtawa gareta ɗin amma ya kasa, yadda tsakiyar goshinsa ke fidda zufa yasa ta fahimta ta ce "Takawa nawa, ni da yarana, Alhassan Singer kamar Aberdeen Abduljabar Abbas, Alhassan Footballer kamar Abu maleek, Yaa K Dr kamar Dr Abdul-hakeem Bukar Bello, Noha Lawyer kamar Moon, Soha matar malam ce kamar Danejo da Yaa Sheikh Aliyu.." Ya ɗan ware idanu sai kuma ya girgiza kai a taƙaice ya ce "Lahhh" Ta zauna kusa da shi tana kallon sai marairaicewa yake kansa ƙasa daya ɗago suka haɗa ido ya saka hannu ya shafi fuskarta ya ce
"Idanunki azaba ne ga Takawa" Ta ce "Ka fito ka ce kana buƙatar ka" Ya yi Miskilin murmushi bai ce komai ba a hankali ya kama hannunta ya ɗora a ƙirjinsa yana rufe ido sun jima kana ya ce "Blessing Woman, Allah ya saki Aljanna" Kasa magana ta yi sai kama fuskarsa da ta yi tare da fara masa wasu lafiyayyun sumbata.
Bayan wata uku akai bikin naɗa Takawa, tare da bashi sanda da Takofi sai wani haɗaɗɗen zobe. Soha da Noha sun yi wayo tare da yin wata ƙiba gwanin sha'awa yaran sun yi jajur dasu kamar na turawa, Yaa K ya sake girma amma jikin nasa sai addu'a ciwon sikila ya sa shi a gaba daman tafi wahalar da maza, ya kwanta jinya asibiti babu adadi, haka kurum hannunsu ya kumbura ba ciwo ba komai ya ja ruwa daga ƙarshe ya fara kure sai da suka je asibiti akace ciwon sikila ɗin ne ya ƙarya ƙashin hannunsa. Alhassan abubuwa suka faskara a halin babansa abinda ya manta ne kawai bai ɗauka ba, hatta zane sai ya ɗauki Ebook ya dinga zane har cewa yake ya zama Aby da Mimi. Da ƙyar Takawa ya tasaa Ummie a gaba da roƙan ta aure Uncle Isma'il Majeederh hadda kukanta, ita sam gani take raini ne ba don tana so ba ta amince. Rohaan ya yi caraf da Sona ƴar Uncle Isma'il. Lokaci ɗaya akai gagarumin biki na fidda raini ƙasa ta ɗauka suka tattara suka nufi Naija domin a can za'a yi bikin. Ummie da Uncle Isma'il, Fatymerh da Akeeth, Zizi da Jawaad, Badi da Hammad, Sona da Rohaan, bikin daya tara dubban jama'a. A nan Majeederh take jin iftila'in daya faɗawa Abuturab, bayan juyin mulki da sojojin sukai a ƙasar Naija ya samu karayar arziƙi dalili EFCC da suka kama shi, ko mota ɗaya bai tsira da ita ba sai ɗan ragowar kuɗi a banki, gashi duk dare sai ya yi mafarkin Maysoon ta biyo shi tana kuka hannunta riƙe da wuƙa zata daɓa masa, tana zuwa kansa sai Jidda ta shiga tsakani tana rufe shi, abin tun ana ganin wasa harya taɓa ƙwaƙwalwar shi ya zauce duk wata ake amso masa magani a dawanau abin kamar taɓin hankali ya zama kamar MIJIN MATACCIYYA.
Da ƙyar ya samu Takawa da Majeederh suka yafe masa, shi kuma Latifa ta nemi yafiyarsa na abinda tayi masa ta faɗawa babarsa komai da saka hannun Hassenat akai haka duk binciken Latifa ta kasa gano dangin mahaifiyarta domin Alhaji Bashir ya ce ya manta ko sunan babarta domin a irin matan da ake safara ya sameta ya yi mata aika aika, abu ɗaya ya sani tana kama da mahaifiyarta.
Alpha ya ware amma mikin son Majeederh na zane a ransa wanda yake jin shi ne zai zama ajalinsa da kuma sonta zai koma ga mahaliccinsa, ta riga ta zama zanen ƙaddararsa, yana ƙoƙarin nunawa ya mance da ita ne, shi kuma ya nemi Maman Alpha ta daina jin zafin Majeederh domin bata da laifi idan da wacce ta cuce shi bai shige Anti ba, ita ce ta yi masa abinda taɓon shi gogewarsa sai wani ikon Allah masanin komai, suka dawo rayuwa da matarsa Zaleehat tana son shi, ba zata wulaƙanta shi ba, ko dan darajar yaran dake tsakani, yau ta gane kansa gobe sai addu'a, daman kuma rayuwar gidan auren haƙuri yafi jin daɗin yawa. Abbu duk inda zai samu labarin Ruma ya bincika babu har wajen ƴan iskan leges ɗin nan amma shiru,kamar shawo ya ci shirwa, Raihana tana zaune aurenta ya mutu tuni wannan gorin zaman gidan data kewa Majeederh ya dawo kanta.
Majeederh na zaune a bedroom ta yi shiru idanunta akan yaranta wanda gabaɗaya shekarar su guda, Ƙamshin turaren Takawa da ta ji na Boadicea The Victorious ya tabbatar mata da shigowarsa, ta kalle shi taga ita yake kallo hawaye ya sakko mata ya ƙarasa ya zauna yana kama hannunta a taushashe ya jima kafin ya ce "Saboda kina da ciki kike kuka?" Ta marairaice ta ce "Kwanika fa? Yaran nan tausayi suke bani" Ya juya ya kalli beds ɗinsu kana ya tallafo fuskarta yana ɗora tasa akai a hankali can ƙasa ya ce "Muna murna, Takawa na son zuri'a karkiyi fushi kyautar Allah ce" Ta ji kalamansa sun kwanta mata sauran da suke kwanika ya suke ji? Ya ɗora hannunsa a cikinta sai ya yi kamilallan murmushi ya ce "Blessing Woman, you're a darling, ke albarka ce,abar so kin mayaye gidan Khalil da zuri'arki" Ta ce "Mun mamaye dai, ka manta ka ce kai ne kake haihuwar?" Ya shafa kai da idanunsa a laɓɓanta ya ce "Sure" Kafin ta yi magana ya haɗe bakinsu waje guda, can cikin fitar hayyaci ya ji wayar Majeederh na ƙara ya ɗauka ganin sunan Alpha ya sa shi lumshe idanu, bata ɗauka ba har kiran ya katse wani ya sake shigowa Takawa ya miƙe tsaye yana cewa "Pick the call...!" Yana faɗin haka ya fice ta ɗaga ta ce "Assalamu alaika"
"Sannu, muna hanya zamu shigo, ai kuna Naija still?" Ta ce "Eh, kai dawa?" Ya ce "Idan munzo zaki gani" Ya kashe kiran ta sanarwa Khalil bai ce komai ba, ba jimawa suka shigowa, mamaki ya kama Majeederh ganin, Barrister Aliyu Sufyan, Alpha, Akeeth, Hammad, Jawaad ko wanne da matansa wasu da goyo wasu ciki sosai sukai farin ciki, daga gaisuwa Khalil bai sake cewa komai ba, sai an yi abu zai girgiza kai kawai ko ya ce "Uhm" har dare suna gidan. Takawa na zaune a Main parlour shi da Majeederh da yaransu aka kira Khalil ganin Abbu yasa ya ɗaga a hankali ya ce "Subhanallah Gamu nan" A ruɗe majeederh ta ce "Lafiya?" Bai ce komai ba sai ya miƙe not too long ya dawo cikin nagartacciyyar shigarsa tana tsaye sanye da kayanta da hijab yana kama Hannunta ya ce "Muje"
[11/2, 20:11] Ummu: *NIMCYLUV*
*_MIJIN MALAMA_*
Book 2 page 107
Final Episode
ArewaBooks: Nimcyluv
Okadabooks: Nimcyluv
Wattpad: Nimcyluv
Facebook: Na'ima Sulaiman Sarauta
Both Twitter and Instagram.
08119237616.