← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 90

Sashe 54

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta miƙe ta sauya kayan jikinta zuwa English wears basu da maraba da babu, ta zuba uban MORESQUE Midnight a duka sassa da gaɓoɓin jikin nata, ta shafa wani lip's glow irin shi gar na ta “You neva run-away" Baya tayi ta zauna saman kujera tana gani dishi-dishi komai ya tsaya mata zafi da raɗaɗin da zuciyarta ke mata ya shige gaban kwatance, ji take kamar ma numfashinta tafiya yake baya dawowa, jikinta ya shiga rawa haɗi da ɓari, a hankali ta ɗauki wayarta ta sake kiran shi sai ta ji an ce “switch up” Ta yi shiru a fili ta ce “Innalillahi wa'inna ilahir raji'un” Tun wajan 9:20 daya fita har ƙarfe ɗaya bai shigo ba, ta haɗe kanta da qiwwa tare da fashewa da wani irin raunataccen kuka.... Wajejen 2 na dare ta ji ya buɗe ƙofar ya shigo muryarsa da take a nutse ɗauke da sallama, Khalil ya tsaya cak ganin Majeederh durƙushe a ƙasa cikin shigar da ba a ita ya barta ba, ya duba lokaci ya zare idanu gently majeederh ta miƙe tsaye, da sauri Khalil ya juya baya sbd kunya baya son kuma taga how hot he's, domin a buɗe yake a mimmiƙe juyawar da ya yi idanunta ya sauka akan lafta laftan kiss ɗin dake bayansa, hannu ta saka ta ɗan taɓa shi ya juyo suna haɗa idanu ya kwaɓe fuska tare da langwaɓar da kai ya furta "Sorry" kalmar ta fito masa da ƙyar, sai yaga tayi ƙyakƙyawan murmushi while hawaye na sauka daga idanunta da hannu ta nuna masa bayan rigarsa, ya zare ido a fili kuma ya ce "Damn it" riƙe hannun Majeederh clamly yayi ya ce "Listen to me Madam" ta girgiza kai ta ce "No, It's ok" Ya jawota ya rungumeta very tight kamar zai rabata biyu hannunsa ɗaya ya ɗora a cikinta wajan mararta ya ce "Thank you" Ya ji tayi shiru yana ƙara shafa cikin ya ce "Karki saka damuwa a ranki, you are pregnant" Still ya ji shiru sai a lokacin ya fara noticing da sakin da jikinta ya yi, ya ɗagota sai yaga sharaf ta faɗa hannunsa ya shiga bubbuga kumatunta muryarsa na rawa ya ce "Madam! Madam!" She didn't answer because she was already unconscious, her breathing stopped with difficulty, a gigice Khalil ya jata jikinsa ya rungume ta tsam ya ce "I am sorry Madam, I'm so sorry" Ya shiga babbugata sosai amma ko motsi ba tayi ba, bai taɓa tunanin kishinta ya kai haka ba sai yanzu, tashin hankalinsa ɗaya cikin dake jikinta wanda ita kanta bata san da shi ba, yama mance shi likita ne a firgice kuma ya miƙe ganin jini na zuba ta ƙasanta daidai lokacin ya dinga jin kiran waya kuma ya gane number Uncle Isma'il ce, tashin hankali biyu ya haɗe masa ga halin da Jee ke ciki ga kiran da ake a wannan tsakiyar daren. *_Arewabooks@Nimcyluv_* Bayan sun sauka a harabar gidan Khalil ya sake tura wheelchair ɗin fuskarsa ɗauke kwantaccen murmushi, suka haɗa Idanu da Rohaan ya harare shi, Rohaan ya ce "Yaro ya girma" Khalil dai a nutse yake tura ƙyakƙyawar wheelchair ɗin da Bafullatanar matar ke zaune kai cikin wata dakakkiyar abaya mai laushi da taushi, speaking calmly ya ce "Are u okay?" Ya faɗa a hankali yana leƙa fuskar matar ganin tayi saurin riƙe hannunsa lokacin daya gangara da ita zuwa cikin entrance, ta zuba masa idanu ba tare da ta ce komai, Mai martaba Ajlaal Sultaan ya ce "Don mind her, kwana biyu haka rigimarta ke tashi" Khalil ya yi shiru sai kuma ya kwaɓe fuska irin bai ji daɗin nan ba, a haka suka nufi gidan Ƙhulud Arzaan ta dinga kallon gidan cike da sha'awa ganin yadda tsarin yake kamar a Turai a haka suka shiga..... Few minutes Khalil ya sake ɗago kansa with different things in his heart ya ce "hope everything goes well?" Mai martaba Ajlaal Sultaan ya numfashi cike da yanayi na kamala da riƙe yana kallon yadda ƴar tasa take ya mutsa fuska a hankali a taushashe yana fidda zallar kwarjini dake lulluɓe a jikinsa ya furta "Allhamd" Khalid ya jinjina kai, gabaɗaya hankalinsu yana hospital gangar jikinsa ce kawai a nan, amma nutsuwa da wani kuzarin da kan riƙe kan shi da shi ya yi nisa tare da ƙaura a jikinsa, ganin kamar tunaninsa da zuciyarsa ta Kaɗaita da inda suke ya sanya Ƙhulud ce wa أخي أنا" زوجتك" Bi ma'ana 'akhi 'ana zawjatuk. Ya ɗan rausayar da kansa gefe yana watsa hannu clamly ya ce "What?" Ƙhulud tayi dariya ta ce "Kana mijin Malama baka iya larabci ba? Ya zama dole naci tarar Hawwa'u, ina matar ka?" Ya lumshe gajiyayyun idanunsa masu ɗauke da wasu masifaffun sinadarai zuciyarsa na masu nauyi ga wata kyakkyawar faɗuwar gaba dake riskar shi tana shigar dukkan wata ƙofofin zuciyarsa da suka bubbuɗe gabaɗaya tare da amsar fargabar a gaggauce da yanayi na sauƙaƙe wanda yake shimfiɗe har saman fuskar tashi. Ya ɗan fiddo ido ya ce "She's in the hospital" A kusan tare cikin zullumi da yanayi na makake na rashin sanin cikakken halin da zuciyoyin nasu suke ciki, Zaytoon ta juya ta kalli Mai martaba shi kuma ya yi saurin girgiza mata kai a kamalance yana mata nuni da tayi shiru karta ɗaga maganar, Ƙhulud ɗin ma ba tayi magana ba, tayi shiru tana kallon Zoya da Zohal da suke lumshe idanunsu za su yi bacci, Mai martaba ya kalleta ganin yadda ta zuba masa Idanu kamar mai karanto gaskiyar dake zuciyarsa wacce dauriya da kamala ta rufe su ta hana fuskarsa nuna, ya dubeta da kyau a nutse ya ce ماذا تريدين أيتها الأميرة؟ “madha turidin 'ayatuha al'amiratu?” Ma'ana me kikeso GIMBIYA? Ta rirriƙe hannun Ajlaal Sultaan sosai hawaye na bin fuskarta ga zufar dake tsastsafowa daga goshinta jikinta ya yi sanyi ƙallo, kanta dake cinyar Ajlaal ya shafa a hankali, yanayin yadda take marairaicewa Ajlaal zaka fahimci matsananciyar Soyayyar dake tsakaninsu shi da Gimbiya domin tuni ya fara birkicewa ganin yanayin nata ya riƙeta sosai a hankali kuma yake goge mata zufar, Khalil ya zame Idanunsa daga kanta yana daga zaunan kuma ya ɗauki remote ya ƙure Acn dake cikin haɗaɗɗan part ɗin da suke zaune, Gimbiya tayi shiru tana sauke numfashi, a hankali ta juya kallonta ya sauka kan Khalil.... Majeederh na kwance idanunta rufe ba bacci take ba, amma yadda tayi shiru zaka ɗauka baccin take, tunanin abinda ya hana Khalil dawowa asibitin take tun safe, bata son zuciyarta ta raya mata yana wajan Debeka domin fahimtar hakan daidai yake da samun rauni a zuciyarta, jin ƙarar buɗe ƙofa ya sanya tayi saurin buɗe ido tana juyawa ganinta ya sauka akan General Alpha Bello khan, ya yi tsaye cikin sabuwar shigarsa ta farin voyel na ƙanan zane a wannan karan bai saka hula ba hannunsa zube cikin aljihu ya ɗan ƙara kallonta sai ya ɗauke kansa gefe, don tunda ta nemi sumewa data gansa bai ƙara shigowa cikin room ɗin ba, duk da kasancewar yana cikin hospital ɗin, ya nemi waje ya zauna yana danna wayarsa yana jin yadda idanunta ke yawo a kansa, can ya buɗe baki ya ce "Lafiya? Wannan kallon fa? Kina bina wani abu ne ko na taɓa yaudarar ki? Akwai abinda kike so ne wanda kika gani a jikina? Kada ki cinye ni" Majeederh ta ware Idanu a ranta tana cewa "Mr arrogant, a tambayi mutum komai banda hali" Alpha ya ɗago kai gabaɗaya yana kallonta ya haɗe fuska sosai ya ce "Kin sanni ne?" Tayi shiru sai kuma a sanyaye ta ce "Who are you?" Ya kalleta sai ya miƙe gently zuwa inda take ƙwance ya zauna tare da miƙa hannu zai kama nata tayi saurin janyewa tana yaƙe a hankali ya ce "Why? Why are doing this to me?" Ta ware Idanu cikin rashin fahimta ta ce "Me na yi?" Ya ce "Stop answering my questions with a question Zabiya" Tayi masa shiru daman idan masifa ce no 1 ne shi, ya runtse idanu ya buɗe muryarsa na rawa sosai ya ce "You couldn't wait for my return, you married someone else" Da mamaki take kallonsa ta kasa cewa komai ba, ya ce "Me ya sa? Kin taɓa tambayar kan ki rashin dawowata?" Ta girgiza kai Idanunta na kawo ruwa ta ce "Am sorry Yaya, but is no my fault yaya da bakinka ka ce baka so na idan ka aureni zaka iya mutuwa ko ka kashe kanka ko ni" Muryarta ta fara rawa sosai tana shassheƙa ta ce "Na rasa yadda a lokacin ji nake na rasa komai nawa, u left me yaya" Sai kuma ta sunkuyar da kanta tana riƙe kukan dake shirin ƙwace mata abubuwa da yawa suka shiga dawowa mata a kanta kamar lokacin suke faruwa da ƙyar ta ce "Yaya na tashi da kulawarka ban san damuwa ba idan ina tare da kai, tun ina ƙarama kake kula dani ka ɗauke ni da hannayenka, hakan yasa na tashi da soyayyarka na ɗauka kawai zumunci ne, sai dana girma na fahimci saɓanin hakan" Ta fashe da raunataccen kuka, Alpha ya yi shiru a hankali ta ce "Bayan na girma na san sonka nake da gaske, na fahimci ba haka a ranka domin babu alamun soyayyata a wajanka bisa dole na haƙura, sai kuma gashi lokaci ɗaya ka dawo mini da son ka sabo na saka rai da aurenka zan mallake ka, amma ƙaddara ta shata mini layi da samun abin da nake so ka sanya ƙafa ka shure al'ƙawarin da ka yi mini, duk da har lokacin You never said that you love me, you just said that you will marry me and then you went away and left me, na wanzu da ciwo da zafin abun a raina na kuma ƙara jin cewa da gaske na zama mujiya a idanun maza tunda naga aya akan ɗan uwana" General Alpha ya daddafe kansa yana komai na sara masa bai san ta yadda zai fahimtar da ita ba, babu wasu sauran kalamai da suka rage masa a bakinsa, ya sassauta murya ya ce "U misunderstood, ki bani dama" A tsorace ta ce "No way" Tayi murmushi ta ce "Maganar dane, yanzu na jima da share tantanma na gane a cikin maza akwai
Chapter 54 · 0% Book details