← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 90

Sashe 17

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💃💃Ko waye zai zama MIJIN MALAMA?
Idan na so mugunta da kuma jan labarin.... Sai kawai na ɗakkowa Akeeth na bashi auren Malama Majeederh ai shima namiji ne? Idan kuma nagarta nake so sai kawai bawa Sheykh Ajlaal Sultaan? Idan kuma dangantaka nake so sai kawai Alpha ya dawo ranar auren a bashi ita? Idan kuma ramuwar gayya nake so sai Majeederh ta auri Aliyu.... Idan soyayyar gaskiya nake so da kulawa, da kuma dole ki so ni ko zaki mutu love by forch madly love sai kawai na bawa Ibrahimul-khalil, Abraham bad boy auren Majeederh.... Na tsaya da typing tunani kawai nake🤔🤔🤔to ita matsalar ma Abraham yaro ne wai ya yi ƙarami bai isa aure ba.... Congratulations TEAM MAI MARTABA AJLAAL SULTAAN🥰
*#Unexpected*

Cak Khalil ya tsaya saboda abinda kunnenshi ya jiye masa His whole body was shaking, his heart was beating hard, he couldn't believe what his ears were hearing because of surprise. Ya juya a hankali yana kallon direction ɗin limim da kuma bakinsa, a ƙoƙarin shi na son fahimtar meke faruwa? Ya runtse idanunsa tare da riƙe jikinsa Ya Allah What is happening here? why should his ears lie to him? Ya tambayi kansa a zuciya, a hankali kuma ya sake ware idanunsa akan Liman ɗin wanda yake cewa "Ma sha Allah, aure ya ɗauro bisi amintattun shaidu, da kuma amincewar ko wanne ɓangaren, an ɗaura auren Ibrahimul-khalil Denial David da Hawwa'u Abdul'aziz Khan akan sadaki 500k Naira dubu ɗari biyar" At that time, Khalil looked like a madman, especially the way he looked at the imam without even blinking his eyes, abin yake ji da gani kamar a mafarki yake gilma masa kamar reflection wanda ya saba ganin kansa ciki, ya juya ya kalli Mai martaba Ajlaal Sultaan suna haɗa idanu yaga yana yi masa dariya, da sauri ya kalli Uncle Isma'il wanda shi ma Abraham ɗin yake kallo suna haɗa idanu da Uncle I ɗin Abraham ya kwaɓe fuska sai kuma ƙafafuwansa suka ɗauki rawa, cikin nutsuwa Takawa ya miƙe ya isa wajan Abraham dake ƙoƙarin sulalewa yana zuwa Abraham bai tsaya jiran komai ba ya rungume Takawa yana sakin wani irin raunataccen kuka mara sauti wanda Mai martaba ɗin ne kawai yake jinsa, ya kuma ƙanƙame shi kamar zai shige jikinsa, shi tunda aka haife shi a duniya ba zai ce ya yi kuka a gaban mutane har haka ba,He couldn't shake himself from the state of happiness and surprise he was in, ya kasa yarda yau shi ne ya auri Maminsa, Jee ɗinsa, ƴar madara Maluma, Maminsa data raine shi ya rayo da soyayyarta yau ita ta zama mallakinsa ta zama matarsa, He just belong to him ya sani, ya rungume Takawa da kyau yana sauke numfashi da wata iriyar zuciya domin abin ya tsammace shi, tsammaci abinda bakai tsammani ba, ya fitar da rai da Malama Majeederh sai gashi yanzu igiyoyin auren shi sun rataya akan ta, Wow dear Ibrahimul-khalil you're lucky. Suna nan tsaye rungume da juna Takawa na sakin wani ƙayataccen murmushi yana bubbuga bayan Abraham, Uncle Isma'il ya ƙarasu yana murmushi ya ce "Yau naga abin da ya daman mazaje da kuka?" Jawaad dariya yake hadda riƙe ciki ya ce "Lallai yaro ya girma ya auri Maminsa" Khalil yaƙi ɗago kai balle ya tanka haka kurum kunyar Uncle Isma'il ta dirar masa a zuciya. Uncle Bello yana naɗa babbar riga zuwa sama ya ce "What did i miss?" Uncle Ismail ya ce "He's crying" Uncle Bello ya ce "Wanne irin kuka ba daɗin ji, baka son ta ne ko me?" Da sauri Khalil ya ɗago da rinannun idanunsa da sukai wani irin jaa ya yi baya kaɗan yana kwaɓe fuska a hankali ya ce "What, ban so fa?" Yadda ya yi maganar yana zare idanu zaka san maganar ya shige shi ance bai son Maminsa, Jawaad ya ce "Yaro an shigo matakin manya, an zama MIJIN MALAMA" Khalil ya yi murmushi kawai yana girgiza kansa har yanzu Shocked bai sake shi ba, muryarsa can ƙasa baya fita ya ce "Ban kula ka, ranar farin cikina" Uncle's ɗin sukai murmushi gabaɗaya Abraham ya sauya kamar bashi ne Bad boy ba, leader team na Gang ɗin su, har ya tsani kace masa Abraham kawai Khalil ko Ibrahim. Suna nan tsaye Barrister Aliyu ya ƙarasu fuskarsa ɗauke da murmushi ya kalli Khalil yana miƙa masa hannu ya ce "Congratulations brother in Islam" Khalil bai kalle shi ba, bai kuma miƙa masa hannu ba fuska sake ya ce "Thank you" Ganin hakan yasa Barrister Aliyu ya dunƙule hannunsa sai kuma ya fice daga cikin Masjid ɗin, Khalil ya ɗan matsa kusa da Takawa wanda suka magana da wani mutum yana ɗan jinjina kansa, Khalil sai zunguro Mai martaba Ajlaal yake amma bai kula shi ba, daga ƙarshe ya juya gabaɗaya ya sakar masa ranƙwa shi aka, Khalil ya shafa kansa daya cire hular ya ce "Auchhhii, it's hurt" Sai da suka gama magana Mai martaba ya kalli Khalil yana ware idanu a hankali ya matsa dab da kunnen shi ya ce "Why? How?" Sosai ya gane me yake nufi sai ya ce "Not here" Suna haka Abuturab ya ƙarasu tun kafin yazo Khalil ya yi saurin barin wajan. Waje ya samu su Uncle Isma'il da Uncle Bello su Jawaad hadda Engr Junaid suna ta yin pictures kowa da farin ciki a fuskar shi. Khalil ya tsaya yana kallon su, gabaɗaya keɓance kansa yake son yi domin ya yi farin ciki wayarsa ya zaro a aljihu yana ɗan daddannawa sai kuma ya mayar jin Uncle Bello yana cewa "Ibrahim mu shiga ciki ku gaisa da mutane" Ya ɗan kwaɓe fuska ya ce "No! Uncle zuwa yamma" Uncle Bello bai takura shi ba domin ya fahimci shocked ne ya masa yawa har yanzu kuma bai gama yarda dashi aka ɗaura auren ba, Motar su Ajlaal ya shiga suka nufi Bristol Palace Hotel..... Abraham na kwance saman gadon hotel ɗin daga shi sai farar singlet da three quarter tuni ya yi watsi da manyan kayan a wahale, lokaci zuwa lokaci yake mirginawa gefe tare da rungume pillow yana sauke numfashi, tunani yake Majeederh zata amshe shi a matsayin mijinta or not? Zata yarda ta kwantar da hankalinta su kwashi roman soyayya ya kula da ita ya bata tattali ko ya? Ya lumshe idanunsa gabansa na faɗuwa a fili ya ce "Common Khalil, wata ƴar ficikaf mace zaka ji tsoro?" Ya ɗan kwaɓe fuska sbd kansa dake masa ciwo bai son yanayin gabaɗaya, a hankali wayarsa ya fara ringing kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya yi picking tare da yin shiru, muryar Latifa ta sauka cikin kunnenshi ta ce "Congratulations Little, congratulations once again" Ya yi shiru bai ce komai ba ta ce "Na maka murna, Majeederh deserves to have any kind of happiness in life,You deserve to be her true and eternal husband" Khalil dai ya yi mata shiru, Latifa tayi ƙasa da murya ta ce "Yanzu kana da gidan da zaka sata ko haya ne?" Silently yana rufe Idanu ya ce "Haya" Ta ce "Ayya, I feel bad for you, to kana da kuɗin kama gidan hayar? Kuma a nan Lodge Road kusa damu ko Darmanawa?" Kamar Abraham ba zai magana ba yana danna ɗaya wayar tasa ya ce "No, Ranta mini za a yi" Nan na Latifa ta nuna babu daɗi ta ce "Ka bani acct number zan baka marriage gift, sai ka haɗa ko ɗan taimako ka nema wajan mutane ka kama hayar ko?" Nan ma Shortly ya ce "Kam ngd" Har zai kashe wayar ta ce "Yawwa ina zaka kama haya ɗin?" Ya yi shiru alamar tunani can ya ce "Dotsa" Tayi murmushi ta ce "Oh Dotsa can hanyar Tamburawa? Ai kama kaita waje mai kyau kana ji ko? To aurenka da Majeederh mutukaraba ita ce matar rufin asiri, kada ka kuskura duk wahala duk azaba kace zaka saketa ka riƙeta sosai kuci wahalar tare, kamar auren zobe na al'ƙawari haka zaka ɗauki auren yawwa Allah ya sa albarka" Kafin ta ƙara cewa komai Abraham ya kashe wayar idanunsa jajur jijiyoyin kansa duk sun tashi, baya son ya lalata mood ɗinsa na yau amma tabbas da sai yaci uban Latifa Omar yaga wanda ya tsaya mata, Ya jima kwance har aka kira Sallar Azhar ya miƙe tare da shiga bathroom ya yi wanka tare da ɗaura alwala, bayan sun dawo daga masjid ya zauna kusa da Mai martaba yana taɓa kafaɗarsa ya lura Abraham gabaɗaya mantawa yake da Sarki yake tare ya yi ƙasa da murya ya ce "Tell me, i can't wait any longer" Mai martaba ya watsa masa harara bai ce komai Abraham ya girgiza kai ya ce "You made a sacrifice? For me?" Ajlaal ya ce "Who told you that I love her?" Khalil ya yi shiru, Ajlaal ya ce Because of you I came to Nigeria, I made sure you married Majeederh, First love, your heart's choice" Khalil was speechless kallon Mai martaba Ajlaal Sultaan kawai yake with shocke Ajlaal ya ce "Bamu taɓa sonta ba, akwai i have my own reasons na following life ɗinta, tunda nazo Naija nama Uncle ɗinta magana, na nuna masa..." Sai kuma ya yi shiru Khalil ya kwaɓe fuska yana marairaicewa sai bai ce komai ba ya yi shiru yana sauke numfashi, Ajaal ya ce "Ka tabbatar ba dan ita ka musulunta ba?" Khalil ya buɗe ido a hankali ya ce "What?" Sai kuma ya girgiza kawai yama rasa me zaice, daga ƙarshe ya miƙe zuwa bedroom ɗin Ajlaal ya yi kwanciyar nan take bacci ya ɗauke shi cike da wani irin nutsuwa da farin ciki.
Chapter 17 · 0% Book details