Sashe 89
Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Takawa da Majeederh a mota ɗaya wata babba ta zamani black colour, Alhassan da Al'hussain da Yaa K suna mota ɗaya ta bar su Soha da Noha wajen Nanny, sai motar masu kula da lafiyar Takawa Khalil data iyalansa, a haka suka bar gidan jikin Majeederh gabaɗaya ya yi sanyi ta rasa me Mijin nata ke ɓoye mata, ta ɗago ta kalle shi tasan ba lallai ya sake magana ba tunda ya yi kafin su fito can ta ce "Takawa meke faruwa ne?" Ya numfasa a hankali ya juya ya kalleta ba tare da ya ce komai ba ya kama hannunta ya matsa alamar Ki kwantar da hankali, Ganin ta sake ƙoƙarin magana ya rufe mata baki tare da janta jikinsa ya rungume.
Har suka isa gidan Abbu ba wanda ya sake magana, gabaɗaya an sauya gidan zuwa ginin zamani wanda Takawa ya zana da kansa, Majeederh ta sake rikicewa ganin motoci kala-kala a harabar gidan Abbu, bata jira shi ba ta fito shi kuma ya tsaya a motar yana zubawa motar gwarazan mazan yaran nasa ido. Cak ta yi ganin Gawa shimfiɗe a parlor ga Aaliyyah zaune tana kuka ga Raihana da sauran matan familyn Khan, sun zagaye gawar sai kuka suke, Mami idanunta jajur ba kuka take ba amma halin da take ciki gwara ta mai yin kukan da ita, Maman Alpha ta yi shiru idanunta akan mamacin, Yaya Bilkisu, Innati sai maƙota mazan kuma suna ɗaya parlourn. Cikin rashin sanin wanda ya mutun Majeederh ta zube gaban gawar jikinta na rawa bakinta na kakkarwa ta ce "A...a...a Abbu?" Innati ta ce "Ba dai Audil azizu ba, Allah ya tsare shi da yin wulaƙantacciyar mutuwa irin wannan" Majeederh bata karaya ba ta cigaba da zame zanin da aka rufe gawar da shi idanunta ya sauka akan fuskar Ruma wacce ta yi baƙiƙƙirin ta sauya kama ta zama wata ƴar firit da ita, Majeederh ta saki zanin tana rufe bakinta saboda kukan da ya zo mata a fili ta ce
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ruma ce? Ruma ta rasu yaushe? Garin yaya? Innalillahi!"
Ta sake fashewa da kuka cikin wani irin firgitaccen tashin hankali, Yaya Bilkisu ta ce "Awa ɗaya da suka shige aka kira mahaifinku a waya ana nemansa a hukumar hisba, yana zuwa suka labarta masa gawa aka kawo musu tun daga garin Lagos, su kuma suka amsheta a details ɗin da take yawo da shi a jaka, sun tabbatar ciwonta ne ya kasheta da kuma Shaye-shayen data fara babu ji ba gani wanda ya taɓa mata huhunta" Majeederh ta runtse Idanunta tsamtsam tausayin ƴar uwarta ya kamata da kuma dalilin mutuwarta ta.
"Allah ya jiƙanki Rumaisa, Ubangiji ya yafe miki zunubanki ya kai ranki zuwa Aljanna maɗaukakiya" Ta juya ta ce "Me ake jira ba a yi mata wanka ba?" Sukayi shiru Aaliyyah ta ce "Wai tsoran taɓa ta suke ji" Da mamaki take kallon su bata ce komai ba, ta miƙe tsaye ta ce "Akwai ruwan zafi ko? Sabulu? turare?" Aaliyyah ta ce "Eh" Jee ta ce "Aaliyyah ku sauya parlour ki duba handbag ɗina za kiga Kur'ani mai ƴa ƴa ki bawa kowa inda zai karanta" Ta miƙe duka sauran suka bita, su Yaya Bilkisu ma fita sukayi, Majeederh ta zauna cike da ƙarfin zuciya da kuma dakiya ta wanke Ruma tas da taimakon Zaleehat sukai mata sutura, hawaye na fita daga idanun Majeederh ta shiga zuba mata addu'o''in samun rahamar Ubangiji tana zaune, tattausar muryarsa ta fara shiga kunnenta ta hanyar yin sallama sai kuma Barrister Aliyu Sufyan, daga nan sai Akeeth sai kuma Jawaad sune suka kama Ruma tare da sanyata cikin makara, idanun Takawa zube akan Jee ganin yadda take ta kuka idanunta har ya kumbura duk abubuwan da Ruma ta yi mata amma yanzu kukan rashinta takeyi? Lallai tsakanin ɗan uwa da ɗan uwa sai Allah.
Abbu ya ce babu zaman makoki ranan uku za a mata sadaka da bakwai kowa ya tafi gida. Ummie na zaune a wani parlour dake gidan ita kaɗai ce sai Takawa daya shigo ba jimawa ya ɗan shige jikinta, dauriya kawai take amma sam bata son ƙamshin turarensa cikinta wani irin juyawa yake ta ce "Ina Fulanin?"
"Wa?" Ummie ta harare shi domin tasan maganar ce baya son yi doguwa, ta ce "Ka je ka ɗauki iyalanka ku tafi gida dare ya yi sosai, ga Prince Alhassan nan sai jan yaran jama'a yake da faɗa" Takawa ya yi shiru bai san ta inda zai fara mata bayanin cewa Majeederh taƙi sauraren shi ba, ita dole tana nan har sadakar bakwai da sauri yaga Ummie ta ture shi tana riƙe ciki ta nufi toilet kai tsaye wajen sink ta shiga kwarara amai. Takawa ya yi tsaye yana kallon ikon Allah shi dai ya san Ummie ƙalau take tun kafin su zo Naija yana shan tambayarta a waya tana lafiya? Yana tsaye ta fito ta kasa haɗa ido da shi, ya dinga kallon yadda ta sake haske ta yi kyau sosai da wata ƙiba sai kawai ya lumshe idanunsa ya ɗan yi murmushin gefe, Ummie ta ce "Me kakewa lumshe ido?" Ya girgiza kai ba tare da ya ce komai ba ya fita a hanya yaci karo da Uncle Isma'il ya yi saurin juyawa ya bi ta wata hanyar Uncle Isma'il ya samu Ummie zaune tana ganinsa ta ɗan miƙe tsaye ya ƙarasa inda take yana kama hannunta ya ce "Aman kika sake?" Ta yi shiru sai kawai ta shige jikinsa ya rungumeta sosai yana jin zafin da jikinta ya yi ya ce "Kai, bari na kira Khalil ya duba ki the temperature is too high" Ummie ta girgiza kai a hankali ta ce
"Zaiyi noticing ina da juna biyu banaso" Ya ce "Miye baki so ɗin?" Ta ce "Yasan ina da ciki, yasan me na yi" Uncle Isma'il ya yi dariya sosai ya ce "Kuma kina da gaskiya, amma ai ya san ba a shan ciki a ruwa ko? Kuma yasan kina da aure" Wayar Uncle Isma'il data fara ƙara ya sanya Ummie yin shiru ya ɗauka yana sawa a handsfree muryar Khalil ya ratsa kunnen Ummie da yake cewa "Uncle ka ɗauki Ummie zuwa gida, ta sha paracetamol zazzaɓin zaiwa babyn illa" Yana faɗin hakan ya kashe kiran, Ummie ta fashe da kuka ita daga yau ba zata sake bari su haɗu da Khalil ba.
Rayuwa ta fara gangarawa har aka manta da Ruma sai mikin abin dake maƙale a zuciyar Abbu yana ganin kamar shi ne silar faruwar komai, ya dinga neman yafiya wajen Ubangiji. Ko wanne ɓangaren na zaman gidan auren suna yin sane cikin kwanciyar hankali sai abinda ba'a rasa ba, Musamman Fatymerh da Akeeth ya cike mata dukkan gurbin data rasa bai taɓa mata gori na daga ƙaddarorinta ba, da rashin samunta a cikakkiyar mace ta yi kuka sosai ta bashi haƙuri ya ce "Ba komai, ba don haka ya aureta ba kawai sonta yake" Kasancewar shi jinin Yoruba yasa muguwar soyayyar shi ta kama zuciyar Fatymerh bata ganin kowa sai mijinta Akeeth. Haka Zizi da Badi ko wacce rayuwar aure ta yi mata daɗi lokaci zuwa lokaci suna zuwa wajen babarsu taƙi yarda ta musulunta har lokacin. Rukunin Gang team suka sake haɗewa a wannan karan zuwa nagartattun mutane suka haɗa hannu wajen buɗe company ɗaya mai suna MIJIN MALAMA Oil and gas... John yaransa biyu da mai sunan Takawa da mai sunan Majeederh a cewarsa sune ƴan uwansa sun gama yi masa komai a rayuwa.
Ummie ta haifi kyakkyawar yarinya mace zallar kyau na yarinyar ya ɓaci, taci suna Nana A'ishah ana ce mata Diyanerh, haihuwar Ummie da kwana biyar Majeederh ta sauka wannan karan ma namiji ta haifa jajur da shi so ma sha Allah, cikakken Balarabe haka yaron ya tashi suka sanya masa Sunan Abbu ana kiransa Arjun, Idan Takawa Khalil ya juya yaga Yaa K, yaga Alhassan da Al'hussain yaga Soha da Noha ga kuma Arjun sai ya rungume Majeederh yana cewa "Thank you" Daga nan kuma haihuwar ta ɗan tsaya mata ba tare da planning ba kawai daga Allah, tuni ta sauke farali da aikin hajji haka su Alhassan duk sun jima da zama alhazawa.
After 5yrs
Abubuwa da yawa sun faru hadda rasuwar Innati, Bayan Diyanerh Ummie ta sake haihuwar yara twins daga nan kowa ya fahimci haihuwar tagwaye a jininsu yake, rayuwar ta sauyawa Uncle Isma'il albarkacin zumuncin daya riƙe, Aaliyyah yaranta uku ta ɗauki ɗaya ta bawa Latifa suna zaune lafiya har yanzu dai Aliyu bai sake mata sosai ba, he just believed yana sonta tunda ya kasa manna mata takardar saki,ya ƙara zama cikakken lawyer wanda samun ganinsa ma aiki ne, ya tashi daga gidan nan ya koma G.R.A
Jawaad ya zama babban Ɗan jarida (ALLAH YANA GANI). Akeeth kuma yana riƙe da kujerar Gwamna domin harkar Demokrad'iyya ya shiga ba ji ba gani, Fatymerh ta zama first lady. Maryam ta gano asalin waye mijinta Almustapha ta tayar da hankali ya saketa gashi yana sonta kamar rai sai da taga zai zauce ta koma gidansa bayan ta tabbatar ya daina abinda yakeyi. Gidan Uncle Bello lafiya suke zaune Bilal ya dawo gidan da zama gabaɗaya.