← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 90

Sashe 85

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"I won't" Ya furta a taƙaice kafin ya mirgina gefe yana jawota ya ɗorata saman ƙirjinsa, hannayensa rungume da ƙugunta ta baya wanne ya haɗa da nasa ya manne waje guda, bakinsa a kunnenta yana fesa mata numfashi mai zafi ƙamshin kunun na fitowa saboda ko brush bai yi ba, bayanta yake shafawa a hankali har ya samu nasarar ɓalle rigar jikinta ta rage sai Inner wears, jikin Majeederh ya saki domin Khalil ya san duk abinda tafi ƙauna a nutse a taushashe kamar mai raɗa yana ƙasa da muryarsa ya ce "I'm sorry" Ta yi masa shiru ya sake cewa "please" Ta buɗe ido tana kallonsa kafin ta ce "Sorry for?"
"My mistake" Ya mirgina kai yana tallafo fuskarta ya ce "Na miki ihu gaban mutane, babban damuwata gaban yaranmu" Ta ɗan yi murmushi ta ce "It's ok" Ya shagwaɓe mata fuska yana kwaikwayon muryarta ya ce "Kiyi haƙuri i won't do it again, ina tsananin son ki kuma shi ne sanadi ALLAH YANA GANI, and ba laifi na bane"

"Laifi na ne kenan?"
Ta tambaye shi tana tsare shi da sexy eyes ɗinta wanda nan take suka sake sauyawa Khalil lissafi ya kasa furta komai sai lip's ɗinta daya fara zagayewa da hannunsa ta ce "You don't trust me, kana tunanin zan iya cin amanarka ne? Idan zan ci me ya sa lokacin da ake zaton ka mutum banci ba? Sai yanzu, da nake ganin ba zan iya rayuwa babu kai ba? Da nake ganin ka riga ka cike dukkan gurbin zuciyata da soyayyarka, da nake ganin ka zama silar yaye damuwata, sai yanzu da hankalinmu ya kwanta, babba abu kuma ina sonka amma shi ne zaka mini ihu a gaban mutane harda ma John?" Sai kawai ta fashe da kukan shagwaɓa tana buga ƙafa da yarfe hannu tare da girgiza jikinta, hakan yasa gabaɗaya na jikin nata motsawa Khalil ya ƙarasa susucewa ya rarumota ya rungumeta sosai yana sauke wani irin numfashi a kiɗime ya fara sauke mata wasu Single Lip Kiss, breathing ɗinsa na sauka a zafafe, so yake ya rarrasheta amma sam bai san ya zai yi ba, ita kanta Majeederh sai data tsorata, tun tana dauriya ta fara ture shi zufa ta wanke mata jiki a gigice a kuma wahale ta ce "Cikina, marata" Maimakon ya saketa tunda ya samu abinda yake so amma kamar ta ƙara masa ƙarfi ne ya sake mata Leave a Mark Kiss, yana ficewa daga hayyacinsa jikin Jee ya fara saki ta raina kanta yau asalin Dr Ibrahimul-khalil take gani, wasu irin hawayen so da ƙaunar mijinta suka dinga fita daga cikin idanunta, tasan baya hayyacinsa da tuni ya fahimci halin da take ciki kuma daman tarata ya yi ta wannan hanyar yake son rarrashinta can ƙasa ta ce "Ya Allah kada kasa Khalil ya yi sanadin fitar cikin nan" idanunta na rufe hannunta ya saki, gudun ruwan da Khalil ya ji a cinyoyinsa wanda suke fita da zafi ya dawo dashi cikin hayyacinsa, ya zame daga jikinta da ƙyar wani buɗe Idanu ya yi lokacin da idanunsa ya sauka akan bedsheet ɗin da cinyoyinta jini yake fita daga jikinta harda guda-guda a gigice cike da tsoro ya tallafota yana "I am sorry Sexy mama, na rasa tunanina" Da ƙyar ta ce "Ka kira Ummie karmu rasa babynmu khalil....," Wani gudan jini ne ya sake fitowa wanda ya sanya Majeederh ƙanƙame Khalil jikinta na rawa.
[11/2, 20:11] Ummu: Da sauri ya kalli Akeeth ya ce "Boss binsan zaka yi? zuwa can Saudiyya ɗin?" Akeeth ya dinga kallon yaron nasa mai suna Ziyad, ganin baiyi magana ba ya sanya Ziyad cewa "Idan babu damuwa kuma ba zan shiga rayuwarka ba, yau ɗaya ina son ka bani dama na baka shawara a matsayina na musulmi kuma ɗan uwanka, wanda yake ci a ƙasan ka" Akeeth ya ɗan yi gyaran murya hakan yasa driver ya ja suka nufi asibiti, Ziyad ya sake cewa "Ka bani dama please" "Ina jinka Ziyad, amma a cikin shawarar da zaka bani banda rabuwa da Malama Majeederh ok"
Da sauri Ziyad ya ce "Dole a kanta ne, ka saurare ni a karo na farko, ba zaka taɓa nadama a cikin shawarar da zan baka ba" A hankali Akeeth ya ce "Ina ji" Ziyad ya ce
"Kai babba ne, kuma mai hankali kasan menene ya dace da wanda bai dace ba Boss, yanzu menene ribarka idan ka auri wacce bata son ka?" Akeeth ya yi shiru, Ziyad ya É—ora da "Kai ne da matarka harda yara kuna rayuwa ta farin ciki, kwanciyar hankali da jin daÉ—i sai rana tsaka wani ya kawo kai da nufin rusa wannan farin cikin, da nufin rabaku rabuwa ta har abada bayan kuma duk duniya banda iyayenka ba wanda kake so sama da matarka don Allah ya zaka ji?" Akeeth ya rufe ido yana dafe kansa dake juya masa, a zaune yake amma jinsa yake kamar zai kifa, a hankali ya girgiza kansa ya ce "Ba zan barshi ba"
"Good, kuma tayaya kake tunanin Khalil zai barka ka raba su da Malama Majeederh? Idan da wanda zai fara bada shaidar soyayyar da sukewa junansu tun kafin su kasance miji da mata bai shige kai ba, zata kawo shi gidan marayunka, ya yi sati zuwa wata da ƙyar suke rabuwa, balle yanzu da yake ganin cewa ita ɗin matarsa ce? Kasan waye Khalil? Idan ransa ya ɓaci shi da mahaukaci bashi da banbanci, ina tunanin kamar ka shiga cikin hurumin Ubangiji ta hanyar nuna maitarka ta son matar aure, matar wani, kuma ba ƙiyayya tsakanin su balle ka ce" Akeeth kallon Ziyad kawai yake, sosai ya fahimta amma zuciyarsa ta kasa fahimta ko gane abubuwan da Ziyad ɗin ke faɗa masa a nutse ya ce "Amma na riga shi son ta, tun a lokacin da take kawo shi gidan marayun nake son ta, i don't know what comes over me dana kasa fuskantar ta da soyayya wallahi"
"Hakan yana nufin ita ɗin ba alheri bace gareka, ita ba kowa bace face ƙaddararka (Your destiny)" A hankali ya ce "Destiny? Fate? Ƙaddara kuma?" Ziyad ya jinjina kai ya ce "Ko shakka babu, Majeederh is your destiny ita ce ƙaddararka, duk abinda Ubangiji zai jarabci bawa da shi har yake wahalar da shi to tabbas abun nan shi ne ƙaddarar shi, kuma kar ka bari hakan ya yi tasiri a zuciyarka akwai mata da yawa a duniya masu ilimi, aji, kyau, da duk wasu Qualities da kake buƙata" A taƙaice Akeeth ya ce "Qualities ɗin Malama Majeederh da ban yake, she's different from others, daban take da sauran matan, kawai na yi sake ban taɓa zaton Abraham zai girma ya ce yana son Majeederh ba, ban taɓa zaton zata iya auren shi ba, na ɗauka za ta yi tunanin yarintar shi ta dubi ƙanƙantar shi" "Me zaka nuna masa a yanzu Boss? Dame zaka fi Khalil ɗin? Da shekaru ne dai kawai, su kuma shekaru are just a number" Akeeth ya kalli Ziyad kamar yana son gasgatawa, Ziyad ya girgiza kai ya ce "Kuma shi namiji a duk inda yake namiji baya ƙanƙanta, zanen sunan shi na namiji zai ta kasancewa cike da iko, kamar yadda Ubangiji ya faɗa a cikin Alkur'ani, suratul Nisa'i, maza gaba suke da mata zasu iya jagorantar su a komai, don Allah Boss karka raunata zuciyar Khalil yana tsananin so da ƙaunar matarsa, yadda ya shaƙu da matarsa ko da iyayensa bai shaƙu ba, ni nake bibiyar shi nake ganin komai, yana da ɓoyayyen sirri fitar shi kawai ake gani, amma yana da wani irin Qualities wanda ba ko wanne namiji ke dasu ba, yana yin abu don Allah shi ya sa bai damu daya faɗawa jama'a waye shi ba, yadda ba a haifeka mahaifa ɗaya da Majeederh ba, haka ba zaka taɓa mutuwa saboda baka sameta ba, believe me" Akeeth ya ce "Abraham bashi da hankali, yana da zuciya bai cancanta da zama Mijin Malama ba, ina tsoran watarana ya yi mata illa nafi kowa sanin waye shi wallahi, Ziyad kar kaga laifina ko ban auri Majeederh ba, kawai ta samu wanda zai dace da ita but Majeederh ba tayi deserving auren mutum kamar Abraham ba, duk wahalar nan data sha" Ziyad couldn't speak, ya kasa magana gabaɗaya sai kawai ya ja bakinshi ya yi shiru, hospital suka nufa aka bawa Ziyad gado saboda karayar hannunsa yana buƙatar resting bed.
Chapter 85 · 0% Book details