Sashe 80
Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Ina son shi tun ban san yana duniya ne ko ya mutu ba? Ina son shi tun baya cikin rigar musulunci, ina son shi tun kafin na san cewa jininmu ɗaya, ina son shi..." Ta kasa ƙarasawa saboda wani irin abu daya caki zuciyarta, can ƙasan zuciyar tana jin kamar bata kyauta mata yadda ta buɗe sirrin da babu wanda ya san da shi ba, daga ita sai zuciyarta wacce kuma ita ce ma'adanar ajiye wani ingantaccen sirrin hijabin rayuwarta bakiɗaya.
Wata kunya ta ji ta lulluɓe ta, tare dayi mata hijabi wa gangar jikinta, tana jin inama wajen da take zaune ya tsage ta shige ciki? Amma ina! Duk yadda ta kai da yiwa bakinta linzami a yanzu bata da ƙarfin qiwar ci-gaba da riƙe hakan, raunatacciyar zuciyarta ta kasa riƙe kanta da cigaba da iya ajiye sirrin da yafi ƙarfin ta, an jima ana ruwa ƙasa na shanyewa, kamar yadda ta jima tana ajiye surruka da yawa, amma duk yadda takai da riƙe zurfin cikinta a yanzu bata da kuzari balle ta hub'ɓasa riƙe hakan.
"I love my husband Khalil! Irin son da ba zan iya furtawa ko gamsar da wanda yake tsagina, ji, ko saurarena ba, zuciyar dake son shi da gaskiya ita kaɗai tasan how much i love him" Ta goge idanunta tana riƙe yanayin da take ji da dukkan kuzarinta da ajin da take da shi, cikin nuna jarumta ta ce "Ina raye, ina numfashi kamar kowa, ina gani,ina ji, amma gani nake tamkar matacciyya ce ni a rami, haske nake ciki amma duhun zuciyata nuna mini yake kamar dare biyu ake!. Ban san cewa akwai wani abu da ake halitta a jikin rayayye ba, sai da na fahimci bayanni akwai halitta a jikina ZUCIYA, Na rasa sukuni na rasa meke mini daɗi a duniyata, zurfin cikin da nake da shi ya sanya ba kowa ya fahimta ba, gabaɗaya zaton jama'a JINKIRIN AUREN dana samu shi ne raunin dake raunata jaririyar zuciyata; zato ne kawai kuma mara inganci, tsammanin so da ƙaunar Abraham ita ke damuna, na ji kunya i have been ashamed, idan na tuna ɗan dana raina shi zuciyata ke so! So ɗin ma na aure" Ta kasa ƙarasa maganar saboda nauyin da kalaman sukaiwa halattaccen harshenta sai ta yi shiru kawai tana rufe ido.
"Ɗan uwana General Alpha Bello khan! Shi ne mutum na farko daya fara so na a duniya, ni kuma Dr Ibrahimul-khalil Abraham shi ne first love ɗina daga nan duniya har lahira, an ce so makaho ne (Love is blind) amma bana gani saboda a kullum da Idanun zuciyata nake son shi, yaushe na fara jin haka mene dalilin har yanzu bani da cikakkiyar amsa ni da kai na, tunani fal ya yiwa ƙwaƙwalwata murfi, tun a baya na furta ƙaddarori ne suke zagaye dani, ɓoyayyun mane mana da rashin sanin wanda zai zama mijin malama ya sanya na rasa madafa, sai dai komai na da farko yana da ƙarshe, kamar yadda tayi silar rusa farin cikina haka tayi silar haɗani da abokin rayuwa,iya hakan kaɗai zai iya sawa na yafe mata zunubanta idan ina da tabbacin tuban da zata yi" Khalil na tsaye kamar an dasa shi, kalaman Majeederh sun ɗaure masa jijiyoyin jikinsa, suna neman kassara masa zuciya, ya rasa kuma a wanne bigire ko tubalin zai ajiye wannan zancen nata mai shirin tarwatsa masa zuciya? A hankali ya sake duban lokacin yaga yaci ace suna airport yanzu gashi already John ya shige da su Alhassan, jin ƙafafuwansa na neman kasa ɗaukan gangar jikinsa ya sanya ya jingina da bangon wajen yana mai zuba mata narkakkun idanunsa masu cike da wasu kalar zantuka wanda baki ba zai iya furtawa ba, sai dai gangar jiki tayi aikinta wajen nuna zahirin abinda zuciya ke ciki.
Mutumin ɗazu ya sake kallon Majeederh cikin yanayi na damuwa a hankali ya ce "Na yi sake, ɗan zaki ya girma why? Me ya sa kayi mini shigar sauri haka Khalil? Kasan yadda nake son matarka kuwa? Me ya sa tawa ƙaddarar da zuciyar ta rasa wacce zata so ko ƙauna sai MATAR AURE? Matar Auren ma da nasan Khalil ba zai taɓa sacrifice a kanta ba?" Ya riƙe kansa da hannu bibbiyu saboda juya masa da yakeyi a zaune yake ji yake kamar zai kifa saboda masifaffan tashin hankalin da yake ciki, zufa ta shiga yanko masa a fili ya sake furta "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ubangiji idan Majeederh alheri ce ka gaggauta kashe aurenta da mijinta na aureta, i don't care da shekarunta, Ya Allah; soyayya da matar aure? Matar Dr Ibrahimul-khalil Abraham? Anya alƙiyamarsa bata kusa tsayawa ba?" Duk ya firgice ya fita hayyacinsa he looks so old amma ba mai lura da hakan saboda wani irin arziƙi da kwarjini, ya zaro hanky ya dinga share zufar dake tsastsafowa daga goshinsa tana sauka a fuskar shi. Jajere ta kalli Majeederh ta ce
"Mun sha ganin mutane ko nace mata da dama, wanda suke ganin kuskure ne ko rashin dacewar ko zubar da aji ne ka auri wanda ka girma, musamman irin tazarar girman naku ke da Dr Ibrahimul-khalil Abraham, ke ya kika ji kuma ya kika ɗauki abun? Ya surutun jama'a ya yi tasiri a zuciyarki?" Majeederh ta yi murmushi cikin tattausan harshe da kalami mai daɗi ta ce "Tunani akan cewa zaka burge mutane, wannan abu ne da ba zai taɓa yiyuwa ba, ko da ace rayuwarka zaka bada a kan su; ko da ace gaskiyarka zata fasa ƙirjinka ta fito,sam sam ba zasu yabeka ba, yafi maka ka saurari zuciyarka a kullum, mutanen da suke kewaye da kai sune suke sare maka quiwa a yayin da kaso aikata wani abu,sai kayi nasara a rayuwa sannan kowa ke son ƙulla alaƙa da kai, babu haramci akan auren wanda ka girma idan zai girmama ra'ayinka, ku girmama na juna, yana da wadata, da zuciyar nema, yana da kyakkyawar mu'amala abinda ake buƙata kawai nagarta da cancanta, idan gaskiya zaka faɗa, duk gaskiyarka ba zaka kai Sayyiduna Abubakar ba, duk ƙaryarka ba zaka kai Musailabatul kazzabu ba, munafurci sai Abdullahi ɗan Ubayyu ɗan salo, ƙarfi sai adawa girman jiki sai samudawa, muni sai Julaibibi, matar da akafi so a duniya ba kamar Nana A'isha matar Annabi Muhammad S.A.W, ƴar da akafi so a duniya babu kamar Nana Faɗimatu, Mulki sai Annabi Sulaimanu, kuɗi sai ƙaruna, talauci sai Mus'ab ibn Umairu shi ne wanda ya mutu likkafani bai ishe shi ba, idan taurin kai mutum yake ji da shi akwai su Ƙuddaru, duk iskancin da mutum zaiyi a duniya ba zai kai Hamana ba, a fito na fito da Allah sai shaiɗan, shi daman ba mutumci ne da shi ba, ya ce tunda aka fifita shi akan ɗan adam tabbas sai ya halakar da rabin su, Ubangiji kasa mu dace muyi kyakkyawar ƙarshe" Gabaɗaya suka amsa da amin. Kowa jikinsa ya yi sanyi Khalil dai wani irin nutsuwa yake ji idan ya kalli Majeederh kuma ya tuna matarsa ce sai yaga bashi da wani sauran buri a duniya. Ta gyara zama a hankali ta ce "To kuma duka wannan sai mutum ya tsaya girman kai don wanda zaka aura ko yake sonka yana ƙasa da shekarunka? Idan zanen ƙaddararku iri ɗaya ne fa? Idan iya rubutu ne ba kamar Annabi Isa, abi Annabi sau da ƙafa sai su Sayyiduna Abubakar Saddiƙu, a bada rayuwa saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama sai Umar Farouk, a yin kyauta sai Sayyiduna Usman Zannur, ayin aike a isarwa da Annabi saƙon shi sai Gadanga ƙusar yaƙi Sayyiduna Aliyu, to da yawan mutane suna take abinda yake farilla suna mai da shi sunna, sunnar ma wasu take ta suke, ban wani ji abu mai kama da damuwa ba saboda babu wani challenges dana samu game da hakan" Gabaɗaya suka jinjina kai cike da gamsuwa.