← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 90

Sashe 14

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

zaune tana azkar kamar daga sama taga mutum ya shigo hankalinsa a tashe ta yi saurin miƙewa tsaye kafin tayi magana ya miƙa mata envelope ya ce "Idan gari ya yi haske ki je gida na miki saki ɗaya, ki yi haƙuri amma wallahi Allah ina son ki, Allah da Manzonsa su ne shaidata i don't even know what comes over me, ina abu madly kawai na ji bani da nutsuwa idan ban sake ki ba, i don't mean to hurt you anymore, wlh ina son ki kuma ki saka a ranka watarana zan dawo" Tunda ya fara magana take kallonsa jikinta sai rawa yake da kyarma lura da yanayinta ya sanya ya jata jikinsa ya rungumeta sosai idanunsa cike da hawaye ya ce "I so much loves you Jiddo, i love you with all my heart and soul amma wallahi idan ban sake ki ba zan samu salama a raina ki yafe mini" Sai a lokacin kuka ya ƙwace mata ta ce "Me ya sa? Wacce irin ƙaddara ce wannan Abuturab? Me ya sa zaka wulaƙantani gabaɗaya watanmu nawa da auren, zaka sanya na shiga jerin matan da za'ana lissafin yawan auren su, me na yi maka haka don Allah ka yi haƙuri kace wasa nake Innalillahi wa'inna ilahir!" Wani irin kuka take kamar zuciyarta zata fita jiya ta gama waya da Uncle ta ce lafiya lou suke amma yanzu ta koma ta batun saki? Jikinta har jijjiga yake shi kansa Abuturab kukan yake ya rungumeta sosai a jikinsa Allah taga zuciyarsa na son Jiddo ɗinsa Ubangiji shi ne shaidar shi "I am sorry, please Hawwa'u ki yafe mini" Kamo fuskarta ya yi trying to kiss her for the first time tayi saurin janye jikinta, babu abinda ta ɗauka sai wayarta ta yi waje, securities basu hanata fita ba, tana zuwa titi ta samu napep ta shaida masa inda zai kaita, tayi shiru sai ajjiyar zuciya take saukewa har suka ƙarasa gidan Uncle Isma'il ɗin mai napep ya dinga magana firgigit ta ce ta dawo tunaninta tana sakkowa ya ce "Kuɗin fa?" A hankali ta ce "Bari na amso" Ganin yanayinta ya ce "Kiyi sadaka da su sbd Manzon Allah" Ta ce "Ngd" Uncle Isma'il na zaune shi da Anti da Jawaad da Sona daman sun saba kullum da sanyin safiya sai sun haɗu waje ɗaya, da sauri ya miƙe tsaye ganin Majeederh kamar an cillota Ya ce "Hawwa'u lafiya?" Ta kasa cewa komai sai jan numfashi da take ya amshi envelope ɗin hannunta, wani irin baya ya yi zai faɗi Jawaad ya riƙe shi ya zube yana faɗin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Abuturab ya cucemu amma babu komai kansa ya cuta, laifinmu ne da muka bashi ƴar mu bayan bai cancanta ba, laifinmu ne da muka bashi ke bayan baki dace dashi ba, wlh tallahi zai san ya yi da ɗan halak" Ya kalli Majeederh ya ce "Da zarar kin yi idda ki sanar dani" zuciyarta tayi mata nauyi sosai da ƙyar ta ce "Bani da idda" Uncle Isma'il da Anti suka kalli juna, tuni Jawaad ya fice daga cikin Parlourn shi da Sona da mamaki Anti ta ce "Kina nufin tunda kika je babu abinda ya haɗaku?" Majeederh tayi shiru Anti ta jinjina kai ta ce "Ya cika tantiri a ƴan iska shi no 1 ne, kenan bai yarda dake ba all this day's? Kenan ƙyanƙyamin haɗa jiki yake dake" Uncle Isma'il ya yi murmushin takaici ya ce "Wallahi wallahi a gobe zan ɗaurawa Majeederh aure da duk wanda na yi niyya" Da sauri ta ce "Uncle please na haƙura da auren" Ya wani kalleta ya ce "Ba zaki ƙare rayuwarki a haka ba, dole ki yi farin ciki kamar kowa dole ki rabauta da miji mai son ki da ƙaunarki, Majeederh buɗe kunnenki da kyau zan baki zaɓi, da Mai martaba Ajlaal Sultaan, da Barrister Aliyu Sufyan, da kuma ɗan abokina Junaid wakike so?" Da wani irin sauri ta ce "Ajlaal kuma Uncle? Mijin Ƙhulud? Aliyu mijin Latifa? Wlh Uncle duk duniya ko zan mutu babu aure ba zan taɓa auren mijin Bestie ba ai cin amana ne" Anti ta ce "Ji shasha? Bashi ne ya ce yana son ki ba? Ko Ubangiji ne ya haramta hakan?" Majeederh na kuka sosai ta ce "Mijin Latifa? Bani da Aminiya sama da ita..." Sai kuma ta saki kuka sosai Uncle Isma'il ya ce "Tashi ki je, ai Ajlaal ɗin jiya ya nemi appointment dani nace masa kin yi aure to Allahamdulillah ba zai taɓa komawa Saudiya ba sai dake, na yaba da halinsa nutsuwarsa da nagartar shi ya faɗa mini yadda ya jima yana son ki tun a Misira" Zatai magana ya daka mata tsawa ya ce "Ban waje, wallahi sai na nunawa Abuturab ni ma ɗan iska ne kuma ɗan yau, zan nuna masa baki rasa mijin aure ba" Yana faɗin haka ya miƙe tare da ɗaga waya ya fita.... Majeederh ta kasa sukuni ita dama a barta ba wani aure daga sakin nata zaa ƙara ƙaƙaba mata wani auren? ta rushe da kuka har gari ya gama haske tana kuka sosai, tunda Uncle ya fita kuma bai dawo ba gashi har wajan huɗu na yamma, tana zaune abin duniya ya yi mata zafi aka buɗe Ƙofar tare da shigowa Sona ce ta ce "Anti wai kizo ana kiranki a parlour" muryarta bata fita ta ce "Waye?" Ta watsa hannu ta ce "Ban sani ba" Tana faɗin hakan ta fice da sauri, Majeederh ta jima kafin ta ɗauki vail tayi rolling kanta tunda yanzu ta daina saka liƙab, a hankali a sanyaye tayi waje ba zaka taɓa cewa tayi 35yrs a duniya ba, tana shiga parlourn taga ba taga kowa ba, a hankali ta sake dubawa tsaye ta ga mutum ya juya mata baya yana sanye da wata gezner ɗin shadda amy green ta amshi jikinsa sosai ta haska fatarsa hannunsa ɗaya zube a aljihu ɗaya kuma yana rungume da Baby Khalil dake bacci abinsa a hankali ta ce "Kai ka ke kira?" Domin bata gane waye ba zuciyarta na bata maybe Junaid ɗin ne ya kwaso yaƙunannun ƙafafuwan shi, jin shiru yasa ta saki tsaki domin kwana biyu faɗa take ji sosai ta juya zata shige ta ji sautin kamilalliyar muryarsa mai taushi da ratsa kunne mai cike da nutsuwa da Ilhama ya ce "Amincin Allah ya tabbata ga ruhin Ibrahimul-khalil...... *Like i always say and always emphasize, things are not always what they seem, Duk abinda kake zargi karka yanke hukunci a kansa sai kayi bincike, ba ko wacce kishiya ko stepmom take kansa cewa azzaluma ko macuciyya ba.. Akwai masu zuciyar musulmi wanda babu tsatsa a cikinta, akwai soyayya ta gaskiya akwai ta algus, akwai mai tsayawa a rai akwai mai gundira..Never and never judge a book by it's cover idan kuma ba haka ba you might spend the rest of your life regretting... Kuyi ta turo ƙudundunanniyyar dubu ɗaya amma kuna bawa mutum dubu ɗaya as free🤓to ai ko ɗan-gote akewa haka ya tafka zabgegiyar asarar balle Sarauta. Ni ba zan zagi ko Allah ya isa ba, ba kuma zanta surutu ba akan abu ɗaya ba, balle bakina ya yi tudu a barni da siyan mansileta.*
Chapter 14 · 0% Book details