Sashe 69
Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washegari suna zaune a parlour, lokacin ma dai tattaunawa suke dake kuma weekend ne, a hankali ta yi sallama ta shigo, suka kalleta Maman Alpha ta haɗe fuska, Latifa ta shigo tana tura wani tsohon mutum a wheelchair, suka dinga kallon mutumin Abbu kamar ya ganeshi sai kuma ya manta ina ya san shi. Maman Alpha ta ce "Mene ya kawo ki yau kuma? Maza tashi ki fita" Tana kuka ta ce "Don Allah ku saurareni, hakan zai sanya ku ƙara fita daga duhun da kuke ciki ta wani ɓangaren" Maman Alpha za tayi magana Uncle Bello ya ce "Bari muji meke tafe da ita ko?" Latifa Omar ta ce "Banga laifinku ba, na cancanci ko wane irin hukunci, son zuciya da kwaɗayi da kuma baƙin ciki ya jani zuwa cikin kabarina tun kafin lokacin mutuwata, ban kasance ƙawa Aminiya ta gari ba, duk abinda ya samu Majeederh ni ce sila amma ba komai ya zama laifina ba" Ta kalli Abbu ta ce "Abbu ka tuna wannan? Wani Alhaji Bashir da kuka yi maganar auren Majeederh akan Deal? Zai baka kuɗi ka bashi auren Majeederh?" Su Uncle Isma'il gabaɗaya suka kalli Abbu shi kuma ya dinga kallon Alhaji Bashir, Latifa Omar ta ce "Shi ne wannan, ga nan ya karɓi nasa hisabin duniyar, ka hana shi auren Majeederh bayan ka amshi kuɗin shi, akan gurɓatacciyar zuciyarsa ya sace Majeederh tare da reping nata, hakan ya faru ba tare da saninta ba, domin an gusar mata da hankali" Tayi ƙasa da kai ta ce "Maman Alpha idan kin tuna sanda bamu ga Majeederh ba tsayin sati har tace mana farkawa tayi ta ganta a asibiti to a lokacin akai reping nata, babana ya shirya hakan" Gabaɗaya suka kasa magana, Yaya Bilkisu ta ce "Ke mene haɗin ki da shi? Bayan Malam Umaru babanki?" Ta ce "Ni Adopted child ce, nima Shegiya ce bana da uwa shi kansa bai san wacece babata ba, yana da yara sunfi 30 yayi amfani da arziƙin shi ya yaudari ƴan mata da zawarawa da yawa, rabin yaran shi duka sikila ne kamar yadda Baby Khalil ya kasance sikila, Mijin Malama baya da alaƙa da baby khalil banda ta Kasancewar shi ɗan uwa, suna kama ne da Dr Ibrahimul-khalil saboda kasancewar, shi da Majeederh are cousins, baby khalil is my younger brother" Abbu ya kasa motsi, bai taɓa baƙin cikin kasancewar shi uba irin yau ba, yana ina duka hakan ke faruwa ne? "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" A fili ya ce
"Nawa ne kuɗin" Latifa Omar ta ce "Ba kuɗin ake buƙata ba yanzu, yafiyar Majeederh ni da mahaifina muke so, abubuwa sun mana yawa, duniya ta juya mana baya sai data bari muka gama jin daɗinta, naci amanar aure data mijina gashi yanzu nida haihuwa sai kallo amma yanke mini mahaifa, duka abubuwan dana shiryawa Majeederh ya dawo kai na, hatta aurenta da Khalil ni ce sanadi nayi zaton bashi da kowa, a gari kawai yake yana gantali, shi da gang team sai nayi zaton zata sha wahala idan ta aure shi, ashe bokana ya rufeni bai faɗa mini asalin waye Dr Ibrahimul-khalil mijin Malama ba" Innati ta miƙe tana dungure kan Latifa ta ce "Annamimiya, algunguma ƴar maza mai warin zina" Kuka kawai take, Alhaji Bashir baya motsi saboda paralyse shi kansa kuma sikila ɗin ce da shi. "Na yafe miki, dake da shi, but it's over between us" Latifa ta ce "Na sani, kinfi ƙarfina kin mini nisa, don Allah don Annabi ki bani baby khalil na riƙe na dinga kallon yaro a gabana ko zan ji daɗi" Majeederh ta ce "Allah ya sauwaƙa, ki ɗauka bashi da haɗi daku, zan ma nesanta shi daku" Maman Alpha ta ce "Ai yara kike so? Sanda kike ta zubar da kyautar da Ubangiji ya yi miki bakya tunanin zaki iya son haihuwa Nan gaba? Hoooo ƙaaasa! An yafe muku tashi kuje" Fita sukai jiki a sanyaye Abbu ya dafe kansa dake juya masa.
A hankali Khalil ya juya kujerar da yake zaune, bluetooth a kunnen shi yana jin komai dake faruwa, domin a jiya sai daya sanya wata na'urar É—aukan sauti a gidan, ya kuma saita ta, idanunsa sukai jajur. John ya ce
"Mene amfanin ɓoye kanka ne? Yana da kyau su san mijin malama is still alive" Khalil baiyi magana ba, sai jijiyoyin kansa da suka fito tare da yin ɗoɗar a saman goshinsa, idanunsa sukai jajir John na lura da yadda naman jikin Khalil ke rawa, gargasar jikinsa ta mimmiƙe tsaye tana zubewa. Har John zai yi shiru sai kuma ya ce "Mene amfanin zuwa Orphanage ɗin nan kace zaka yi rayuwa cikin yaran da kake taimakawa?" Khalil ya miƙe tsaye yana dafe kansa John ya miƙe ya ce "Ko wajan Ummie ne ka....," Bai ƙarasa maganar ba yaji Khalil ya ɗauke shi da mari ya damƙi wuyansa ya haɗe da jikin bango duka jikinsa rawa yake idanunsa sun firfito waje da ƙarfi ya ce "Shut up!" Sai kuma ya saki John Khalil ya dafe kansa a gigice ya ce "My head" Daidai nan Faɗimatu ta shigo da basket kyakkyawar yarinya cikin kamilalliyar shiga, John ya ce "Wife stay right there" Faɗimatu ta kalli John wanda sunan shi tuni ya koma Othman Zannur. Ta ce "Dear Yaya Khalil na kawowa abinci fa" John ya ce "Wife i said ki tsaya nan ko" Ta tsaya tana kallon Khalil durƙushe, John ya kama hannunta suka fice tare da rufe ƙofar, babban Orphanage ne, gidan marayun ya haɗu Khalil tun yana asalin bad boy ɗinsa ya gina, Faɗimatu a gidan ta tashi itama har zuwa lokacin da John ya aureta, yara ne sosai a gidan Khalil na mutuwar son su kamar rai haka kowa na Orphanage ɗin. Khalil ya jima zaune kafin ya miƙe tsaye ya ɗauki bottle water ya zubawa tsakiyar kansa, kamar ya kira Zaytoon ko Mai martaba Ajlaal haka yake ji, amma ya ɗauki niyyar sai ya yiwa kowa hauka duk wanda ya shiga rayuwar Majeederh dame ƙoƙarin raba shi da ita more especially GENERAL ALPHA BELLO KHAN. tsayin wata guda kenan kullum Khalil yana zuwa bedroom ɗin Majeederh, sai asuba yake guduwa ya razana Uncle Bello hade da General, Majeederh kuma taƙi yarda ta tare, ta yarda zata rayu da ruhin Khalil tunda yana sanyata cikin farin ciki, kuma har yanzu a tunaninta a mafarki yake zuwar mata, tayi wani irin kyau haske da ƙiba Maman Alpha har mamaki take, cin abicinta ya ƙaru shi da kan shi Khalil ya fahimci haka, har wata guda ba wanda ya san labarin Khalil na raye! Even his mother, Aaliyyah bata ƙasar ma bakiɗaya ita da Barrister Aliyu ya ɗauketa sun barwa Latifa gidan.
Yau ma kamar kullum Khalil ya hauro ta katanga ya sanya fararen kaya voyel ne fari tas da shi, kai tsaye direction ɗin da zai kai shi bedroom ɗin Majeederh ya nufa, ya zuge glass ɗin window ya diro, abinda bai taɓa gani ba ya gani, ya ganta kwance ta rungume Alhassan dake ta kuka zai sha tea cikin dare tana bashi kuma ya tarwatsa cup ɗin saboda ya ji haushi, baccin da ya yi kenan bai sha ba, Khalil ya zubawa fuskar Alhassan idanu ganin wata mahaukaciyar kama da suke da yaron, nan da nan ya fara loosing control ɗin shi, so da ƙaunar yaron ya wanzu a zuciyarsa, ya ƙarasa bakin gado ya zauna, a hankali ya kifa kansa tare pecking kumatun Alhassan yana buɗe idanu yaga yaron ya kafe shi da Idanu, sai kuma ya ɗauke shi ya rungume yaron kamar yasan babansa ne ya ƙanƙame shi yana sauke ajiyar zuciya, sun jima haka kafin Khalil ya goya yaron abayan shi dake Alhassan ɗan fitina ne irin babansa ya ƙanƙame shi, Khalil ya kama window ɗin ya dira yana jin Alhassan yana kyalkyala dariya a haka ya fice da yaron goye a bayansa...
[24/09, 8:05 am] Sdy Auwal Gstc: *MIJIN MALAMA*
*BOOK 2 PAGE 96*
Arewabooks:
Facebook:
Instagram:
Tictiok:
Wattpad:
Okadabooks:
*Searching Na'ima Sulaiman Sarauta, to find out my account in all social network.*
*If you want to talk to me directly, find me on Instagram or Facebook👑*