← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 90

Sashe 57

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ya numfasa bayan ya ɗan kurɓi ruwan da aka bashi mai sanyi sbd jikinsa dake rawa bayyane. Ya yi shiru na wani lokaci kafin ya ce "Ba zan iya cewa ɓatan su plan ne ba, garkuwa ko akasin haka, nasan dai akwai dalili wanda _Only God knows!_, Hakan ya sanya mini tsanar Nijeriya bakiɗaya, tun bayan barinmu ban taɓa zuwa ba sai dalilin Majeederh, mun rasa biyuni tun suna shekaru 6 a duniya lokacin Rohaan shekarar shi 4, daga nan ban san mene ya faru ba, sai bayan shekaru wajan 30 Ubangiji ya bayyana mana Gimbiya, ba baki ba ƙafa, bata cikin hayyacinta haka muka sameta a ƙofar masarauta, bamu da masaniyar aurenta banda yanzu, nasan tunda ta fara dawowa daidai take iya buɗe idanu ta zauna saman wheelchair bata da walwala kullum cikin kuka take, ciwon yau dab na gobe daban, tana yawan zane wanda ban san yadda akai ta zama ƙwararriyya a harkar zanen ba, ta zana baby boy, ta saka _I love u_ wani lokaci ta zana babban kuskure ta saka masa wuƙa a ƙirjin ban taɓa tsayawa na yi noticed me hakan ke nufi ba sai yanzu da gaban ku ta kira sunan Mr President da inda yaronta yake, kila bayan Khalil yana da wani ɗan maybe kuma dai Khalil ɗin ne wanda take nufi" Ya yi shiru yana mai da numfashi, tunda uwarsa ta haife shi bai taɓa magana mai tsayin hakan ba, har wani yaji-yaji ƙirjinsa yake na azaba. Mijin Malama baya fahimta sbd malam da shocked, ya kuma kasa gasgata abinda ke faruwa. A hankali Abbu dake jingine jikin kujera ya ce. "Kafin rasuwar Fulani ta bar mini WASIYYA ga yaranta, ta shaida mini yadda na yi zaton ita Bafullatana ce to ba haka bane, bata da mantuwa ba kuma zata taɓa mancewa ba, sace su akayi lokaci guda bata san su waye ba, amma taga mata da yawa, babu mamaki masu safarar mata ne a tunanin Abbu; sun shiga cikin jeji sosai sai motar su ta tsaya a nan kuma, they have been attack in the middle of the forest, ta ce; bata san mene ya faru ba sai farkawa tayi ta ganta cikin Fulani na garin Gombe, tayi rayuwa dasu ba tare da sun san wacace ita ma, haka ta zauna har tsayin shekaru goma sha biyar daidai lokacin dana aureta kenan, bata haihuwa ba sai da tayi shekara 25 domin tayi ƙanƙanta da haihuwa, har sannan bamu san asalinta ba" Abbu ya yi shiru a hankali kuma ya ce "Hatta ni ɗin nan, kawai tazo da gwala-gwale a jikinta wanda bani da tabbacin Fulanin sun san muhimmancin su gaskiya, sanda Ubangiji zai amshi rayuwata sannan ne take faɗa mini cewa idan Allah ya ƙaddara zuwana Saudiyya naje Palace na basa photon zan samu cikakken bayani, ta faɗa mini hakan ne domin bata san yaranta su tashi da kaɗaici na rashin dangin uwa, kamar yadda ta tashi ba danginta ba kuma wanda ta sani" Idanun Abbu ya cika da hawaye sosai ya ce "I was ashamed, I didn't become a good man, I couldn't fulfill my wife's will" Hawaye masu zafi suka saukar masa ya yi saurin ɗauke kai muryarsa na rawa ya ce,I failed as a father; I was not a good father, I humiliated my daughter and turned her into my investment" Ya sunkuyar da kansa ƙasa ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!I ruined Majeederh's life" Kowa na wajan sai da ya ji tausayin Abbu ya ƙara cewa "I failed as a father!" Uncle Isma'il ya ce "U won't, duk abinda ya faru ƙaddara ce wacce ta riga fata, Ubangiji ya riga ƙaddara hakan baka da laifi, duk abinda ka yi baka cikin hayyacinka an sanya tunaninka da ƙwalƙwarka a kwalba rufe, idan da wanda ya yi asara ni ne wanda auri mace mai tsanani son zuciya kowa yasan yadda kake so da ƙaunar Majeederh" Abbu ya girgiza kai kawai, daman ba sosai yake magana ba idan ya tuna wai da bakinsa ya tsinewa Majeederh sai ya ji duniyar ta masa zafi. Zaytoon ya kalli Gimbiya ta ce "Ur turn, bamu labari" Gimbiya tayi shiru tafi ƙarfin seconds arba'in ba tayi ko motsi ba, babu alamar zata tanka can ta ce "Ya faɗa muku, ya fini sanin komai" Ta faɗa Idanunta a gefe tana kallon Khalil da ya yi lamo jikin matarsa kuma ƴar ruwarsa ta jini, Mr President ya san da shi take ya yi kamar bai ji ba, jinkima da taurin kai ya haɗu waje guda wanda Khalil ya yi gadon ko wanne daga wajan uwa da kuma uba. Uncle Bello kallon kowa yake yana son ganin waye zai fara sauke izza ɗin shi, Innati ta ce "Tur ƙasshi; gobara a gefe, kawai ku kaiwa juna hari, to wlh tallahi iblis ne kawai mai wannan izza ɗin da girman kan ai kuna ganin dai yadda ƙarshen shi bai kyau ba" Innati ta ce "Kai shugaban ƙasa ka fara bamu labari ai sarauta ba wasa ba ta take komai billahi" Yadda Gimbiya bata motsa ba haka Mr President ba wanda ya kalli ɗan uwan shi, can ya miƙe tsaye ya ce "Bani da lokacin ɓatawa a nan, kamar yadda ta faɗa haka ne Khalil ɗanta ne, ita ce babarsa kuma ni ne ubansa" Gimbiya tayi wani miskilin murmushi tana girgiza ƙafa ta ce "What are you afraid of? Ko kuma...." Da sauri Dad ya kalli Gimbiya ya ce "Jidda" Ta miƙe tsaye itama tana murmushi idanunta tar a kansa ya ce "Karki manta you are still my wife" Ta kalle shi sosai clamly ta ce "Zan sauke maka girman kan ka" Ya ce "Baki da zarra, ba a haifi mai iya sauke mini girman kai da jinkimata ba babu shi" Khalil kallonsu kawai yake ganin kamar zasu daku kuma wai sune iyayen shi, what kind of parents they're? Ya miƙe tare da miƙawa Majeederh hannu ta kalle shi ta kasa cewa komai, idanunsa jajur kamar gauta naman jikinsa na wani rawa ya ce "Zo" Ta miƙe tsaye ya damƙe hannunta tare da nufar waje Uncle Isma'il ya ce "Khalil ina zaka?" ba tare daya juyawa ba, ya sake damƙe hannun Majeederh kamar zai ɓalla biyu rai ɓace ya ce "Idan duka su biyun suka sauke girman kansu, suka faɗa muku yadda suka haɗu, da aure suka haifeni ko babu sai mu dawo, muna son juna; i love my wife zan ci-gaba da amsa sunan Mijin Maluma, suna iya kashe junansu idan sun so" Yana faɗin hakan ya nufi waje Gimbiya ta ce "Criminal" Dad ya ce "Da wasa kika faɗi waye ni zan kashe yarinyarki dake wajena, Abraham has a sister, su tagwaye ne kamar yadda kuke da ƴar uwarki, rana ɗaya kika haife su ni na ɗauketa tun a labour room, sbd wannan ranar na yi miki al'ƙawari daman ni ne wanda zai fara sauke girman kan ki, kin san waye ni sarai tun kafin na aureki, idan ki ka yi kuskuren faɗawa kowa asalina na rantse da Jesus sai na yanka wuyan ƴarki" Da sauri Khalil ya juyawa ya kalli Dad ya ce "Before you kill my sister, let me kill you first" Yan faɗin hakan ya saki hannun Majeederh tare da nufar inda Dad ɗin yake....

NIMCYLUV
[12/09, 11:29 pm] Sdy Auwal Gstc: *MIJIN MALAMA*

*BOOK 2 PAGE 83*

*Arewabooks@Nimcyluv* 83

Bari na muku recommending book's nawa.
Chapter 57 · 0% Book details