← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 90

Sashe 2

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kukan ta ya shiga ratsa dukkan wata jijiya dake kan His Excellency Abu-turab zuwa tsakiyar ƙwaƙwalwar shi, me ya sa ta kuka har haka? Bata son shi ne ko yaya? Ko kuma kukan farin ciki ne ta same shi a matsayin mijinta? He couldn't understand why she was crying, deep down na zuciyarsa yana jin faɗuwar gaba. A hankali ya nemi waje ya zauna saman kujerar dake parlourn ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa, ya jima nan zaune He was thinking about where to start?? Ya miƙe yana gyara zaman babbar rigarsa ya nufi Main parlour ya samu Uncle Isma'il zaune shi da Jawaad ya zauna yana rusinawa ya ce "Sannu Uncle" Uncle I ya ce "Yawwa Ur Excellency, har ka fito? Fatan lafiya? Ta dai fito ko?" Ya jinjina kai cikin nutsuwa ya ce "Eh, daman nace yanzu zamu ta fi ne?" Uncle I ya girgiza kai ya ce "To ni dai san samu ka tafi da matarka, tunda babu amfanin wani zaman tana ƙarƙashin ikonka a yanzu, to amma kasan bidia'a irin ta mata yanzu sai ka ji wannan surutu, kuma ni ma a karan kai na ina son sai mun zuba mata furnitures ɗin ta da komai ai ba a kai ta haka ba" His Excellency ya ɗan kalli Uncle I can ya ce "No need Uncle,I have fixed the part where she will sit, added new furniture's that was ordered from Turkey" Uncle Isma'il ya yi jim sai kuma ya girgiza kai ya ce "I don't think that would be possible, gwara dai ka bari akai mata na iyayenta wanda za mu yi, daman ai responsibility ɗin mu ne" His Excellency kallon Uncle I kawai yake bai san yadda zai masa bayani ya fahimta ba. Ganin hakan yasa Anti data fito daga bedroom ta nemi waje ta zauna tana ɗan murmushi ta ce "Ba aikin lada zamu hanaka ba, kasan mu mata muna da gutsiri tsoma, ina tsoran watarana a goranta mata rashin kayan ɗakin ace kai ka yi mata komai" A hankali Abuturab ya ce "Haba Anti, ko ban auri Majeederh ba zan mata komai, plx na yi niyya" Ta girgiza kai ta ce "Baka san mata ba ne Ur Excellency, musamman dangin miji kaɗan daga cikin halinmu ne gori" Ya lumshe idanunsa ya buɗe calmly ya ce "Oh, a bari na tafi da ita, after that sai ku kawo mata tunda kun matsa" Uncle Isma'il ya ce "Better, hankalina sai ya fi kwanciya da hakan" Anti ta ce "Amma kayi mana alfarma, ko zuwa Magriba ne sai ka dawo ku tafi not now" Abuturab ya ce "if you are more comfortable with that, Allah ya kaimu" Ya miƙe tsaye Uncle Isma'il ma ya miƙe suna haɗa hannu ya ce "Thank you, Uncle" Daga nan ya fita yana rufe Idanu, sbd daman bai gama warkewa ba ya matsa dole sai ya zo. Tun kafin ya ƙarasu P.a Hammad dake tsaye shi da Jawaad suna hira zaka ɗauka abokai ne, sbd Hammad he's so funny and nice person friendly to everyone. Driver ya buɗewa His Excellency Abu-turab back seat ya shiga ya zauna, Hammad ya ce "Jawaad see you soon" Ya ce "Ok Dear bye" driver yaja motar bayan Hamma ya shiga gaba, slowly suke tafiya bisa umarnin Abuturab ɗin. Majeederh har yanzu tana zaune bakin ƙofa, tana jin kamar bata kyautawa Abuturab ba na rufe ƙofar da ta yi amma gabaɗaya she's Uncomfortable da shi, zuciyarta ta kasa ganinsa matsayin mijinta na sunna, what should I do?“ Think, Majeederh” Zuciyarta ta bata amsa, ta ƙara sunkuyar da kanta kamar ƙaramar yarinyar, her heart broke, she hugged her knees even righter. Nothing hurts like they words, maganganun mutane da surutun su akanta suke damunta, taya zata ya fewa Abraham? Duk duniya ta tsane shi wallahi bata ko ƙaunar jin sunan shi balle sake ganin mai kama da shi. Kukan Baby Khalil ya sanya ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi inda yake tana zuwa ta ɗauke shi, haka kurum ta samu kanta da ƙura masa idanu, wani kyakkyawan bugu zuciyarta tayi sbd wani mahaukacin kama da yake sake yi da Abraham, ya juye sak Abraham komai da komai musamman yadda yake tsotsar lip's ɗinsa da saurin kwaɓe fuska, tayi saurin rufe Idanunta,tare da rungume Baby Khalil a hankali ta ce "Allah ya isa, ba zaka taɓa ganin daidai ba a rayuwarka, Ubangiji ya rusa maka farin cikinka kamar yadda ka rusa nawa, Allah ya hanaka kwanciyar hankalin kamar ka hana nawa kwanciya Ubangiji ya raba ka da iyayen...," Anti data murɗa ƙofa ta shigowa da spare key ɗin dake hannunta tayi saurin cewa "Subuhanallah! Ya isa haka" Kalmar da ta tsayar da Majeederh daga mummunar addu'ar da take akan Abraham. Ta nemi waje ta zauna idanunta akan Baby Khalil tana ƙara ganin kammminsa da Abraham ɗin kafin ta ce "Why? Wannan muguwar addu'ar ta mece Majeederh?" A hankali ta ce "Ya rusa mini rayuwa Anti" Anti ta girgiza kai kawai kafin ta sauke numfashi ta ce "Idan Abraham ya lalace still ke ya lalacewa tunda uban ɗan ki ne khalil, kina ganin yadda suke muguwar kama" Majeederh ta haɗe fuska tare da yin ƙasa da kanta. Anti ta ɗora da cewa "Bai kyauta, bai kyauta, bai kyauta amma hakan baya nufin ki yi mummunan alkaba'i akan shi, idan ki ka ce kin barsa da Allah kaɗai ya wadatar, wlh duk wanda ya buɗe baki ya ce ya barka da Allah to mutum ya shiga uku, no need ki yi wannan addu'ar ko dan Khalil ɗan ki plx, Majeederh ke malama ce kin fi kowa sanin me ya dace da wanda bai dace ba, Majeederh Ubangiji ne ya amshi addu'armu ya dubi halin da kike ciki ya haɗaki da miji na kece raini, kaf familyn Khan! Babu wanda ya yi dace da miji irin naki" Ta ɗan yi shiru tana ƙara girgiza ƙafa ta ce "Wlh yanzu baki da wanda ya shige Abuturab, yana son ki sosai Majeederh ki yi ƙoƙarin kyautata mu'amalar ki da mijinki, ki duba yadda idanun duniya ke kan ki ko? Kada ki yarda ki bada wata ƙofa da zaku samu matsala da mai gidanki yanzu shi yake da iko akan ki, yi na yi bari na bari, ki riƙe uwar mijinki hannu bibbiyu da sauran dangin miji, babu ruwanki da kowa balle a ƙara saka mini wani tension ɗin kizo jininki yana mugun hawa zuciyarki ta buga a iska, ƙaddarar data same ki ita take ta trending a duniya kiji na faɗa miki bawai iya Kano ko Nigeria ba, da kin shiga Google ki Twitter za kiga shi ne the most trending news" Gaban Majeederh ya faɗi ta runtse Idanunta, ita kam taya zata daina tsinewa Abraham? Babban takaicinta wai ɗan cikinta shi ne yaga tsaraicinta? Ya yi mata Fyaɗe ya tuzarta ta a idanun duniya shikenan yaga komai da komai nata duk irin killace jikinta da take, takaici ya sanya ta ƙara runtse Idanunta ta nemi hawaye ta rasa. Anti ta ce "Kuma da kike ta tsinewa Abraham akan me? Sbd baki yadda ƙaddara ba? Kada ki tsawaita ƙiyayyarki akan shi domin abin da ka tsana watarana shi kakewa mugun son da ba zaka iya controlling kanka ba,I am advising you as a mother and not your uncle's wife, ko da wasa kada ki faɗawa kowa matsalarki sai wanda kika yarda da shi, Abuturab ɗin nan ya fi Abbu a wajanki, Abbu ya kureki shi ya amsheki hannu bibbiyu da ƙaddara data faɗa miki yanzu ne lokacin daya dace ki kwantar da hankali ki samu nutsuwa da mijinki Majeederh" Ita dai Majeederh was speckless ta kasa cewa komai. A hankali ta ce "Anti Abbu ya tsine mini, kada na lalace" Anti ta girgiza kai ta ce "A'a in sha Allah ba zamu ga wannan rana ba, zai sakko ne, naso Abuturab ɗin ya bari an ɗan gyaraki amma ina, ko arba'in ma kiyi sai ki tare" Da wani irin sauri ta ce "Kamar bani da gata Anti? Yau ɗin nan zan wani bisa" Anti ta ce "Hakan ma ce Allahamdulillah, gata kowa kina da shi gaba da baya" Tana faɗin hakan ta miƙe bayan ta amshi Khalil daya koma bacci tana cewa "a sauya masa suna, uba Khalil ɗa Khalil?" Majeederh ta haɗe rai ta ce "Uwa kawai yake dashi" Anti bata sake cewa komai ba ta fice daga bedroom ɗin. Grandpa na zaune a parlour shi da wasu manyan mutane, ya ɗaga kai a hankali idanunsa ya sauka akan Abraham dake tsaye kamar kurarre ya zubawa gefe ɗaya jirkitattun idanunsa wanda sukai wani kala. Grandpa ya kalli mutanen ya ce "This discussion has come to an end. We will meet tomorrow morning at the office" Suka miƙe tare da kwasar ducoments sukai waje, Grandpa ya miƙe yana isa inda Abraham ke tsaye frm head to toe yake kallonsa ganin gabaɗaya ya sauya kamar bashi ba, ya yi sanyi ba zafin ran nan, shi ya ɗauka da gaske ya samu matsala a ƙwaƙwalwar shi, shi ya sa bada shawarar kai shi can asibitin mahaukata ashe depression ne kawai. Zai kama hannunsa ya ji ya ce "I want a plane that leaves in an hour to Germany" Grandpa ya yi murmushi, so Finally ya haƙura da Majeederh kenan? Ya haƙura da auren Mamin tasa? Ya ce "Right now my grandson" Wayarsa ya ɗauka ya yi danne-danne na wasu daƙiƙo kafin ya ce "Done, nan da 30 minutes jirgin zai tashi daman" Abraham bai kula Grandpa ɗin nasa ba ya nufi upstairs kai tsaye, Grandpa na zaune ya ganshi ya fito cikin sabuwar shiga nrml shiga ya yi ba wacce ya saba ba, Camouflage-print cargo trousers da Gymashark sports t.shirt kansa na nan a hargitse har gefen goshinsa duk ya cukurkuɗe amma hakan bai hana wani irin ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious fita daga jikinsa ba, ya shiga sakkowa daga upstairs ɗin fuska kamar ya ce ya shiga uku, hannunsa zube cikin Aljihu sai ka ɗauka wani babban mutum ne he just 20yrs ko gama rufata bai ba. "Ka shirya tafiya wajan Denial kenan?" Ya yi masa banza, murmushi Grandpa ya yi tare da miƙewa yabi bayansa, back seat suka shiga bakiɗaya driver ya jasu zuwa airport sai da sukai nisa ya
Chapter 2 · 0% Book details