← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 90

Sashe 77

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A hankali ya miƙe cike da nutsuwa yana gyara zaman sunglasses ɗin fuskarsa, yadda fuskarsa tayi jajur zaka san kukan da Majeederh take ya taɓa zuciyarsa da gaske, ba zai iya jurewa ba domin yana gab da samun matsala a kamalance ya fice ta ƙofar baya daidai nan kuma ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious ya karaɗe wajen hakan ya sanya director da camera man ɗin da suke kusa ɗago kansu zuwa gare shi, if they are not mistaken wannan shi ne mijin Malama, the ex-president son, jikan masarautar Saudiyya hamshaƙin ɓoyayyiyar mai arziƙin nan na ban mamaki, mamallakin kamfanoni kala-kala, uban marayu wanda ba a san adadinsu ba, Dr Ibrahimul-khalil Abraham Kspider, Mijin Malama. Khalil ya haɗe fuska sosai domin baya ɗaukan raini, sai kame kansa yake kallo ɗaya kuma a tsanake zaka yi masa ka gano ƙwayar idanunsa da take iri ɗaya data Majeederh, Khalil hannunsa zube cikin Aljihu ya yi wani irin sahihin kyau mai fusgar hankali musamman yadda yake lullumshe Idanu, ya juya kaɗan idanunsa ya sauka akanta ta kifa kanta a saman armchair tana kuka a hankali Silently, shi bai sam bai son loosing control ɗinsa akanta wajen wanda bai ma san miye so ba, balle damuwa da su, ya jima da sani kuma da fahimtar cewa ita ɗin dai, ita ce Rauninsa (His Weakness). Ba sauri yake ba yanayin yadda jikinsa ke motsawa so romantic and sexy zaka ɗauka sassarfa yake idanunsa buɗe amma kamar a rufe suke yadda yake lumshe su, ba zai iya cewa ga wanda suke wajen ba idanunsa Majeederhn kawai suke gane masa, bata yi aune ba ita dai ganinta tayi tsaye gaban mutum hannunsa ɗaya zube a bayanta ɗayan kuma ya ɗora a kafaɗarta yana zubawa fuskarta wani irin kallon na mai kama da tuhuma, ta kasa ci-gaba da kallonsa saboda idanunsa da sukai mata kaifi da gaske ɗin har lokacin kuma hawaye na bin fuskarta ta sake ɗago idanunta taga bai motsa ba ko ƙifta idanunsa bai ba ita kawai yake kallon bakinta na rawa ta ce "Ma...ma.." ta kasa furta komai saboda yadda taga ya buɗe mata Idanu sai kuma ya ɗan matse kafaɗarta irin "Speak up" ɗin ganin tayi shiru ya sa ya damƙi hannunta tare da fara tafiya da ita zasu bar daƙin da ake recordings shirin na Mata a yau.
"Man please" A taushashe ya furta "Uhm" ta riƙe hannunsa ta ce "Calm down dear" Rinannun idanunsa ya buɗe mata sosai ba tare daya furta komai ba ta kwantar da murya ta ce "Why are you here?" Ya ɗan saketa yana girgiza kai da hannu ya nuna mata kanta sannan ya nuna mata idanun dake fita daga cikinsu a taushashe kamar zai mai raɗa ya ce "muje" ta ce "Bamu gama ba" Ya zare mata Idanu ya ce "Ba buƙata" Baki ta buɗe za tayi magana ya yi saurin cewa "Hawwa'u!" Ta kalle shi a gigice tsoro ya mamaye zuciyarta bata san cewa tana jin shakkar Khalil ba sai yanzu, idanunta ya sake ciko da hawaye wanda kuma shi ne baya so harga Allah, Hafsat A.b Hamza ta ce "Sorry for the interference" Ko inuwarta Khalil bai kalla ba ya riƙe hannun Jee zasu bar wajen Hafsat ta ce "Matarka abar so ce, banga laifinka ba Dr Ibrahimul-khalil, amma zan so kayi mana afuwa zuwa sanda zamu ƙarasa wannan program ɗin please, mutane da yawa suna jiran irin wannan ranar don Allah don Annabi albarkacin azumin dake bakinka" Khalil har lokacin bai kalli Hafsat ba, idanunsa akan Majeederh ya durƙusa daidai kunnenta yana warming bayanta kamar zai rungumeta ya ce "Kome zakiyj, ki tuna" Tayi saurin kallonsa a taƙaice ya ce "Ki tuna, I love you!"
Yana faɗin hakan ya fice daga cikin wajen, Majeederh ta ji kamar ta bisa ta ji dalilin wannan fushin nasa? Bata da wani option wanda ya shige ƙarasa program ɗin, ta koma ta zauna zuciyarta ta kasa nutsuwa a wajen, ta kalli Jajere jin tambayar da tayi mata ta ce "Mutanen da muka yarda dasu harlau sune suke son ganin bayanmu, as i was saying ƙaddara ita tayi tasiri a rayuwata, bisa gudunmawar ƙawa da matar wan babana, bana da masaniyar cikin dana samu wanda jama'a suka dinga Allah wadai dani, amma a yanzu abu ɗaya zan faɗa muku wannan cikin ɗan da aka haifa ƙanin Latifa ne, mahaifinta shi ne uban baby khalil, ina lalube cikin duhu ina ganin ɗan uwana ya guje ni ranar aurenmu ashe shima ƙaddara ce ta faɗa masa, saboda kawai ba a son ganin farin cikina, he left me sanda nake tsananin buƙatar shi, ina da tarin masoya a ɓoye ba tare da na san waye zai zama Mijin Malama ba, JINKIRIN AUREN dana samu shi ne ya zame mini sanadin haɗuwa da inuwata, kuma na yarda wani jinkirin alheri ne,In addition, you can't run faster than your shadow, slowly but surely" Ta riƙe hawayen idanunta da kyau ta ce "Na yarda ɗan uwana ba rabona bane, bayan wannan ƙaddarar mahaifina ya tsine mini yana ganin tamkar ina sane nayi cikin shege nake playing game a gidansa, abin mamaki ina haihuwa manema suka fito kala daban daban, a ciki hadda mijina a yanzu na auri Abuturab ina tunanin na samu inuwar da zan raɓa na samu nutsuwa ashe kura ce da fatar akuya, ba zance ga farin cikin dana samu a gidansa ba ko sau ɗaya, abu ɗaya na sani taimakon da ya yi mini, At his house, I was diagnosed with depression, na kamu da depression hakan yasa na kasa bacci a ko wanni dare tsinuwar mahaifina ke amsawa a kunnena, ya d'aureni yana bani maganin bacci saboda ciwon kan da nake, he turned me to a drunkard...," Wani irin rikitaccen kuka ta fashe dashi wanda ya sanya Halima Ben Umar ta toshe bakinta saboda kukan da yazo mata, wanne irin hali mata suke ciki ne? Wacce kalar ƙaddara ce wannan irin ta Majeederh? Ta jima tana kuka kafin ta ce "Naga rayuwa amma yanzu Allhamdulillah! Ya zama tarihi" Halima Ben Umar ta ce "Ya akai mijinki ya amsheki a yadda kike?"
"He believed in destiny, Mijina; daban yake" Majeederh ta bata amsa a taƙaice, Halima Ben Umar ta ce "Mene alfanun auren wanda kika girma? Kuma tayaya kike iya yi masa biyayya duba da cewa tazarar da kika basa mai yawa ce?"
A duka tarin tambayoyin wannan ita ce tambaya mafi tsauri da Majeederh zata amsa, ta yi murmushi sosai ta ce "Me? Na yi girman kai wajen biyayya ga samun aljanata? bari na faɗa muku abinda ko shi mijina bai sani ba, wanda kuma personal issues na rayuwata amma yau zan buɗawa duniya gaskiyar lamarin" Daidai nan Khalil ya sake shigowa domin shi gaggawa ce da shi, shigowar shi ba daɗewa mutumin ɗazu ya shigo majeederh tayi tattausan murmushi ta ce "Wallahi wallahi wallahi, tun kafin Dr ya ce yana so na, nake son shi, so mai yawa son da bana iya bacci a lokacin ma bai san waye shi ba saboda ƙarancin shekaru ina son Khalil tun kafin na aure shi ina son Khalil tun yana bad boy ban tabbatar da ina son shi ba sai ranar daya dawo gareni a cikin B.u.k ranar taron da mukai a hall a gaban kowa....
[11/2, 20:11] Ummu: *MIJIN MALAMA*

*BOOK 2 PAGE 100*
Chapter 77 · 0% Book details