Sashe 6
Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Maman Alpha ta faɗa tana amsar Little dake ta bacci abinsa cike da kwanciyar hankali yana yi yana tsotsar lip's. "I go for your idea Maman Alpha, amma mene amfanin kai mata shi ɗin? Nan da wata tara za kiji wani babyn yazo ita da mijinta sa raini abin su" Cewar Yaya Bilkisu. Uncle Bello mamakin mata da halinsu ya cika shi magana ɗaya amma sai wannan ya ce wannan ya ce? Ya miƙe tsaye ya ce "Nan da ba gidan biki bane da ake ta gutsira magana" Ya dubi Majeederh ya ce "Ke Hawwa'u ta shi kuje Allah ya tsare ya baki sa a" Sai a lokacin ta ce "Uncle kamar mara gata ni kaɗai zan je haba..." Sai kuma ta saki kuka wanda kana ganinsa za kaga da biyu tayi shi, da kukan barin Baby Khalil dana tafiya ita ɗaya. Uncle Isma'il bai tsaya jiran mai bata haƙuri ba ya damƙi hannunta sukai waje yana zuwa ya samu P.a Hammad da Jawaad suna hira hadda tafawa kamar wasu sa'anni. His Excellency yana zaune a bayan mota tun zuwan su bai fito ba, ya sanya wani haɗaɗɗen brown ɗin Yadi mai kyau da tsada ɗinkin Half body da gajeren hannu babu babbar riga, yanayin yadda fuskarsa ke fitar da annuri zaka san cewa shi ne angon,Happiness lies on his face,He feels himself like a new man, calmness descends on him in his whole body. Maimakon ya buɗe Ƙofar ya fito sai ya danna number Hammad tana fara ringing ya katse, Hammad dake tsaye shi da Jawaad ya yi saurin barin wajan yana zuwa ya saka hannu ya buɗewa Majeederh bayan mota. "Bismillah" majeederh ta juya ta kalli Uncle Isma'il idanunta ya yi rau rau a hankali ta ce "Plx Uncle kai kazo muje" Ya zare idanu ya ce "Rufa mini asiri da abin kunya, kin ga shiga gobe ai zaki ganmu" Hawayen da take riƙewa ya shiga sakko mata ta ce "Shikenan kamar mayya" Yana riƙe dryrsa ya ce "A'a bamu haifi mayya ba" Shi kansa ya yi tunanin Abuturab ɗin zai fito daga motar ya kama hannun matarsa sai yaga shiru a hankali ya ce "Ki yi haƙuri, haka ko wacce mace take jin zafin rabuwa da gidan iyaye kin manta har wata ƙasar kika je shekaru 8 ba uwa ba uba babu kowa naki balle kuma gidan miji? Gidan biyayya da samun aljannarki?" Ya lallaɓata tana kuka sosai haka ta shiga bayan motar Hammad ya rufe ya zaga da sauri bayan sun yi sallama da Jawaad akan idanun Uncle Isma'il,da Uncle B Jawaad suka fice daga cikin gidan sai a lokacin tausayin Majeederh ya kama Uncle's ɗin, Uncle I duk abin nan hankalinsa yana kan Abraham tun ɗazo yake neman Digits ɗinsa ya shaida masa Maminsa tayi aure kada ya sake dawowa da maganar aure, amma magana ɗaya ake ta faɗa masa number a kashe yake. Tunda suka ɗauki hanya take shassheƙar kuka, tana da juriya da zurfin ciki da iya riƙe kanta amma tunda wannan ƙaddarar ta faɗa mata ta samu kanta ta saurin karaya da al'amuran rayuwa saurin kuka da shiga tunani, tana jin rayuwar babu daɗi ta kuma riga data saddaƙar bata da rabon farin ciki a duniya. His Excellency Abu-turab ya ɗan lumshe idanunsa yana jin nutsuwa na saukar masa a hankali ya juya ya kalleta ya ce "Jiddo, Mrs kuka kamar yarinya?" Ta yi masa shiru ya miƙa hannun ya riƙo nata mai taushi sosai ya haɗe da nasa ya ce "Stop haka nan" Ya faɗa can ƙasa, ya ƙara ɗan matsawa drawing her more closer to himself daidai kunnenta yana ɗora kansa a shoulder ɗinta ya ce "Common baby Jiddodo, haba Wifey" Ya faɗa yana riƙota bakiɗaya ta tura baki tana ƙasa da kanta, ta rasa me ya sa zuciyarta bata da sukuni da Gwamna ɗin? Tana so ta amshe shi hannu bibbiyu matsayin mijinta hakan ba zai faru ba sai ta saki jikinta da shi. Bai ƙara ce mata komai ba yana riƙe da hannunta har suka isa Government house. P.a Hammad ya buɗewa Abuturab ƙofa ya fito yana fitowa kuma kai tsaye cikin gidan ya shige ganin haka yasa Hammad buɗewa Majeederh ƙofa ya ce "Fito ki bisa kada ya shige" Ta fito a hankali tana jin faɗuwar gaba tayi bismillah dai ta shiga cikin gidan, babu kowa a main parlour tuni kuma His Excellency ya shige upstairs ta bisa a baya har zuwa ɓangaren shi ya buɗe ƙofa tare da zama saman kujera ta nemi waje ƙasan carpet tare da zama sun jima a haka kafin ya ce "Yaushe zaki arba'in?" Ya faɗa without looking at her ta bashi amsa ya miƙe yana ɗaukan wayarsa ya ce "Oh good night" ya shige Bedroom ya barta nan zaune tana binsa da kallo, a hankali ta gyara zamanta tare da jingine kanta da jikin kujera ƙirjinta na ɗagawa taya zata fara rayuwar aure da wanda bata san halinsa ba? Ta fahimci yana sonta amma shi ɗin kamar ba mutum ne mai bada kulawa da nuna damuwarsa akan iyalan shi ba. Ta ɗauki niyyar kyautata masa ko hakan zai sanya ta manta abubuwan baya tayi facing future life ɗinta, haka ta raya daren idanunta biyu ta kasa koda runtsawa fitowar Abuturab uku yana ganinta zaune a fitowa ta ƙarshe taga ganshi da cup da magani bai ce mata komai ba kuma, ana sallar asuba ya fito sanye da jallabiya sai ƙamshin perfume ɗin Dolce and gabbana yake ko inda take bai kalla ba ya nufi fita zuwa masjid.