← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 90

Sashe 38

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yadda Inna ta sunkuyar da kanta kaɗai ya alamtawa Latifa Omar maganar haka take, cikin yanayi na kiɗima ta shiga girgiza kai ta ce "Kada ki ce mini haka maganar take, kada ki ce ni Shegiya ce bani da uba, kada ki furta hakan a gareni na ruƙeƙi Mama" Girgiza kai ta ci-gaba da yi while hawaye na zuba a Idanunta ta ce "wallahi faɗar shegiya ce ni bani da toshe daidai yake da bugawar zuciyata Mama, ki ƙaryata Dr ki ce He's lied to me, ki ce ba haka bane, bani Latifa yake nufi ba, bana son samuwar wata hujja ko tubalin da zai sanya na tsani sunana na Latifa Omar, You are my real parents, I have no one better than you in my world" Ta kalli mahaifinta dake kwance yana numfashi da ƙyar, ta juya ta kalli Inna wacce hawaye ya gama wanke mata fuska taƙi cewa komai, Dr na tsaye yana kallon Ikon Allah Latifa ta zube saman qiwwoyinta ta ce "I know that I am not an adopted child, I am not Shegiya and I was born wedlock,ku duniya ta sani matsayin iyayena Mama meke faruwa mene gaskiyar al'amarin? Shin ne Adopted child ce ko ƳAR-AMANA (Nimcy upcoming book)?" Inna ta ɗago kanta zuriyarta na bugawa da ƙarfi, ranar da take ta gudun zuwanta gashi ya zo, ranar da bakinta ba zai ƙarya ba ta kalli Latifa ta ce "Gaskiya kike son sani Latifa domin zuciyarki ta daina kokwanto, ko kuma salama da sanyi kike buƙata na kwanciyar tashin hankalin naki a yanzu ta hanyar rufe miki ainahinki da asalin wace ke?" Latifa ta ce "Gaskiyar nake son sani Mama, ina fatan kalaman da zasu sanya fuskata cikin walwala ya fito daga cikin bakin ki" Inna ta ce "Ke ba ƴar Malam ba ce, ba kuma ƴata ba ce" With shocked Latifa ta saki baki tana kallon Inna, kukan ya tsaya mata cak, gata dai a raye tana numfashi, ƙirjinta na harbawa alamar zuciyarta a daidai take aikinta, amma zufar dake yanko mata ya kure dukkan wata nutsuwar data samu wanda kai tsaye mai Kallonta zai samu tubalin gina tunaninsa wacce sarrafa ƙwaƙwalwarsa ga cewa ta samu matsala, tana raye amma jinta take tamkar matacciyya a rufe a cikin rami sbd tsananin gigita da tarin kiɗima wanda ya haɗe mata da tu'ajjujin jin al'amarin dake neman ruguza gobenta. Inna ta ce "Wannan shi ne gaskiya al'amarin, ke ƳAR-AMANA ce, rana tsaka kina jaririyar Malam ya shigo mini dake matsayin TSINTACCIYA, har yau har kwanan gobe bani da masaniyar daga inda ya samoki, balle na bincika asalinki ku da asirrin ce ne" Latifa Omar ta kasa cewa komai tana ƙoƙarin saita numfashinta dake ƙoƙarin yi mata gaddama. Dr ya ce "That means he is the only one who knows the truth about who Latifa is, and who is her real father?" Inna ta ce "That's what I mean" Dr ya jinjina kai. Kafin su motsa na'urar jikin Malam ta fara ƙara da sauri Dr ya yi kansa yana duba gudun oxygen ɗin dake aiki a jikinsa, ya ƙara ɗaga kai ya kalli na'urar yaga numfashinsa ne ke tafiya yana yin ƙasa baya dawowa, Inna ta miƙe ta ce "Malam kada ka tafi ka barmu cikin wannan juyayyen al'amarin mai wahala fahimta ko gane asalin shi, kai ne kaɗai shaidar da zata fitar daga Latifa daga cikin halin da take ciki, tun ba yanzu ba nake jan kunnenka daka faɗa mata gaskiya amma kayi burus, ni ma kace nayi ta aurena idan na faɗa haka muke zaune tsayin shekaru, mai yasa kake ƙoƙarin tafiya bayan kasan zaka bar baya da ƙura? Eh Malam Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" A daidai lokacin numfashin Malam ya gama tsayawa cak! Alamar ran shi ya tafi zuwa kushewa tasa ta ƙare ciwo bana tashi bane, Latifa Omar ta ƙurawa gawar Malam idanu kamar shasha kuma ta saki murmushi while hawaye na zuba daga cikin idanunta ta ce "This is something that will never be possible, there must be someone involved in all these things, it is necessary to find out who it is" Wannan abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, dole ne a samu wanda ke da hannu a cikin dukkan wadannan abubuwa, wajibi ne a gano ko wane ne. Inna dake kuka kamar ranta zai fita ta ce "Kul na kuma ji, ahir ɗinki Allah ne kawai mai yin yadda yaso da rayuwar bawa, ki yarda Ubangiji ya ƙaddara miki taki rayuwar haka nan, ya aminiyarki Majeederh tayi da nata rayuwar? Ba gashi komai ya zama tarihi ba, kalli wanda take aure ashe ɗan shugaban ƙasa ne, Kiyi haƙuri mu yi addu'a sai komai ya zo da sauƙi" Kamar zautacciyya Latifa ta ce "Majeederh" Mai yasa ba zata barta haka bane, ta ƙwace mata komai ba, a hankali ta ce "Now Majeederh will take revenge on me? Amma tasan abubuwan dana mata ba" Ita a dole yadda ta cutar da Majeederh bata yarda sakayya Ubangiji ya fara nuna mata ba, ta jingina hakan da alaƙanta shi da wani ke mata asiri. Ta riƙe kanta da hannu bibbiyu ta kurma ihu cikin I.C.U ɗin ta ce "Wai meke shirin faruwa dani ne, Ubangiji me na aikata da zafi har haka"... Uncle Isma'il na zaune a parlour shi, waya yake yi a hankali har Anti ta fito fuskarta ɗauke da murmushi yana ganinta ya kashe wayar yana haɗe fuska ta ce "Ashe ka shigo tun jiya, ina ta zullumin ina ka kwana" Uncle Isma'il ya ce "Kin san ai ba zan bar Kano ba tunda ba kurciya aka yi mini ba, aka rabani da Jawaad da Sona" Zuciyarta ya bada sauti gabanta ya faɗi, ta daure da ƙyar ta ce "Ayya wanne irin kurciya ba daɗin ji, yanzu dai bari na kawo maka breakfast" Ya ɗago idanunsu ya zuba mata su ya ce "Lubna" Ta ce "Na'am" Ya ce "Stop pretending plx" Ta ce "Kamar yaya kenan Abban Jawaad?" Ya ce "Kamar yadda dai kika ji na furta, ki daina nuna you're smart, wlh tllhi I'm smarter than yanzu, i am smarter, kuma ko da ban gano gaskiyar labarin ba; babu mamaki garƙame tunanina ki kai da bakina kika yarda da ɗan maƙulik a tekun maliya" Baki ta buɗe za tayi magana ya ɗaga mata hannu ya ce "Baki da wani harafi da zaki harhaɗa wajan fahimtar dani abin da na jima da fahimta, da kuma wanda na gane a yanzu, ki buɗe kunne da kyau kiji! Ba zan tambayi hujjarki tayin hakan ba, yiwa Alpha kurciya da raba Abbu da majeederh tun tana shekaru goma, sam ba zan yi hakan ba Lubna abu ɗaya zan faɗa miki, wlh wlh Allah ba zan barki ba, ki shirya amsar hisabin duniya domin zaki amshi kasonki tun kafin zuwanki kushewa" Uncle Isma'il da idanunsa sukai jajur ya ce "Wlh wlh ina jin ni ba alkairi bane a cikin ƴan uwana, na zama silar baƙanta zuciyar su, ki shafa mini baƙin fentin da ba zai taɓa gogewa daga fuskata ba dani da yarana, kin raba Alpha da iyayen shi, da mahaifar shi cibiyar shi, kin raba shi da ƙasar shi bakiɗaya, a cikin hankalinsu yake ko yana cikin gushewar tunani ke kaɗai kika san hakan, kin raba soyayyar fari, Since Majeederh was a little girl, he has been taking care of her, he loves her so much, he has nothing to ask or care for except her, na jima da sanin zallar so yake mata, ba so na ƴan uwa ba so ne irin na aure, He is an arrogant and deep inside that is why his situation is not understood, wlh wlh bana ko jin ɗar baƙin cikin auren su kike shi ya sa ki ka aikata hakan" Uncle Isma'il ya goge hawayen daya sakko masa ya ce "Ki kwantar da hankali bashi ki kaiwa ba, Jawaad da Sona su kika jawa, faɗar Ubangiji ce duk abin da kayi za ai maka, ƙaiƙayi koma kan ɗan masheƙiyya, zaki saka wutar gaba tsakanin Mijin Malama Khalil da ɗan uwan Malama Alpha" Ya miƙe tsaye yana kaiwa da dawowa ya ce "Me tayi miki da zafi har haka ne don Allah? Me kuma ɗan uwana ya yi miki?" Za tayi magana ya ƙara ɗaga mata hannu ya ce "Ya isa, enough is enough bana son ƙara ganinki Lubna ki tattara komai naki ki shige Gombe ki koma cikin Fulani wajan Ruga a ci-gaba da tatsar nono, ashe da nake cewa Fulanin Gombe ba dai asiri ba gaskiya ni ma ba haka kika barni ba, Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Lubna kin cuceni kin cuci kan ki, kuma kin cuci yaranmu, maza ki fita daga gidan nan, na sake ki saki ɗaya, na sakeki saki biyu, na sakeki saki uku" Dim! Anti ta yanke jiki ta faɗi babu inda yake motsi a jininta, Uncle Isma'il ko a jikinsa ya sanya kai ya fice, yaci karo da Jawaad a entrance zai shigo ya ce "Jawaad" Ya ce "Abba" Ya bashi key ya ce "Muje gidan Uncle ɗin ka, i can't drive myself" Jawaad ya amshi key suka nufi gidan Abbu.... Kasancewar weekend ne yasa kowa yana gidan, Abbu na zaune a parlourn shi dake part ɗinsa, baya cewa komai sbd abubuwan da suka taru sukai masa yawa a zuciya, lokaci yake sawa a kira masa Majeederh sai ya yi ta Kallonta can yaje ta je kawai, yanzu ma yana zaune sanye da Khasmir fari tas ya ɗora ƙafarsa akan table idanunsa rufe ya jingina da jikin kujera, hannunsa riƙe da black tea yana ɗan juyawa,a hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar Parlourn ta shigo bakinta ɗauke da sallama ta shigo, tana sanye da hijabi har ƙasa ta ƙara haske tayi ƙima ta ƙarasa zata zauna ƙasan carpet ya nuna mata saman kujera ta zauna ta ce "Gani Abbu" Ya zuba mata idanunsa ya yi ta kallonta ta sunkuyar da kanta ƙasa, ya jima yana binta da kallo kafin ya ce "So da gaske kece dai Hawwa'u" Tayi murmushi ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce "Kina son Mijin naki?" Tayi shiru clamly ya ce "Open your heart dear" A hankali ta ce "Even though I did, is a different thought that flashes through my mind" Ya shiru abubuwa
Chapter 38 · 0% Book details