← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 90

Sashe 83

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Innati ta fashe da matsanancin kuka hankali tashe ta ce "Asstagafirullah! Allah na tuba bana iya bacci idan na tuna a gidan nan aka bunka iska ta biyu, a gidan nan aka dinga lalata, bani da nutsuwa ana tsokala tsinke a kunnena wuta za a tsokano saboda tashin hankali" Uncle Bello da yake shigowa ya ce "Ibrahim ku tashi ku tafi kar ku yi missing Flight ɗinku" Majeederh dai kuka take, Alhassan ya cika ya yi fam ya kafe Innati da ido, Baby Khalil ya kalli Abynsu ya ce "Aby mene buga iska?" A harzuƙe Innati ta ce "Ubanka Ibro shi ya bugawa babarka iska, ya ƙunsa mata ciki wallahi tallahi" Da wani sauri Majeederh ta miƙe tana yin waje domin Uncle Isma'il ya ce har yanzu Alpha na asibiti kuma karta kuskura ta je, ta jima tsaye kafin taga Khalil ya fito shi da Jawaad da yaran tana ganinsa ta buɗe ƙofa ta shiga saboda wata matsananciyar kunya data lulluɓe mata jiki, bata taɓa jin kunyar mijin nata Dr Ibrahimul-khalil irin yau ba, bata son ma haɗa Idanu da shi, shigowa motar ya yi bayan ya saka yaran tana ganinsa ta rufe ido sarai ya ganta ya share, a haka suka nufi airport, Uncle Isma'il tuni ya sanya ayi masa binciken gidan su Zuleehart a can Ghana accra ɗin. Zuwan su airport ba wahala bayan an musu komai passengers sun fara shiga, Khalil na sallama da John yaga wani ya tsaya kusa da Majeederh kallon su yake, a tsorace Majeederh take kallon mutumin fuska rufe ya miƙa mata envelope babba fara tas sai wani ƙaramin rose dake maƙale a jiki ta ce "Waye kai?" Ya ce "Sanin ko waye ni bashi da muhimmanci, domin bani ne wanda yake zuwa gareki ba, ni ɗin Manzo ne, bi ma'ana ɗan aike, Boss Ubangida shi ne wanda ya aiko ni.....,"
"Ok da kai da ubanka yake ko wa?" Khalil yama kasa ƙarasa maganar ya nufi kan mutumin "Ni fa ɗan aikene, ko a zamanin jahiliyya ɗan aike baya laifi kuma..," Wani mugun naushi da Khalil ya sauke mutumin shi ne ya hana shi ƙarasa maganar, ya damƙi wuyansa tare da yi masa gware nan take jini ya ɓalle, Alhassan me zai yi ba ihu ba yana tsalle yaga ubansa na faɗa, mutumin ya ɗaga hannu ya ce "Ka saurare ni please, zan faɗa maka ko waye" Bai bashi damar magana ba ya damƙi hannun ya karya Ihun azaba ya saki da wani irin fitsarin wahala, ya ce "Ka tsaya ka ji" Khalil ya sake kaiwa bakinsa naushi haƙori ɗaya ya fita ya saka hannu ya zare ribbon ɗin kansa a kausash ya ce "Bana buƙatar reasons, ka zama shaiɗan mai raba aure ko?" Ganin Khalil na ƙoƙarin yin kisa yasa majeederh cewa "Man...," Wata masifaffiyar tsawa ya daka mata tare dayi mata nuni ta kama yaran su nufi jirgi, polices ɗin wajen suka tsaya domin babu wanda bai san waye Khalil ba, ya kalli mutumin ya ce "Kai kayi kaɗan wajen siyan soyayyar Matana, Ubangidan naka ya fito muyi gaba da gaba, zan tafi Saudiyya idan ɗan halak ne shi cikin uwarsa da ubansa ya biyoni zuwa Palace ga i.d card nan" Yana faɗin hakan ya cilla masa I.d card ya nufi cikin jirgin bai yarda ya nufi wajen Jee ba domin sai yanzu yake jin nauyin tsawar da ya yi mata, yana shiga cikin jirgin mutumin ya nufi mota jiki jina jina da jini, yana shiga wanda ke cikin motar ya ajiye azkar ɗin hannunsa ya ce "Sorry" Mutumin ya ce "Boss Ubangidana Akeeth ni zan baka haƙuri" A hankali Akeeth ya girgiza kai ya ce "Ka yankar mini ticket na zuwa Saudiyya now, I'll follow him....
[11/2, 20:11] Ummu: Khalil ya sake rungume Gimbiya yana jin kamar ya shige cikinta ya huta wani irin kewarta ta saukar masa tare da mamaye jikinsa, ƙofofin zuciyarsa suka bubbuɗe da soyayyar Ummien nasa, idanunsa sun yi jajur saboda yadda a karo na farko tun bayan sanin wace mahaifiyarsa ya ji tana kuka, a hankali hawayenta masu zafi suke sauka a bayansa wajen wuyansa, ta ƙanƙame shi da kyau kamar zata sake yin cikinsa ta haife shi, a hankali a kuma nutse tana babbuga bayansa tana shafawa saboda jin yadda yake sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri, wata na korar wata.
"Ummieeeyyy" Iya abinda bakinsa ya furta kenan, saboda bashi da ƙarfin zuciyar da zai faɗi abinda yake saman harshensa a yanzu, ya sake rungumeta, wata gamsasshiyyar nutsuwa na sauka a jikinsa, sai yanzu ya ƙara tabbatar uwa, mahaifiya rahama ce, dole wanda ya rasa tashi ya zubar da hawaye.
"Ibrahim? Khalil yarona"
Gimbiya ta furta a kamalance tana jin dukkan wata damuwar zuciyarta na shekara wajen uku ta yaye nan take, zuciyar ta wanke tare da yin fari daga duhun damuwar da Mr President ya sanyata "Kana raye? Zan sake ganinka?" Yadda take maganar da ƙyar zaka san cewa ba ƙaramin ƙarfin hali tayi ba wajen furta kalaman, Khalil ya ɗago a hankali ya zubawa mahaifiyar tasa ido, shi mamaki yake wai ita ta haife shi? Ya ɗan yi Miskilin murmushi kafin ya ce "Allah bai ɗauki raina ba, ina tare dake, zan ji daɗin uwa Ummie" Sharr! Wasu hawayen suka sake sakko mata a hankali tayi murmushi mai laushi ta ce "Ya Allah!" Ta kama hannunsa tana tattaɓa shi ya riƙe hannunta ya ce "The real Ibrahimul-khalil is back, your son ɗanki ya dawo" Da sauri ta sake jawo shi ta rungume a wannan sa'ilin kasa riƙe kukan ta yi, ta sake shi bisa umarnin zuciya. Majeederh dake tsaye ta yi ƙasa da idanunta hawaye na zuba a cikin idanunta, lallai uwa! Daban take a cikin rayuwar yaranta, yadda Khalil ya narke jikin Ummie kaɗai ya isa ya fahimtar da ita yadda ya yi kewar mahaifiyarsa, ta rufe ido tana jin soyayyar mahaifiyarta fulani na ƙara sauka a zuciyarta ko wanne motsi tayi sai ta tuna da ita, bata san soyayyar uwa ba, babu rabon kuma zata samu ɗin Ubangiji ya fita sonta tunda ya ɗauke ranta ya barsu. Jin an kira sunanta a taushashe ya sanya ta ɗaga kanta Gimbiya ta gani riƙe da hannun Khalil tana kallonta alamar ita ke kiran nata, ta nufeta jiki a sanyaye da sauri twins da Yaa K suka mara mata baya, tana zuwa Gimbiya ta ce "ke fa ba Daughter-in-law ba ce, you're my daughter ko baki auri Khalil ba" Kunya ta kama Majeederhn ta sunkuyar da kanta Khalil ya ɗan shafa kansa speaking calmly a taushashe ya ce "Ummie ki rungumeta itama" Gimbiya ta kalli Khalil sai kuma ta ɗauke ido ta ce "Come closer dear" Ta haɗa su ta rungume a jikinta tana rufe ido a ranta ta ce "Alhamdulillah!"
Chapter 83 · 0% Book details