← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 90

Sashe 3

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ce "Grandpa" Ya ce "Yes dear" Ya ɗan yatsuna fuska sosai ya ɗauki seconds bai ce komai ba sai da sukai nisa sosai ya ce "About the Gang team, Where's Taj?" Grandpa ya yi shiru sai kuma ya watsa hannu yana ɗaga shoulder's ya ce "I don't know where he is, after you left the country, the Gang team was gone" Abraham ya yi shiru yana buƙatar ganin Taj, ya ji ina yakai al'ƙawarin da ya yi masa na wasiƙa? Ina yakai envelope ɗin? Har suka isa airport Abraham bai sake ko buɗe ido ba balle magana, suna isa jirgin na shirin rufe ƙofa bai tsaya jin me Grandpa zai faɗa ba, da sauri sauri ya shiga taka steps ɗin benen har ya shiga yana shiga ƙofa ya rufe, Grandpa ya yi murmushi yasan Abraham fushi yake da shi, yana kuma fatan this time around ya samu daidaito da mahaifinsa Denial. Yana tsaye har jirgin ya tashi kana ya shiga mota yabar wajan shi ma... Maman Alpha ce zaune ita da Anti sai Yaya Bilkisu a hankali ta ce "Daman komai ya yi farko yana da ƙarshe, gwara Majeederh muna ganinta munga Irin ƙaddarar daya faɗa mata,amma ɗan uwanta ba? Babu wanda yasan duniyar da Alpha ya shiga" Ta faɗa cike da damuwa. Yaya Bilkisu ta ce "Allah ba azzalumin bawansa bane, sai dai bawan daya zalunci kansa da kansa, Allah kuma baya ɗorawa bawa abinda ba zai iya da shi ba, sai dai bawa ya ribaci ƙaddarar daya jawa kansa, mu duka muna addu'ar Ubangiji ya dawo da hankalin Alpha zuwa gida kullum da shi nake kwana nake tashi ki duba shekara nawa yanzu?" Maman Alpha ta yi shiru tana wani irin murmushin takaici Anti ta ce "Haka ne, In sha Allah yana nan lafiya ma" Kafin su yi magana suka ji sallama da mamaki Anti ke kallon Latifa Omar wacce ta shigo ɗauke da damuwa bayan sun gaisa ta ce "Anti don Allah ku yi haƙuri dan gane da reported ɗin da na yi a gidan jarida, raina ne ya ɓaci duk yadda na yarda da Majeederh nake kareta a gaban jama'a da iyayenmu amma hakan bai hana taci amanata ba, na ɗauka Majeederh tana sane da cikin jikinta ta rufe ni shi yasa raina ya ɓaci, Apparently I a made misunderstanding, without stopping to research the matter, ku yi haƙuri plx" Yaya Bilkisu ta ce "Allahamdulillah, tunda kin gane kuskure ne, kuma ke ɗin aminiyya ce ta gari ga Majeederh" Ta ƙara basu haƙuri kafin ta shige bedroom ɗin da Majeederh take ciki. Ta sameta zaune riƙe da Baby Khalil da idanunsa yake buɗe ta ƙura masa idanu, tayi murmushi ta ce "Mai jego" Majeederd dai bata ce komai, Latifa ta shiga bawa Majeederh haƙura Exlty yadda ta bawa su Anti hadda kukanta, ganin Majeederh bata ce komai ba ta ce "Plxx Bestie let by gones be by gones sharrin shaiɗan ne" A hankali tana rufe ido ta ce "No bad" Tana jin a ranta tabbas sharrin shaiɗan ɗin ne, tunda ta yarda da Latifa ita ɗin ƙawar arziƙi ce wacce samun kamarta zai wahala musamman idan ta tuna har mijinta ta bata opportunity na aura, ta ƙara lumshe idanunta damuwarta biyu ce a yanzu yadda abu ya tsine nata ya kureta kuma ya cireta daga cikin yaran daya haifa ya sadaukarwa da duniya ita yafi komai ɗaga mata hankali, idan ta tuna wai little ɗan data raina da hannunta shi ne ya yaga rigar mutuncinta sai ta ji zuciyarta ta mata nauyi bata jin daɗin komai a duniyar, tana fatan mutuwarta ta risketa amma da alama kamar yanzu ta saka hannu a fata na rayuwa, suna ɗaki su Anti kuma na parlour suna jiran har dare ya yi Abuturab ya zo tafiya da matarsa.... Zaune take tayi wani irin zama kamar zatai sujjada ta yafa wani jan mayafi akanta, mutumin dake gabanta ya ce "Ke la'ananniyya ce, ke muguwa ce, yake azzaluma me kuma ya kawo ki yanzu bayan sharaɗin da nayi miki?" Ta ƙara sunkuyar da kai tana shakkar haɗa idanu da mutumin sbd muninsa bakinsa har wani hayaƙi yake ta ce "Kamar yadda ka sani tun farkon zuwana wajanka akan Aminiyyata ne, ta hannun damana, bana buƙatar duk wani cigaban ta tunda na fahimci ta fini komai na rayuwar duniya, tana da kyau tun muna raya ta tashi da farin jini duk da baa ganin fuskarta, wannan dalilin yasa na da ƙushe wannan farin jinin nata, danginta na sonta tana kare mutuncinta, ta fini ilimi nesa ba kusa ba, har tazo taci gasar Kur'ani ta duniya, na mayar da ita mujiya a wajan maza, ban san tana da ciki ba kai ne ka fara ankarar dani, a sanda na koma gida bayan na bar nan sai dana kashe dubu ɗari biyu na maganin da zai zubu mata da jinin al'ada duk dan kada ta gane, sannan ka ƙara yin aiki da jinin zai dinga fita duk wata, kai ne ka sanya Aljanu kwantar da jiki, kuma kai ne kasa Aljanu suka tashi cikin kuma suka haɗa ɗan cikin motsi duk da yana cikin ƙoshin lafiya, kai ne ka hana likita ganin cikin Majeederh, kullum results zai nuna she's good...." Da sauri mutumin ya ce "Tsinanniyya la'ananniyya dai na yi mana turanci a nan ko na turɓuɗeki ki zama toka ko ɗan akuya" Jikinta na rawa ta kwaso wata ashar ta maka alamar ban haƙuri ta ce "Kuma ni na ƙara rura wutar son da takewa Abraham har take sake masa jikinta, kada ka manta kafin aikin yanan ya ci sai dana zubar da ɗan cikina babu adadi, kai ne ka sanya na fara bin mata ƴan uwana sbd duk aikin da kake mini akan rusa rayuwar Majeederh, kai ne kace na sanya mijina ya aureta yadda zan fi jin daɗin durƙosar da rayuwarta kai ne....," Ya yi saurin dakatar da ita da faɗin "To cikakkiyar azzaluma Ubangiji ba zai barki ba, lallai zaki girmi abinda kika shuka yanzu na haka wani cikin ne dake gashi nan ina Kallonsa a ƙasan mararki kuma ya zama dole ki zubar da shi" Gaban Latifa ya faɗi ta sha cikinta tana lumshe idanu ta ce "Zan zubar idan zaka mini abinda nake so" Ya ce "Bayan mugwayen abubuwan da kikai mata me kike buƙata yanzu?" Ta ce "Kada ka taɓa bari Abuturab ya kusance ta balle ta haihuwa har ɗan ya samu gadu, kada ma su haɗa gado har abada sannan ina son sanin waye MIJIN MALAMA na gaske??
Chapter 3 · 0% Book details