← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 90

Sashe 55

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

nada ban" Calmly ya ce "Wannan nada ban ɗin ni ne" Ya zame tare da durƙosawa a gabanta tunda ba zata iya tashi ba, she's in serious sick ya ce "Kin taɓa tambayar kanki me ya sa na fifita ki da ƙanne na? Da sauran ƴan uwanki mata? Kin taɓa tunani me ya hanani aure bayan Ubangiji ya bani ikon yi? Kin taɓa tambayar ko da wasa bana maganar wata ƴa mace?...," Tayi shiru ya kalleta murya ƙasa ya ce "I did this because of you" Ya yi ƙasa da murya underneath his breathe ya ce "I love you, i so much loves you Hawwa'u i love you" Kuka take sosai kafin ta ce "Am sorry Yaya, Ina son mijina" Da sauri ya ɗaga kansa ya ce "Liar, a rashina kika so shi, a babu ni kika amshe shi, sbd na yi nisa dake kika kusance shi, sbd na raba hannu dake kika riƙe nasa, yanzu kuma na dawo" Ta kasa cewa komai sai kallonsa da take da ƙyar ta ce "I love Khalil Yaya" Da ƙarfi ya ce "Stop saying this to me, ba zan taɓa yarda dake ba kamar yadda kike so na, har yanzu har gobe har ƙiyama ta tashi you will still loving me....," Daga bakin ƙofa suka ji an ce "Loser" Muryarsa ta fita da ƙyar Majeederh bata buƙatar sanin ko waye ƙamshin turarenta ya wadatar ya shaida mata cewa shi ne, Alpha ya Khalil dake cikin wata fitinanniyyar Shadda dark blue ya harɗe hannu a ƙirji, Ubangijin ne kaɗai yasan adadin daya kwashe tsaye yana jin su, idanunsa ya rine har baka ganin ƙwayar idanunsa sosai slowly ya ƙarasa shigowa ciki ya nufi inda Majeederh take kai tsaye tayi saurin rufe Idanunta tunaninta dukanta zai yi, sai ta ji saɓanin haka ya saka hannu tare da ɗaukanta cak ta buɗe idanu tana saurin riƙe shi a hankali taga ya miƙar da ita tsaye kamar sai saketa tayi saurin saka hannu ta rungumesa tana kwantar da kanta a ƙirjinsa a shagwaɓe ta ce "ba zan iya tsaiwa ba, I feel dizzy" Khalil ya kalleta sai kuma ya yi murmushi mai kyau ya ce "I'm hear with u Madam" Tayi murmushi domin harga Allah tama mance da batun Alpha a wajan, a hankali a nutse Khalil ya rungumeta tare da janta zuwa bakin window ya yaye labule da hannu ya nuna mata ƙyakƙyawar motar dake wajan an saka flowers tare da yin rubutu “For u wife” daga gefe aka ce "Thank you so much" Ya juya da sauri tana kallon Khalil murmushi fal fuskarta ta ce "For me?" Ya jinjina kai ya ce "Yes Wife" Sosai take mamakin yadda a kalaman Khalil babu i love you, a hankali ta shige jikinsa tare da rungumesa sosai tayi masa small kiss a wuya ta ce "Thank you, Allah ya ƙara ariziƙi" Ya shafa cikinta yana sauke numfashi a hankali ya ce "Ya ƙara alrdy" Ya nuna mata hancinsa ta kalle shi ya ce "Kiss me" slowly tayi kissing wajan ya nuna baki ya ce "Not small, a special kiss Madam" Ta ja hancinsa a hankali kuma ta haɗe bakinsu waje guda ta shiga sauke masa wani irin masifaffan hot kisses ta mance da wannan ɗan ƙwaninin yaron take tsaye ta mance suman da tayi na bata so da ƙaunar shi, da wani irin ƙarfin ta ji an fisgeta har sai da tayi ƙara tana ƙanƙame jikinta jikin Alpha duka rawa yake, A tsorace Majeederh ta ƙwace hannunta Alpha ya yi kneeling down a gabanta ya ce "I know I did you wrong, karki hukunta ta wannan hanyar u hurting me" Sai kuma ya fashe da wani irin kuka ya nufeta kamar zai rungumeta ya ce "I love you so so much &most, i so much loves you Hawwa'u, wallahi ni ne wanda kike so ba shi ba, idan taƙamar kin rai ne shi ni na ni na raineki i sacrificed alot sbd ke i love you Hawwa'u ki tambayi Abbu shi ne shaida" Da wani irin zafin nama Khalil ya nufi kan Alpha ya shaƙi wuyansa sam Alpha bai attempting kare kansa ba, Khalil ya shiga zubawa Alpha wasu tagwayen maruka yana sakar masa naushi a ciki, Majeederh ta runtse idanu tana jin saukar marukan har zuciyarta da ƙarfi ta ce "Khalil!" Ta kira sunan shi da ƙarfi, ya tsaya cak sai kuma ya juya yana kallonta ta ce "Stop" Ya saki Alpha ya ce "Jee stop kika ce? Akan shi?" Ta girgiza kai ta ce "Ba a kansa bane, bana son wani abu ya faru ace kai ne" Ya dinga kallonta sai kuma ya yi wani irin wannan Alpha ya tsaya gaban Khalil ya ce "U see? Ka dai gani hakan zai tabbatar maka da gangar jikinta kake aure ba zuciya ba, kaga zahirin True and enternal love" Khalil ya sake juya ya kalli Majeederh za tayi magana ya ɗaga mata hannu ya juya da sauri ya fice daga cikin room ɗin yana buga musu ƙofa da ƙarfi, wani irin jiri Majeederh ta fara ji sbd tashin hankali da ƙarfi kuma ta saki ƙara tana dafe mararta kafin ta faɗi Ajlaal dake shigowa ya taro ta faɗa jikinsa a sume.... Tun shigowar shi emergency ɗin yake tsaye ya kasa ko zama, a hankali kuma Uncle Isma'il ya ce "Alhji Abdul'aziz ka shiga mana?" Ya ɗan girgiza kai ya ce "No, Allah ya bata lafiya" Maman Alpha dake zaune ta ce "Amin" Sai kuma ta juya ta ce "Yaya Bilkisu, Hajiya Asabe Here is my neighbor Zuleehart ku gaisa" Yaya Bilkisu ta ce "Sannu Zuleehart ya gida" Tayi murmushi ta ce "Allhamd, ya mai jiki?" Ta ce "Lafiya Allhamd, ya kuma yara?" Ta ce "Suna can tare da driver" A hankali Zuleehart ta gaisa da kowa har Khalil kana ta ce "Ance maka da lafiya kai ma? Allah ya sauwaƙe" A hankali Alpha ya ce "Thanks" Ya faɗa without looking at her. Daidai nan likita ya fito hannunsa da paper ya ce "Ku canki jinin waye ya yi daidai dana Malama" Uncle Isma'il ya ce "Kowa ya san nawa ne" Uncle Bello ya ce "haba Yaya ina laifi ni ma" Jawaad ya ce "Ai nawa ne ma" Dr ya ce to bari na kira results ku ji ya ce "Alhaji Isma'il" Uncle ya ce "Yes" Dr ya ce "Doesn't match" Ya kira Uncle Bello ma haka, haka Jawaad duk ba daidai bane A hankali ya ce "Dr Ibrahimul-khalil Abraham" Khalil ya sauke numfashi a ɓoye Dr ya ce "Congratulations na jima banga jini da ya yi daidai irin naka da nata ba" Jawaad ya ce "Wow! What love" Dr ya ce "But am sorry to say ba zamu saka mata naka ba, jikinka ya ɗan hau kana buƙatar hutawa" Khalil ya kasa cewa komai Dr ya kalli Alpha kana ya juyawa ya ce "Ajlaal Sultaan?" Mai martaba Ajlaal Sultaan ya ɗan ware idanunsa bai ce komai ba, ya ce "Congratulations" Ya kuma cewa "General Alpha Bello khan? I congratulate you" A ɗan hargitse Khalil ya ce "Ban so, ban son jinin kowa a jikin matata" Da sauri Alpha ya ce "To bari naga ko zaka hana" Shi ma Khalil ya miƙe yana tattare hannun riga ya ce "To bari naga uban wanda ya isa a saka mata jinin da ban so" Abbu dai na tsaye, Zaytoon na zaune haka Ƙhulud Gimbiya daman tun zuwan su take bacci a cinyar Ajlaal har zuwan Abbu da sauran mutane duk bata sani ba, Uncle Isma'il ya yi saurin shiga tsakiya a fusace da sauri Khalil ya saka hannu ya ɗaga Uncle Isma'il cak ya matsar gefe yana kallon Alpha ya ce "Idan kai isa kuma ka haifo ka je a saka mata jikinka, zan nuna maka kai ƙaramin ɗan iska ne" Alpha ya ce "Ni ne ɗan iska?" Khalil ya ce "In capital letters ƙaramin ɗan iska" Daidai nan kuma Zizi ta shigo da sauri ta nufi wajan Khalil tun kafin ta ƙarasa ya daka mata tsawa, a hankali President Denial David ya shigo daidai lokacin kuma Gimbiya ta buɗe Idanunta kai tsaye kuma ganinta ya sauka akan Daddyn Khalil jikinta ba wani irin rawa da ɓari ta dinga kallonsa, Ajlaal ya riƙeta ta fisgi cikin mamaki al'ajabi da wani irin tu'ajjuji Ajlaal yaga Gimbiya ta miƙe tsaye akan ƙafafuwanta laɓɓanta na rawa ta shiga nuna Dad da hannu da wani irin ƙarfi ta ce "Denial.., Denial where's my son?" Sai kuma ta fasa wata gigitacciyar ƙara tayi baya Khalil dake tsaye bai san lokacin da ya yi kanta a gigice a kuma kusan tare da shi da Ajlaal suka nufi kanta cikin rashin sa a Khalil ya saka hannu ya ture Ajlaal Gimbiya ta faɗa jikinsa a sume daidai nan kuma Abbu ya juyo idanunsa ya sauka akan kyakkyawar fuskarta.....
Chapter 55 · 0% Book details