Sashe 45
Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ruma ce tsaye a tsakiyar parlourn hannunta ɗaya a kanta tana zunduma ihu ɗaya hannu kuma riƙe da trolley ɗinta cike da kayanta, ta zube a ƙasan carpet tare da yin zaman ƴan bori ta ƙara zunduma ihu ta ce "Na shiga uku na lalace, na shiga uku Shikenan mutuwa zan yi na gama yawo ajalina ya zo, innalillahi wa'inna ilahir raji'un" Kuka take da kururuwa wanda hakan ya ƙara ɗaga hankalin duk wanda yake wajan, Abbu dake part ɗinsa kwance ba lafiya ya fito da ƙyar tare da jingina da jikin bango yana shigowa kuma abin da idanunsa ya fara gani shi ne Majeederh, ya tsura mata Idanu kafin ya sauke numfashi yana rufe Idanu, a rikice Yaya Bilkisu ta nufi wajan Ruma ta ce "Ke lafiya? Waye ya mutu mijin naki ne ko?" Ruma na kuka wiwi ta ce "Ni na mutum Yaya, ni ce na mutu na shiga uku na lalace wayyo rayuwata" Maman Alpha ta ce "Don't Force her, ku bata bottle water mai sanyi" Majeederh ta nufi wajan fridge ta ɗakko ruwa tare ɓalle murfin ta zuba mata a cup, Yaya Bilkisu ta amsa ta bata ta sha sosai, tana gama sha ta kifa kanta tana sauke ajjiyar zuciya sai kuma ta ƙara fashewa da kuka, ba wanda ya ce mata komai, Mami zuciyarta ta tsinke ta shin ya nuna ƙarara akan fuskarta, daman ita bata iya fargaba ba ta miƙe da sauri sbd cikinta daya juya ta nufi toilet, Yaya Bilkisu ta kalli Abbu cike da tausayawa ta ce "Ka zauna mana kai da ba lafiya ba" Ya zame idanunsa daga kan Majeederh wacce take ɗan danna waya tana son kiran Aaliyyah ta ji ina ta tsaya, calmly yana rufe Idanu ya ce "No, am ok here" Ta ce "To Allah ya kyauta, Ubangiji ya rufa mana asiri abu daga wannan sai wannan Allah mun tuba ka yafe mana" Maman Alpha ta kalli Ruma ta ce "What's happening to you dear?" Ruma ta miƙawa Maman Alpha gwajin da Dr ya bata, ta miƙe tsaye da sauri bayan ta duba zufa na yanko mata all over herself ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Hasbunallahu wani'imal wakil, what is this? How can that be possible?" Ruma ta sake fashewa da kuka,Maman Alpha ta ce "Don ubanki maza kike bi ko me? Garin yaya haka jama'a mun shiga uku" Cikin Mami ya ƙara juyawa ta miƙe da sauri zuwa toilet a karo na babu adadi Ruma ta ce "Wlh tallahi ni ba ƴar iska bace, bani da lafiya zazzaɓi ciwon kai ga rama shi ne naje ganin Dr ya bani text na na wannan ina dubawa naga the result was positive, amma ban taɓa iskanci ba wlh" Yaya Bilkisu ta ce "Wai dan kwatagwal ubanku meke faruwa ne, kun sa ina jin kamar na yi zayo a wando" Maman Alpha ta ce "Yaya wai fa Hiv ne da ita" Yaya Bilkisu ta ce "Uban uwar meye kuma Hiv, wani abu ne haka" Ta ce "Ƙanjamau fa Yaya" Yaya Bilkisu ta ce "Sunan waye haka kuma ba daɗin ji" Maman Alpha ta lura ruɗewa ta sanya Yaya Bilkisu faɗin hakan, ta ce "Ciwon ƙanjamau fa" Yaya Bilkisu tayi shiru kamar mai tunani ta ce "Hiv, ƙanjamau cuta mai karya karkuwar jiki fa?" Ta fashe da kuka ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, Ubangiji Meke faruwa da iyalan khan ne? ALLAH mun tuba Allah, Ubangiji ka dube mu da idon rahama" Mami ta kasa cewa komai sai ajjiyar zuciya take saukewa, Majeederh kukan tausayin ƙanwarta ya kama ta mance da abubuwan da suka dinga mata, har murna take ta ƙwace mata saurayi, ke nan da tuni itace da wannan wahalar? Maman Alpha ta ce "Ina Imran ɗin to?" Ta ce "Ashe all this year's soldier ne, na air force he just pretend, da aikin shi da iyayensa duk na bugi ne, wani babban aiki ya kawo shi ne wanda zai ɗauki shekaru shi ne ya yanke hukuncin yin aure, before he leave the country, tunda mukai aure bai taɓa cikakken kwana uku a gidana ashe yawon neman mata kawai yake son ran shi, zai zube kayan abinci kuɗi da komai amma babu kulawa bai damu dani ba, idan naga murmushi a fuskarsa to dare ne buƙata ce ta kawo shi, wlh ban taɓa sanin bashi da lafiya ba, i didn't noticed that, wlh ni an cuceni da aka haɗani aure da shi bayan kun san bashi da Iyaye a nan gashi ya saka mini ciwo mutuwa zan yi ban mori komai a duniya ba, ba ɗa ba jika tunda sai zubar mini da ciki yake har ƙwayoyi sun daina aiki a jikina" Gabaɗaya wajan ya yi shiru, aka rasa wanda zai magana musamman Abbu da Mami, shi tunani yake waye kuma Imran ya akai aka bashi auren Rumana? Ruma na kuka ta ce "Me ya sa Abbu? Anti Jeederh Imran ya ce yana so, me ya sa ka bashi kuɗi masu yawa sbd rabo da ita ni kuma ya aureni, why Abbu sbd ni baka so na Anti Jeederh kawai kake so? Kasan halinsa shi ya kaƙi yarda ya aureta sai ni, to ni me na yi maka? I'm not your child or what?" Mami ce ta ɗaga hannu tare da zabgawa Ruma tagwayen maruka ta ce "Enough Ruma, zafin ciwo da ƙaddara ba hauka bane mahaifinki bai yi lalacewar da zaki faɗa masa haka ba" Ruma ta dafe kunci ta ce "Ƙaddara? Me ya sa za ayi wa ƙaddara ƙarya? Bayan babu ruwanta ko da ruwanta to siya mini ita akai, Abbu plan everything, shi ne ya siya mini wannan ƙaddarar" Kuka take sosai, Maman Alpha batai mamakin ƙaddarar data faɗawa Ruma ba, da kuma rashin kunyar da take shimfiɗawa Abbu, ko da Abbu baya cikin hayyacinsa ya yi wa Majeederh all abubuwa da ya yi mata, to fa Ubangiji ya ba zai barshi haka ba, Majeederh yarinya mai tsananin biyayya haƙuri, komai zai ce mata she never said no! To her father. "Ruma what are you saying? Me kike cewa haka? Abbu ne fa your father?" Ruma ta ce "And so f***ck what? Ki saurara mini Anti Jeederh kuma dole ki ce haka sbd ya kuɓutar da rayuwarki ya hanaki auren Imran ni ya bani, sbd ya fi so da ƙaunarki, sbd ya fifitaki daga cikinmu, sbd ke arziƙin shi ce kina kawo mishi kuɗi, to halayyata tayi bambam da naki, I'll take a revenge on it" Ta yi murmushi ta ce "I'm still wondering bayan ga Aaliyyah why he choose me? Wonderful" "Kin san wanne kalaman bakin ki ke furtawa haka Ruma? Ta ya ya kike tunanin mahaifinki zai zaɓa miki mijin da ba na gari ba?" Ruma ta yiwa Majeederh wani wulaƙantaccen kallo ta ce "Zahiri, baki san zafi da raɗaɗin da zuciyata ke mini ba, shi ya sa har kike iya tsayawa a gabana kike fada mini magana banza da wofi, My life is ruined because of you and your father" Majeederh ta saki baki, zuciyarta na tsinkewa sbd jin abinda da Ruma ta faɗa, ta ji ƙirjinta na ya mata nauyi, ta rasa madafa da kuma ma'adanar da zata saka mugwayen maganganun na Ruma, masarrafar da zata samawa jirkitaccen zancen nata tubalin ginawa da kuma fahimtar shi da kyau ya tsaya mata da aiki, tayi jigum da ƙyar kuma ta haɗiye wani bushasshen yawo ta ce "Ruma!" “Baki da iko ko zarafin yi mini ihu akai na, ki barni da abinda mahaifinki ya jaza mini just because of you! Sbd kawai ke†Majeederhn was thinking akan anya Ruma hankalinta ɗaya, ta ja numfashi ta kalli Maman Alpha ta ce "Mene laifina? Me na yi mata da zata alaƙanta hakan dani? Me ya sa kullum zuciyata bata rabuwa da damuwa ne?" Maman Alpha da tayi shiru sbd tashin hankali da mamakin sabon hali irin na Ruma ta ce "Hisabin duniya ya bata nata kason, you sow and you reap†Ta juya ta kalli Ruma ta ce "Kin san duka nan ba sa'anki ko? Ba kuma wanda zai ɗauki sabon iskancin da kika zo da shi, don haka ki saurara ki nutsu ki rungumi ƙaddararki mu taru mu nemawa juna mafita, babu wanda bashi da abinda ke damunsa a wannan rayuwar kin gane? Don haka let by gones be by gones" Ruma ta ce "Wannan ƙaddarar tare daku zan rabata, zaku ce na faɗa muku" Mami ta zabga mata mari zata ƙara mata mari ta ce "Stop! Mami kada ki sake marina, ai kina kallo aka yi auren You neva said anything balle ki yi yunƙurin hanawa" Yaya Bilkisu ta ce "Ah to! Ke banza ce kuma baki zama abar tausayi ba wallahi tallahi, ki fito ki ce sbd a hana Majeederh aure ke ki auro aka tauye hakƙinta aka rabata da shi ta ƙarfi da ya ji ba don bata son shi ba, kuma da rabon ba zai zama Mijin Malama ba, kwaɗayi da son abin duniya ya sanya kika miƙa hannu bibbiyu kika amshi soyayyar shi ba tare da kunya ko shakkar ƴar uwar taki ba, babu kalan wulaƙancin da ba ku yi mata ba sai wanda kuka manta, rashin kunya kowa kamar ba gaba take da ku ba, Kinga kenan hakƙinta ke binki shi ya sa kika tsinci kan ki a haka warrrrr" Yaya Bilkisu ta faɗa tana buga cinya kafin ta kalli Abbu ta ce "Sai ka shirya domin yanzu ka fara gani, ta ce ƙaddarar tare zaku ɗauka ku rabata kashin dankali, amma babu abinda zai samu Majeederh da izinin Allah, ka cire Majeederh daga cikin zuri'ar ka, ka mayar da ita matacciyya bayan tana numfashi a duniya, ka ce baka da wata yarinya mai irin sunan Majeederh, to Allahamdulillah! Ni na ji daɗin hakan gashi nan ƴar cikinka a kan idanunka a gabanka da hankalin ta da komai ta ce bata da haɗi da kai, kayi zaton Majeederh zata lalata maka sunanka dana family ko? To gashi nan ita Ruma ta ɗakko hanyar yin gutsi-gutsi da sunan" Ta juya kan Mami ta ce "Ke ma ishara ce, akan idanunki sukewa Majeederh tsiwa da baƙaƙen maganganun amma sai kin yi niyya kika tsawatar da su, kunnen uwar shegu kike ai, da aka zo da maganar auren Imran hadda ke a