← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 90

Sashe 74

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Khalil ya matseta a ƙirjinta gudun zuciyarsa na ƙara yawa da ƙarfi yana ƙoƙarin kasa riƙe kansa, shi kansa da zai iya kukan zai, sai dai jarumtar shi da ƙarfin zuciyarsa bana kuka bane a gaban matarsa, kukansa zai iya kassara gabɓanta, ya raunata zuciyarta, ya makarantar da ita bayan kasancewarta mai Idanu, ya doɗe jinta, ya zautar da ƙwaƙwalwarta, a hankali yake ɗan bubbuga bayanta can ƙasa yek furta "shiiiyy, shiiiittt" ita kanta ba ji take ba, ya tallafo fuskarta da hannayensa yana kifa tasa fuskar saman tata ya murza hancinsa akan nata a hankali ya fara sauke numfashi yana ƙarewa lip's ɗinta kallo wanda suka jiƙe ga lamp lipstick a bakinta, jikin kukan yaƙi tsayawa gashi bashi da wani option na rarrashi wanda ya a shige “Kiss" a nutse yana sake rungumeta numfashinsu na sauka zuciyarsu na bugawa a daƙiƙa guda ya shiga sauke mata wasu special kisses asalin sumbata kukan ya tsaya ta kalle shi kamar yadda shima ke kallonta a hankali ta rufe Idanunta zuciyarta na buɗewa, gangar jikinta na janta akan linzamin zuciyarta da wani irin firgitaccen sihirtaccen yanayi suka shiga kissing juna da sukkan su da ƙauna mara algus irin son da akewa laƙabi da (eternal true love, pure purity built for God).
Khalil ya yi mata murmushi still yana riƙe da fuskata ya ce "Not every husband is lucky enough to have a wife like you. My whole life I have dreamed of getting a woman like you, The woman who is a perfect homemaker, lovely mother, a successful manager, and the best wife is not a myth; it’s YOU. Thanks for everything, INA SON KI"
Jee ta girgiza kai ta ce "Na fi kowa dace da sa a Khalil, i love you more than anything, Ubangiji ya wadata lemanka ya sanya alheri a ciki, ya rabaka da haramun ya sadaka da halak ya tsarkake zuciyarka a kullum ya baka ikon kula damu, I love you so much &most MAN"
“MAN?” Khalil ya furta yana ware idanu irin sunan bai kwanta masa ba ya jata zuwa wajan cake ɗin tana dariya ta ce "Yes, my stubborn husband mai karya jama'a for know reason" Ya ware Idanu ya ce "No reason? A taɓa ruhin babban likitan kice no reason" Ya miƙa hannu zai damƙota tayi baya ya ce "Funny woman" Ta rungume shi ta baya tana ɓalle maɓallar rigarsa hannunta a kwance a ƙirjinsa ya lumshe gajiyayyun idanunsa ya ce “Sexy mama”
A ranar Majeederh taga hauka wajan Khalil hauka na soyayya idan ta ce cikinta zai iya zubewa babu mamaki, domin wani irin ciwo mararta keyi na azaba da sun haÉ—a ido da Khalil yake kashe mata idanu a lokacin ya faÉ—a mata dukkan wasu plans É—insa na cikin watan Ramadan da yadda zai yi handling ayyukan shi ta sake bashi shawara wacce ya ji daÉ—inta sosai ya sake rungumeta yana faÉ—in "Thanks Malumana"
12:00 aka buga bindiga daga gidan sarki wacce ake shaidawa al'ummar musulmi ganin jaririn watan Ramadana, zuƙata su kwanta da niyar ɗaukan azumi, tun a lokacin daga Khalil ya yi zukuɗi ya zama abin tausayi ta san kuma abinda yake tunani a ransa ta dinga masa dariya bai kulata ba can ya mirgina cinyarta ya ce "Kwana nawa ne ma?" Ta ce "Wata guda ne cif mijin Malama zai azumi" bai kulata ba ta ce "Dame za ka yi shur?" Sbd ya huce haushin da take bashi ya ce "Towon shinkafa miyar kuka a saka man shanu, sai farfesun kai da ƙafa" Ta shafa kansa ta ce "Done" tasan ba zai taɓa cin wannan da daddare ba. Tana fita ya gyara kwanciya bacci ya ɗauke shi na gajiya, ya jima bai yi bacci mai daɗin wannan ba, yana ji tana tashinsa amma ko Idanunsa ya kasa buɗewa Majeederh ta zuba masa idanu ta jima da sanin nauyin baccinsa a hankali ta saka hannu ta jawo tafin ƙafarsa jin ana jan shi ya buɗe ido ba can ba ya ce "What?" Ta ce "Shur" Ya girgiza kai ta ce "pls dear ka samu ladan shur ɗin" Ya miƙe gabaɗaya ya nufi bathroom ya sakarwa kansa ruwa ya fito da towel ya kalleta can ya ce "To time ɗin da a shiga?" Ta girgiza kai sai kawai ya damƙota yana kashe switch ɗin bedroom ɗin. Washegari miliyoyin musulmai dake duniya banda wasu sassan garuruwa suka tashi da azumin watan Ramadan a bakinsu, gari ya sauya yana yi na ibada ya bayyana, tun safe Khalil ya fita sbd zakkar da za a fitar da maganar kayan sallar Orphans ɗinsa da abinda za ayi musu ya kashe kuɗi miliyoyin da bai san kan su. 11:00 ya dawo ya ɗauki Majeederh zuwa Arewa24 akan program ɗin Mata a yau da aka gayyaceta.
Kowa na azumi gaban iyayensa, wasu gidan mazajan su ita kuma ƙaddararta azuminta na farko a gidan yari, bayan fitowarsu kowa da uniform na jikinsa an raba musu aiki, wani gandiro ba ne yazo yana tambayar "Latifa Omar?"
A hankali ta ce "gani nan" ya ce "Kina da vistor" tayi shiru sai kuma tabi bayansa, tsaye ta samu Barrister Aliyu Sufyan Alhassan cikin wani tattausan voyel ya ƙara yi mata kyau fiye da ko yaushe Gandirobar ya ce "5 minutes sir" Aliyu ya ce "Thank you" magana sukai da Latifa a nan yake shaida mata an ɗauke ta daga gidan prison ɗin san zuwa Ikot Ekpene Prison dake Akwa ibom, Latifa Omar ta dinga kuka kamar ranta zai fita daga nan kuma mota aka zuba su ita da wasu akai gaba da su. Lokacin da suka isa gidan yarin tana shiga was the first data tara gani shi ne Mr President..
[11/2, 20:11] Ummu: A zafafe cikin faɗa da wata dakakkiyar tsawa wacce ba a taɓa ji Uncle Bello ya yi ba ya ce "Kin yi kaɗan Barrister, baki da wannan ikon da hurumin, idan har ni na haifi Alpha, kuma Majeederh ƴata ce to aure tsakaninsu ya haramta har gaban abada wallahi tallahi" Yana faɗin hakan yana saka hannu tare da miƙar da Khalil tsaye ya kama hannun Majeederh ya sanya acikin na Khalil, da sauri Khalil ya damƙe hannunta yana sauk'e wata ajiyar zuciya. Majeederh ma ta riƙe hannun mijinta tana Jin kamar ta rungume shi ko zata samu sauƙi a zuciyarta, bata da tension ɗin komai a kanta, ta yarda komai ya faru da bawa hukuncin Ubangiji ne, ba wanda ya isa ya ɗora maka abinda Ubangiji bai nufa ba, wani abun lesson ne a rayuwarka. Maman Alpha ta share idanunta tana kallon mijinta ta ce
"Damuwar wasu ka sani banda ɗan daka haifa? Ashe zaka iya zuba idanu ɗan daka samar da shi ransa ya salwanta akan abinda kake da ikon mallaka masa?" Uncle Bello ya ɗaga mata hannu ya ce "Look! Barrister ban iya son zuciya ba, ba zan fara saboda Alpha ba, idan a matsayinki na Barrister mai kare hak'ƙin ɗan adam da talakawa wanda aka cutar bai sanya kin gane illar abinda kike shirin yi ba, to nima ba zan mara miki baya ba, General musulmi ne yaci ace ya yarda da ƙaddara ya yi kuma imani da ita" Ya juya ya kalli Khalil da kansa ke ƙasa ya ɗora kansa a wuyan Majeederh idanunsa a lumshe Uncle Bello ya furta "Ibrahim ɗauki matarka ka je, yanzu ne za ku yi rayuwar farin ciki da kwanciyar hankali" Khalil ya ware idanunsa a hankali yana mai jinjina kansa.
Uncle ya ƙara haɗe hannayensu waje guda ya ce "Ibrahim da ga yau ka zama tsaki kume gefe na rayuwar Hawwa'u, ka ɗauka bata san kowa a duniya ba sai kai, ka zama garkuwarta, duk sanda Majeederh tayi kuka saboda kai i won't forgive you, idan Majeederh tayi kuka saboda kai to daga ranar zaka san waye Bello,kuje maza kuje daga yau yanzu babu wata matsala da zata sanya hankalinku tashi, ko da akwai zan yi maganinta ba tare da saninku ba, Ubangiji ya yi muku albarka ya baku zuri'a ta gari ya wadataku da arziƙi mai amfani" Idanun Majeederh cike da hawaye ta rungume Uncle Bello ta ce "Na gode Uncle" Uncle ya shafa kanta yana jin sonta har zuciyarsa ya ce
"It's my responsibility dear, ki kula da mijinki kin ji? Duk son da kukewa juna hakan bazai hana ku samun saɓani ba, ki kyautata masa, kiyi supporting nasa always be by his side" Ta jinjina kai, Majeederh ta kalli Alpha dake kwance gefen idanunsa na zubar da hawaye ta miƙa hannu zata taɓa shi Maman Alpha tayi saurin cewa "leave him alone" Uncle Bello ya ce
"Majeederh bi mijinki, I'll talk to her " Khalil ya ɗan matsa kusa da Uncle a karo na farko ya ɗan rusuna with so much respect, saboda Uncle ya masa abinda ba kowa zai masa ba, ya dinga tattaro abubuwan da zai furta a wajen yi wa Uncle Bello godiya da bashi haƙurin dukan ɗan shi da ya yi amma ya kasa, can ƙasa muryarsa so Calm ya ce
"I am sorry" Uncle ya shafa kansa ya ce "I wish you all the best and happiness in your life Ibrahimul-khalil" Khalil ya miƙe ya kama hannun Majeederh suka fita, suna zuwa corridor ya ji ta sake shi ta tsaya ya juya yana zuba mata narkakkun idanunsa, wanda suke cike da gajiya a hankali ya ɗaga mata gira alamar "Miye?" Ta ƙarasa da sauri ta rungume shi tana kwantar da kanta a ƙirjinsa muryarta na rawa ta ce "I love you, I love you Man, na ji tsoro!" Ya riƙo fuskarta yana kashe mata ido ɗaya, yana jin zuciyarta na bugawa, sun jima a haka kafin ya kama hannunta suka nufi reception, Alhassan na ganinsu ya tafi da gudu ya nufi wajen Khalil yana faɗin "Aby" Khalil bai saki Majeederh ba ya ɗauki Alhassan ya ƙarasa inda su Innati suke da su Abbu, Innati ta riƙe haɓa hannunta riƙe da bottle water mai ɗan iskan sanyi sai turiri yake ta ranƙwashi Alhassan ta ce "Algungumi to kai dai ba abokin arziƙi bane a gaskiya, wani abu ne kuma Aby?" Majeederh ta yi murmushi Mami ta ce "Har kun fito?" Ta ce "Eh Mami" Innati tayi ƙasa da murya ta ce "To ya naji ban ji wani ihu yana tashi ba?" Abbu ya kalleta da mamaki a hankali ya ce
"Ihun me kuma?" Innati ta ce "Na mutuwar Soja mana?" Abbu ya sake kallon Innati da mamaki sosai ya ce "Wani ne ya ce ya mutu?" Innati ta ce "To jira nake a fito da gawa fa? Ashe bai mutu ba? Zaman me yake ba gwara ya margaya uban kowa ya huta da rashin tawakkalinsa ba? Wai da gaske yana raye?" Ba wanda ya ce mata komai ta fashe da kuka sosai tana zare gefen zaninta ta ce "Bafa ƴar iska bace ni da zanna magana ana mini kallon wata arniyar legas, kawai a kira dreba ya kai ni gida duk sanda ya mutu na dawo" Khalil ya ɗauke idanunsa wallahi kamar an masa dole dole wajan furta "Zamu tafi" Mami ta ce "Tafiya kuma? Yau ɗin nan Khalil ko can gidanmu ba kuje ba" Jee ta ce "A'a zamu" Ta ce "To shikenan" Majeederh ta amshi Al'hussain ta rungume, Khalil ya kama hannun Baby Khalil su biyar abinsu sukai waje, Khalil ya kalli Majeederh sai ya ɗan kwaɓe fuska ta haɗe rai itama ya miƙa mata key ya ce "Plx" karɓa kawai tayi ta nufi wajen driver, bayan ta ajjiye Al'hussain a baya, baby khalil ma na baya, Alhassan na cinyar Khalil tayi Bismillah tare da yiwa motar key tai reverse a hankali ta harba motar zuwa bakin gate ganin zata nufi hanyar gidan Uncle Bello a taƙaice ya ce "Hubb Lodge Road" Ta kalle shi waya yake dannawa ta ɗauke kanta4d, a jikinta take jin duk motsinta akan idanunsa, tayi murmushi kawai tana mai ci-gaba da driving.
Chapter 74 · 0% Book details