Sashe 15
Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
#Who is the husband?... She looked at him with surprise and excitement baki buɗe take kallon Khalil She couldn't believe that he was in front of her, because he was different from the Khalil she knew before, da sauri ta rufe bakinta tare da ɗauke Idanunta tana haɗe fuska sosai domin har cikin ranta bata ƙaunar sake ganinsa a rayuwarta. Abraham dake tsaye rungume da Baby Khalil ya ɗan ja baya kaɗan yana ƙare mata kallo frm head to toe, ta sauya bakiɗaya ta rame sosai idanunta ya faɗa, sai siririn hancinta da tsukakken bakinta da duk ya bushe, shap ɗin jikinta na nan daram musamman faffaɗan waist ɗinta dake kwance, ya ɗauke idanunsa a hankali kuma ya miƙa mata Baby Khalil ɗin, ta watsa masa harara mai nuna yadda take tsananin tsanar shi, shi dai bai ce komai ba kallonta kawai yake, because He has nothing to say, no words in his mouth. Ta saka hannu ta amshi ɗanta tana sauke ajjiyar zuciya ta rungume shi sosai, Abraham dai yana tsaye hannunsa zube cikin Aljihu Majeederh ta kasa yin shiru da bakinta ta ce "Stay away from me and my son, ban ce kada ka sake dawowa gare ni ba? Ka fita daga rayuwarmu tun kafin nayi maka baki, kasan kamar uwa nake wajanka da nayi maka baki zai bika" Ya yi ta kallonta Calmly ya ce "Ohk" Ta juya zuwa bedroom ɗinta sai kuma ta ƙara juyawa taga ba ita yake kallo ba wayarsa ya zaro daga aljihu yana dannawa a nutse ta ce "Ka fita daga gidan nan, kayi nisa damu, kuma ɗana bashi da alaƙa dakai hakƙin uba na yafe" bakinta dake motsawa ya zubawa idanu a hankali kuma ya miƙe tsaye yana mayar da wayarsu zuwa aljihu, walking slowly ya nufi inda take fuska ɗaure bata taɓa ganin fuskarsa haka ba, ta juya zata shige bedroom ɗin ya yi saurin cafko hannunta tare da bayar da ita baya zuwa jikin bango ya saka hannunsa a both sides ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious yana fita daga jikinsa, ya dinga kallonta ba tare da yace komai ba, tama ɗauka yabar wajan ta buɗe idanu a hankali taga fuskarsa dab da tata kamar zai haɗe fuskokin nasu, tana ɗaga idanunta taga bakinta kawai yake kallo tayi saurin ɗauke fuska gefe ɗaya, silently bakinsa na fidda ƙamshin Spraymintt mouth freshener ya ce "Ohk, kuma nace wajanki nazo? da wani mitsitsin bakin ki" Majeederh dai bata ce komai ba, domin bata son duk abinda zai haɗata da shi. Ya ƙara matsar da fuskarsa dab da nata murya can ƙasa ya ce "Kuma da zaki ce ba ruwana ɗana ke ki kai cikin? Ki biyani cikina da ƙwayayen haihuwata sai na bar miki shi" Cikin fusata ta ce "Ka matsa ka bani waje before I lost my temper" Ya dinga kallonta sai kawai ya juya da sauri tare da barin parlourn, yana fita tana sauke ajjiyar zuciya mayataccen turaren shi duk ya addabeta, ta shige bedroom tana zama saman gado idanunta akan Baby Khalil daya kwaɓe fuska Exlty yadda Abraham yake abinsa tun yana ƙarami ta lumshe idanunsa tana jin soyayyar ɗan ta har cikin zuciyarta, gabaɗaya yanzu bata son aure tana son ta rayu haka tunda Allah ya nuna mata ɗanta na cikinta, ta fahimci babu komai a cikin aure sai tashin hankali ba soyayya babu kulawa. Anti ce ta shigo ta sameta tana jijjiga baby khalil dake kuka yana harba ƙafa Anti ta ce "Au ke ya kawowa?" Majeederh ta kalli Anti bata ce komai ba ta ce "Ai tun safe Abraham ke gidan nan a part ɗin Jawaad ya dameni wai ina ɗan shi, na faɗa masa yana gidan Uncle Bello babu jimawa sai gashi rungume da yaron, wannan mugun kamar da Abraham yake da yaron nan ya ɓaci kamar shi ne yana ƙarami" Majeederh ta haɗe fuska tamau ta ce "Plx Anti ki daina haɗa my son with someone else" Anti ta riƙe baki ta ce "Au haba? Dole ya amsa sunan Ibrahim Ibrahim, ko kuma Ibrahim I Khalil kuma kin manta ke kika saka masa sunan? Kuma dole a cewa mijin iya baba ba zaki hana duniya faɗar cewa ɗan Abraham bane" Majeederh ta ce "Ɗana tsarkake ne, shi daban wancan daban" Anti ta gyara zama sosai ta ce "To Albishirin ki Abraham ya musulunta, yama jima da zama Muslimi ya sauya gabaɗaya daga yadda kika san shi, ke banda ya sauya tunda yazo gidan nan ai wajanki zai fara zuwa amma ko sunanki bai ambata ba balle kuma yace kina ina, he just asked where's his son, kuma shi ma yasan ba zai sameki ba, da Jawaad yana basa labarinki bayan barinsa garin da kuma labarin mutuwar aurenk ko ƙala bai ce ba, ya kwanta tare da yin shiru kamar bacci, sallah bata taɓa shige shi akan lokaci da jami'i, so ki kwantar da hankalinki He didn't come because of you, he came because of his son, Stop the small talk and shrug" Anti ta miƙe tsaye har taje bakin ƙofa ta tsaya ta ce "Uncle yana kiranki" Gaban Majeederh ya faɗi ta ɗan marairaice ta ce "Plx ki ce bana jin daɗi" Da wani irin kallo Anti ta ce "Tell him by yourself" Tana faɗin hakan ta fice, Majeederh ta runtse Idanunta tana zuciyarta na bugawa sosai tasan rabuwarta da Abuturab alheri ne tunda ta roƙi Ubangiji ya zaɓa mata mafi alheri, bata son ta shiga layin matan da za'a dinga lissafawa Aure, bata ji daɗin aurenta da his Excellency ba, bata san farin cikin dake cikin aure ba, ta gama karaya tasan bata da rabo da farin ciki bata da rabo na ladan dake gidan miji. Da ƙyar ta miƙe ta nufi parlour ta samu Uncle Isma'il zaune shi da Uncle Bello suna magana a hankali suna ganinta sukai shiru,ta zaune ƙasan carpet kanta a ƙasa bayan ta gaishe su Uncle Isma'il ya ce "Hawwa'u" Ta kasa amsawa sbd fargaba ya ce "Kamar yadda na faɗa zan ƙara, wallahi wallahi Allah a gobe zan aurar dake, daman furniture's ɗinki da kayan kitchen da komai suna nan, abu ɗaya zan faɗa miki inma ki fitar da gwani a cikin su, Mai martaba Ajlaal Sultaan, Barrister Aliyu Sufyan, Engr Junaid, ko kuma Dr Ibrahimul-khalil, ko kuma na aura muki wanda ya fara zuwa ya saman wato Mai martaba" Majeederh ta rasa waye wani Dr Ibrahimul-khalil, idan ta auri Aliyu bata kyautawa kanta ba darajar Latifa a wajanta ta shige ta auri mijinta, idan ta ce Mai martaba kuma da wanne idanu zata kalli Ƙhulud Arzaan? Wacce ta ɗauketa matsayin ƴar uwa kamar Aaliyyah da Ruma da Raihana da su Sona, Du'a, Widad da Sahar? Idan kuma ta ce Engr Junaid bata san halinsa ba infact she don't even know who he is? Uncle Bello ya numfasa ya ce "Kina da lokacin daga nan zuwa Subhi, ki yanke hukuncin da kike ganin ya dace dake Hawwa'u, ki dai sani a wannan karan zaki rayuwa da wanda yake son ki ne, kuma a yau kowa zai zo ya sameki ki bashi lokaci ku tattaunawa, but am sure you'll like His Highness" Uncle Isma'il ya girgiza kai ya ce "Definitely" Ita dai bata ce komai ba suna zaune Jawaad ya shigo ya ce "Uncle na sauke shi a special parlourn gidan nan" Uncle Isma'il ya ce "Ok zata zo" Ya juya ya kalli Majeederh ya ce "Ga can Mai martaba kije yanzu ku gaisa" Majeederh ta marairaice ta ce "Uncle ni ban son auren please" Wata kyakkyawar tsawa ya daka mata jiki na rawa ta miƙe zata fice ya ce "A haka zaki? Idanu buzu buzu duk a jime" Ta ce "To ya ganni a haka" Uncle Bello mamakin Majeederh yake kwana biyu ta sauya ga saurin kuka ga magana kai tsaye, ko mene dalilin sauyawar nata? _Only God knows!_ A hankali ta shiga parlourn bakinta ɗauke da sallama cikin siririyar muryarta, ta shiga kanta a ƙasa bata yadda sun haɗa idanu da Mai martaba Ajlaal Sultaan ba. Shi kowa yana zaune hakimce saman kujera ya ɗan kishin giɗa, jikinsa da wata farar jallabiya ya ɗora hirami a kansa sai ƙamshin perfume ɗn Jean Paul Gaultier sai lumshe idanunsa yake, tunda kuma ta shigo yake kallon fuskarta a karo na farko har ya gaza ɗauke fararen Idanunsa duk da irin basarwa ta Mai martaba, maganarta ya dawo dashi daga tunaninsa da take cewa "Gani" Kamar bai jita ba haka ya yi shiru yana mai da idanunsa tare da rufewa, Malama Majeederh ta ɗago kai tana kallonsa tana mamakin girman kai irin na Mai martaban, ko da yake ba laifinsa bane jinin sarauta dake yawo a jikinsa ne. A hankali ta ce "Gani" ba tare daya buɗe idanu ba ya ce "Kewa?" Ya ja numfashi ya ce "Suwa suka kira ki?" Ta ce "Ohk Maybe mistake ne" Tana faɗin hakan ta miƙe tsaye har ta je bakin ƙofa ta ji ya ce "Haw...wah" Cak ta tsaya a hankali ta dawo ta zauna, ya gyara ya zama yana buɗe ido calmly ya ce "Mun gani, mun yaba, muna son aura" Majeederh ta kasa Kallonsa sbd kwarjini ganin haka yasa ya ɗan gyara murya ta ce "Ƙhulud? ba zan iya mata haka ba" A hankali ya ce "Su waye haka? Oh Fulani kawai amincewar ki muke nema" Ta ce "Zan yi tunani" Ya jinjina kai he can't stop himself wajan kallon riskarta Bai ce komai ba tasan ɗin bazai tanka ba, har zuciyarsa yake son Majeederh amma yanzu tunani kala daban daban ya shiga kansa, ya miƙe yana tafiya a nutse sai da yaje ƙofa ya ce "Kuyi tunani mai kyau". Yana faɗin hakan ya fice ta bisa da kallo koman shi a nutse yake, ta jima kafin ta miƙe tana fita entrance na gidan taga Aliyu tsaye shi da yayansa Almustapha sun saka kaya iri ɗaya, Almustapha ne kawai yake magana amma hankalin Aliyu na kan Majeederh tayi kamar bata gansa ba, Almustapha ya ce "Assalamu alaiki" Ta tsaya tana amsawa can ƙasa bayan sun gaisa da Almustapha Aliyu ya ƙarasu inda take ya ce "Kin gama guje gujen?" Ta kame fuska bata ce komai ba ya marairaicewa fuska ya ce "I will ask for your help again and