← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 90

Sashe 16

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

again, Hawwy, help my heart and accept me as your husband" Tayi shiru yana sauke numfashi murya kamar mara lafiya ya ce "Don Allah, don Allah ki taimaka mini ina son ki Jiddatul-khairy, bani da zaɓin zuciya sama dake tunda na fara haɗuwa dake har yanzu bani da ishasshiyar lafiya, bana cikakken bacci, bana cin abinci sosai wlh ko maƙiyina a duniyar ba zan so ya kamo da irin wannan son mai zautar da mutum da son kai shi kushewa ba, i loves you ina son ki" Wani irin tausayin Aliyu ya kamata domin kaf cikin su tafi tausayin shi yana da wata kalar zuciya mai sanyi da son kyautatawa mutum a hankali ta ce "Baka taɓa cewa kana so na ba sai yanzu?" Ya girgiza kai ya ce "Ba zaki gane ba, ki fara amince mini zan yi miki bayani amma ko Latifa darajarki take ci" Ta kalle shi sai ta ce "Thank you, yanzu ma taci gaba da cin darajata" Ya yi saurin durƙoshewa gabanta ya ce "Ki duba Allah ki tausaya mini, zan nuna miki cewa baki asara ba, zan baki farin cikin da kika rasa zan nuna miki so da ƙauna, ban miki al'ƙawarin fari na har abada ba, amma daga gareni zaki ta samun kwanciyar hankali, Ina son ki ina tsananin ƙaunarki, zan ma kira Hajia da Papa su baki hakuri, ga Yayana Almustapha he's here to ask ur help, zan kira Anti Biba, Anti Rahmerh, da Antin Turkey su baki haƙuri kada ki wofintar dani Please" Idanunta ya cika da hawaye Almustapha ya ce "Plx Malama Majeederh a baya bana son tarayyarku amma yanzu na amince bana ƙasar ma sbd ke na dawo ki tausayawa Abokina aminina my younger brother idan wani abu ya sameshi ba zan yafe miki ba" Majeederh jikinta duk rawa yake ta ce "Am sorry ba zan iya auran mijin Latifa ba, wlh duk duniya zata haɗu ban iya auren mijin Bestie yadda Abbu ya haramta a gareni haka Aliyu, Am sorry" Tana faɗin hakan tai cikin gidan Aliyu zai bita Almustapha ya yi saurin riƙe shi sai kawai ya faɗa jikin yayan nasa yana wani irin kuka kamar zuciyarsa zata fito..... Anti ce tsaye waya kare a kunnenta ta ce "Yawwa duk yadda za ka yi kai ka sani ka tabbatar Abraham bai auri Majeederh ba, ka sanya masa soyayyar Sona a zuciyarsa, kamar yadda Alpha ya tattara kayansa yabar garin yace baya so kasan duk yadda kayi kasa Abraham yace baya son Majeederh, ai kace mini shi ɗin ɗan babba mutum ne? Yana da nasaba mai girma ga uban dukiya?" Magana akai ta cikin wayar can ta ce "Good, sau biyu aikin ka na bani matsala gashi Kuɗi dai ina baka sosai kamar hauka, nace ka saka Majeederh ta zaba karuwa ta ƙarfi da yaji amma kace ba zai ba, saboda ƙarfin addu'a da azkar ɗin da take, hakan yasa ƙaddara tazo ta sauƙi maimakon ta zama karuwa sai akai rapped nata, kuma....," Da sauri ta ajjiya wayar ta ce "Jawaad how many zance ka daina faɗo mini without my permission eh?" Ya ce "Sorry Maa, dinner is ready" Ta haɗe fuska ta ce "Fice ka bani waje kai ta abu kamar zautacce" Ya fita zuwa dining room. Majeederh ta fito sanye da duguwar riga wacce ta bi jikinta sosai fuskarta fresh kana ganinta kasan akwai damuwa a tattare da ita dan dai jaruma ce kawai, kai tsaye ta nufi dining room ɗin cak ta tsaya ganin Abraham zaune ɗare ɗare akan kujera suna ta tafka uban musu da Jawaad Uncle Isma'il kuma na zaune yana ta musu dariya wannan yace shi ne babba wannan ya ce shi ne babba. "Majeederh ƙarasu mana" Tsit Abraham ya yi kamar bashi a wajan ya zaro wayarsa ya shiga dannawa fuska haɗe babu alamar fara'a kafin ta zauna Uncle Isma'il ya ce "To Antin bata ƙarasu ba, ki zuzzuba mana abincin" Ta yi jim sai kuma ta zubawa Uncle Isma'il ta zubawa Jawaad ta zuba nata kaɗan, tana neman wajan zama Uncle Isma'il ya ce "Wa zai zubawa Ibrahim ɗin?" Ta ce "Uncle.." Ya ce "Ranki zai ɓaci" Ta miƙe ta nufi gefen tare da ɗakko plate ta shiga zuba masa, shi dai Khalil wayarsa kawai yake dannawa Uncle Isma'il na kallon tulin abincin data zuba masa tare da nama da yawa ta ciccire albasa da tumatir "Ya kika cire masa kuma?" Tana ajjiye spoon ta ce "Baya ci" Kallonta Uncle Isma'il da Jawaad kawai sukai tana gamawa zata bar wajan a hankali ta ji muryarsa daidai kunnenta ya ce "Thank you" Ko su Uncle Isma'il ba su ji ba, Jawaad nata yi wa Khalil surutu daman haka yake shi kamar aku, Abraham daman baya wasa da cikinsa abinci kawai yake ci sai da ya cinye abincin tas ya sha ruwa ashe tuni Uncle Isma'il yabar wajan sai Majeederh dake ƙoƙarin tashi "Hawwa'u" Dam! Zuciyarta ta buga jin sunanta raɗau abakin Abraham, ta juya da sauri da tunanin ko bashi bane suka haɗa idanu ya harɗe hannunsa a ƙirji, Jawaad ya bar wajan tayi tsaki zata bar wajan ya ce "Kina barin wajan nan ni dake ne" Ta wani kalle shi ta ce "To sannu ubana" Ya girgiza kai ya ce "Ki zauna magana nake so mu yi, bana son kuma kai hannu jikin ki balle aja mini aya" Ta ƙara jan tsaki rai ɓace ta ce "Kai da jikina har abada yaro" Ya miƙe tsaye ya ce "Idan dai kika sake hannuna ya taɓa ki to ko Uncle I da Uncle B basu isa su ƙwace ki ba" Ganin yana nufuta yasa ta juya da sauri zata bar wajan ya saurin saka mata ƙafa kamar zai taɗeta ta faɗi da sauri kuma ya cafko gaban rigarta yana haɗuwa hatta bra ɗinta tayi kamar zata faɗa ƙirjinsa ya saurin ɗan baya ya riƙe waist ɗinta sosai ta ce "Zan baka abinda bakai tunani ba, sbd kai ɗan yau ne daman ance ka haifi yaro banda halinsa wlh..." Hannunsa yasa ya cafke lip's ɗin nata tare da murɗewa azabar da taji yasa tayi saurin riƙe masa ƙugu da duk hannunta jikinta idanunta ya yi rau rau sai da ya murɗe mata bakin son ran shi kafin ya saketa ai kowa lip's ɗin sukai jajur sosai suke mata azaba takaici yasa wani irin hawaye zubu mata, Abraham ya tallafo fuskarta kamar mai raɗa ya ce "It's hot?" Ta yi masa shiru ya ƙara leƙa fuskarta silently ya ce "What??" Sai kawai ta fashe da wani irin raunataccen kuka na zallar takaici jawota ya yi jikinsa ya rungumeta zata ƙwace ya ƙara matseta a jikinsa gabaɗaya baƙin ciki ne yasata kuka gashi bata da wani ƙarfin kokawa dashi ta runtse Idanunta taja jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi "Gobe za mu yi aure, ni ba zan wani tsaya roƙanƙi ba kamar su dole ya zame miki yarda" Da dukkan ƙarfinta tasa ta hankaɗe shi, ta ce "Wallahi na tsaneka bana ƙaunar ganinka dana aureka gwara na zauna ba aure ko na auri wani, ko bakai mini komai ba kayi mini ƙanƙanta da zama mijina ɗan cikina sbd kai baka da kunya wani ɗan mitsi-mitsi dakai har kai ka isa yin aure ba, wlh bana ƙaunarka" Tana faɗin haka ta shige Khalil ya zube yana riƙe kansa fargaba da tsoran rasa Jee ya wanzu a zuciyarsa... Da asuba Uncle ya tambayi Majeederh me ya yanke? Sai ta ce masa ta amince da Ajlaal shi take so, Sosai Uncle Isma'il ya ji daɗi domin shi ma Ajlaal ɗin ne ya kwanta masa, daga nan ya kira Aliyu ya bashi haƙuri akan ba zai taɓa yiwa Majeederh auren dole ba, daga nan ya kira Khalil har Parlour shima ya kura masa bayani akan ya bawa Ajlaal Sultaan auren Majeederh, Khalil kasa magana ya yi sai jikinsa daya ɗauki rawa da sauri ya fice ya nufi hotel ɗin da Mai martaba Ajlaal Sultaan ya sauka, sosai ya dinga neman afuwa akan Ajlaal ya haƙura ya bar masa Jee ɗinsa amma fur Ajlaal ya ce "Sorry, i wishe you all the best da zan iya dana bar maka ita, but muma muna sonta" Abraham kamar zai zauce wani zazzaɓi ya rufe shi, shikenan ya rasa Majeederh ya rasa Ƴar Madara ya rasa Maluma da ƙyar yakai kansa gida.... Gidan Uncle Isma'il ya cika da ƴan uwa hadda Mami su Raihana da Ruma kowa na family Abbu ne kawai babu, kowa jira yake ji waye MIJIN MALAMA? Tunda duk basu san shi ba... A Masjid ɗin dake layin gidan Uncle Isma'il ake ɗaurin auren abun mamaki manyan mutane sosai ta ko'ina kamar wanda jima ana sanar da ɗaurin auren, cikin masallacin cike yake sosai da mutane, Aliyu Sufyan Alhassan yasha wata dakakkiyar shadda yana zaune gefe, ga Mai martaba Ajlaal ango ya shafa farar shadda sai ɗaukan idanu take, abin mamaki hadda Abuturab wanda da gayya Uncle Isma'il ya kira shi, Jawaad na gefe daga can ɓangaren Abraham ne durƙoshe yasha wata shadda fara tas kusan iri ɗaya data Mai martaba jikinsa duk rawa yake zuciyarsa na bugawa amma ya yi imanin Jee ba rabon shi bace Maybe Allah ya haɗa su don ya rabauta da addinin musulunci bawai dan ya zama mijinta ba hakan yasa ya haƙura...... Manyan mutane da liman ne suke magana a hankali Abraham ya miƙe da sauri zai fice daga cikin Masjid ɗin daidai nan Liman ya ce.....
Chapter 16 · 0% Book details