Sashe 56
Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Bari na rage muku zafin weekend Arewabooks sun shige ku da shafi 7 ya haka🤣🤣
*_Arewabooks@Nimcyluv_*
Uncle Isma'il ya goge zufar data yanko masa, duk da juriya irin ta shi da jarumtar shi a kullum a koda yaushe, bai hana shi sunkuyar da kai ba sbd hawayen daya taro cikin idanunsa ya ce "Alhj Abdul'aziz ka taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo? Bayan matarka daka bunne da hannayenka wacce matar kake nufi eh?" Abbu ya girgiza kai, yana damƙe photon hannunsa idanunsa ƙurr akan Gimbiya wacce ko kallo bai isheta ba, daman ba komai ke jan hankalinta ba, masifaffiyar jinkima ce da ita ga taurin kai da zafin zuciya, Abbu ya kalli wan nashi ya ce "Isma'il karka ce mini na haukace ce don Allah, bayan gaskiyar da Idanuna suka shaida mini gashi nan gata nan tana motsi, tana magana my wife is still alive Isma'il" Uncle Isma'il ya girgiza kai cike da damuwa ya ce "Idanunka sun yi mika ƙarya, ko baka haukace ba babu shakka ka fara zaucewa, zatonka ya saɓa lissafin da zuciyarka ke maka, Fulani bata duniya ka sani mun sani, she's no more" Abbu ya yi shiru sbd komai ya tsaya masa daga aiki cak, jijiyoyin dake sarrafa ƙwaƙwalwar zuwa wanzar da tunani mai kyau ta ɗan ta kata masa da aiki na zuwa Shuɗewar daƙiƙo, Uncle Isma'il ya kama shi ya zaunar,kowa ka gani a parlon ya girgiza. Calmly Mai martaba ya ce "I can see the picture?" Uncle Isma'il ya miƙawa Mai martaba Ajlaal Sultaan, ya amsa tare da ɗora dara-daran idanunsa akai, wat kyakkyawar bugawa zuciyarsa tayi da ƙarfi a zaune yake amma sai daya nemi miƙewa tsaye Gimbiya tayi saurin damƙe hannunsa, domin duk wani abu na zubar da ƙima bata haɗa hanya da shi ba, duk girman abu tana iya haɗiye ta gwammace ya illata zuciyarta da a fahimci rauninta, a fili cikin ƙasa da murya ya furta "Samra" ambatar sunan Samra ya sanya Zaytoon zaro idanu waje cike da tsoro da fargaba, Rohaan ya yi saurin jingina da kujerar dake kare da gangar jikinsa, yana jin kamar duniyar ke juyawa masa, Gimbiya ko motsi ba tayi ba sai zufar dake tsastsafowa ta saman hancinta wanda ke bayyana asalin tashin hankalin da take ciki, Mai martaba ya kalli Uncle Isma'il ya ce "Ita ce ya rasu?" Uncle Isma'il ya jinjina kai, Mai martaba ya yi shiru yana kiran sunan Allah gabaɗaya zuwa Nigeria da suka yi ƙaddara ce, rashin sani ne, salwantar da RUHI BIYU ya ƙaddara zuwan nasu, ya kuma wargatsa farin cikin zuciyoyin su. A hankali ya ce "Samra da Hawwa'u biyuni ne, tagwaye ne ciki ɗaya ne ya kawo su duniya, rana ɗaya, wata ɗaya, shekara ɗaya, irin biyunin da ake cewa Identical twins, gane kamar su zai maka masifar wahala, Mahaifinmu Sultaan ya auri mahaifiyarmu Balarabiya ce, amma bata Saudiya ba Larabawan Diffa,wanda aka fi sani da larabawan Mahamid" Ya yi jima na wani lokaci kafin ya ce "Larabawan Diffa suna magana da larabci ne, kuma suna Balarabiya, amma ba su da alaƙa da Larabawa na yankin Maghreb na Afirka ko Larabawan Gabas ta Tsakiya, asalin su ƴan Sudan ne dalilin farin da ka yi a 1974 na Sahelian, hakan yasa suka nufi Diffa,sannan wasu da ke gujewa yaƙin basasa a cikin ƴan Sudan ɗin da rikicin Chadian da Libya a cikin shekarun 1980, suka zauna kusa da Diffa . Shugaban Ƙasar Nijar na farko wanda ɗan asalin Diffa Arab ne Mohamed Bazoum, bisa wannan dalilin da kakanmu mahaifin Takawa yaje Nijar yankin Diffa sai Babana Takawa kenan Sultaan ya haɗu da mahaifiyarmu har sukai aure, a haka kakanmu ya rasu aka bawa Mahaifinmu Sultaan sarautar Saudiyya, nine wanda ya fara haifa sai kuma Twins Samra da Hawwa'u, haɗuwar jinsu biyu kuma duka Arab sai Ubangiji ya bamu wani irin sahihin kyau musamman biyuni, wanda kuma kyan nasu ya jawo musu matsala da yawa, bayan haihuwar su aka haifi Rohaan autanmu kenan, iya mu kenan, kuma mahaifiyarmu ta rasu a haihuwar shi ne, Yayan ƙanin Mahaifinmu wanda ya kasance uba ga matata Ƙhulud ya raini Rohaan, wani babban uzuri ya kawo mu Nigeria wanda kuma a nan ne muka rasa biyuni lokaci mun shiga tashin hankali wanda baki ba zai iya faɗuwa ba, zuciya ba zata iya ɗauka ba, rauni ya mamaye zuƙanmu ruɗewarmu ta bayyana a sarari sai Mulki ya samu tawaya Takawa ya fara rashin lafiya rashin" Mai martaba Ajlaal ya yi shiru cike da damuwa yana jin kamar a lokacin ne komai yake faruwa, dal yake ganin hakan a cikin idanunsa.