← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 90

Sashe 25

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Maman Alpha na fita ba je ko hanyar inda tasha take ba ta nufi Lodge Road gidan Abbu, ta samu Mami zaune a parlour tana kallon My better half a telemundo "Zuwan bazata har haka?" Maman Alpha tayi murmushi ta ce "Wlh, Yaya Bilkisu bata zo ba?" Mami ta ce "A'a tace zata zo ne?" Maman Alpha ta ce "To maybe ta fasa, daman Hawwa'u ce taƙi kwantar da hankalinta ta amshi khalil matsayin mijinta" Mami tayi shiru sai kuma ta ce "Ina saka kaina a matsayinta, abun ne da girma ba auren wanda ya girmeta bane matsala, a'a ko kaɗan the problem is ita ce ta raine shi, tana jinsa har yanzu kamar ɗanta her little bawai husband ba" Maman Alpha ta ce "Amma kam dai kin bani mamaki Hajiya Asabe, faman ƙaddarallahu hakƙa ƙadrihi, babu wani abu daya isa ya samu bawa face abinda Ubangiji ya ƙaddararta masa, ki ɗauka Majeederh ƙaddarar Khalil ce, shi ma ƙaddararta ce, Allah ne kaɗai yasan abinda wannan auren zai haifar tunda har aka yi shi, idan muka yi ja wannan al'amarin kamar muna ja da hukuncin Ubangiji ne, kuma wlh Majeederh na son mijinta tunda har ta iya dakatar da Abban Jawaad daga marin Khalil, idan har ba Ubangiji ne ya haramta auren ba bai kamata mu da kanmu mu haramta shi ba, babu aya ko hadisin dake nuna haramcin haka" Mami ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "You're right kina da gaskiya Barrister" Abbu ne ya shigo sanye yake da babbar riga da Jamper ta wata dakakkiyar shadda shampo light blue ya ɗora hula akansa, ya ɗan yi jim Mami ta ce "Sannu da shigowa Alhji" Ya zauna Maman Alpha ta ce "Barka da gida Alhji" Ya ce "Kina lafiya?" Ta ce "Allahamdulillah" Ta gyara sosai ta ce "Ducoments da dukan wasu files na takardun Majeederh nazo amsa, date of birth, voter card, national ID card, tun daga kan primary zuwa diploma nata ka bani duka gabaɗaya, ba ruwana da award data samu da keys ɗin motocin ta ba ruwana" Tunda ta fara magana Abbu ke kallonta ya ce "Kee Bello ya turo ki? Ko Isma'ila, to na hana na ƙona tuni" Ta ce "Photocopy ka ƙona, at this time ba zan zuba idanu ba, babu wanda ya turo ni na kuma sauke matsayin ƙanin miji nazo a matsayina ta Barrister kuma ɗaya daga cikin shugabannin kungiyar human rights ta reshen jihar Kano" Ya ce "To na hana" Ta ce "Ohk daman na fara binka ne a hankali za kaji kira daga human rights kuma wlh da kanka zaka jawo a ɗaure ka, ina record ɗin abinda kai kanka baka san da shi ba, at the end a matsayinka na uba duk da ka faɗawa duniya baka da ƴa Majeederh to yana da kyau ka sawa rayuwar auren ƴarka a albarka hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, dole ta amsa sunan Majeederh Abdul'aziz Khan!" Abbu ya riƙe kansa da sauri sbd tsara masa da yaji ya yi kamar zai tsage ya miƙe da sauri yabar ɗakin.
Khalil na zaune a parlourn Maman Alpha tun zuwansa gidan ko motsinta bai ji ba, hannunsa kuma ɗauke da Baby Khalil wanda ya yi wayo sosai har ya fara zama tuni Sallama ya ji an yi ya haɗe fuska sosai Latifa ta shigowa tana murmushi ta ce "A'a Mijin Malama ne a gidan" Bai ce mata komai ba tayi ƙasa da murya ta ce "Hala baka samu cikon gidan hayar bane shi ya sa take ta zaune bata tare ba? Kuma kaje ka nemi taimako wajan jama'a? Kana don Allah su taimaka aure kayi kuma baka da ko sisi na zaman gidan haya da abincin da zaka bawa matar?" Khalil dai bai ce komai ba idanunsa akan Baby Khalil dake ja masa saje ya miƙe tsaye akan cinyoyinsa Latifa ta ce "Allah sarki ai talauci babu daɗi masifa ce sosai, da kuma zaman banza ai ko ɗan dako da ina shara daka fara" A hankali ya ce "Ohk" Maman Alpha ce ta fito daga bedroom tana murmushi ta ce "Latifa ce?" Ta ce "Wlh ina Bestie?" Ta ce "Ai da kam tana nan parlour zaune" Kafin su sake magana T.v dake kunne a channel ɗin Arise News aka shiga sanarwar zuwan President of Germany ƙasar Nijeriya a gobe Sunday, har yanzu ba a san dalilin zuwansa ba amma na tunann yazo ganawa da shugaban ƙasar Nijeriya ne akan harin da za'a kai ƙasar Nijar" Latifa ta washe baki ta ce "Wow shugaban ƙasar Germany a Naija? Ai wallahi da ina gidan jaridarmu ni ce ta farko na buga wannan ƙyakƙyawan labarin, kuma mutumin nan baya tsofa sai uban arziƙi kamar yaƙi gashi baya da ɗa balle jika" Khalil dai jin labaran kawai yake amma hankalinsa a tashe yake yasan wajansa yazo yana ji a jikinsa ba haka nan zai zo ba, zai zo ne ya raba shi da Majeederh. Latifa ta ce "Khalil dubi shugaban ƙasar nan plx gaskiya arziƙi ya yi" Gently ya ɗaga kansa ya kalli Dad ɗinsa da ake ta nunawa sai kuma ya miƙe tsaye ya nufi bedroom ɗin da Majeederh ke ciki tsaye ya ganta hannunta riƙe da waya hankalinta ya gama tafiya akan wayar har ya tsaya a bayanta yana kallon chat ɗin da suke, a hankali idanunsa ya sauka akan Abuturab wanda kuma da shi take chat ɗin. Ya duba reply da take masa na "Plx help Ur Excellency i couldn't sleep, ka faɗa mini sunan maganin da kake bani nake bacci sanda nake gidanka" Wani irin huci ta ji a bayanta kamar na kumurcin maciji ta juya da sauri idanunta ya sauka akan Khalil da yake tsaye dab da ita, kallonta kawai yake babu ƙiftawa jikinta ya ɗauki rawa domin tun bayan abinda ya faru ranar juma'a take ɓoye masa a hankali ta ce "Sorry....," Hannu ya ɗaga mata murya bata fita sosai ya ce "A Medicine? What medicine? Yaushe kika fara sha waya koya miki sha?" Gabaɗaya jikinta rawa yake ta shiga girgiza masa kai, idanunsa kamar za su fito waje ya daka mata wata razananniyyar tsawa ya ce "Stop nodded your head" Ya faɗa da ƙarfi wanda yasa ɗakin ya amsa gabaɗaya ya birkice ta rasa yadda za tayi sai kawai ta faɗa jikinsa ta rufe fuskarta a ƙirjinsa tana ƙanƙame shi, shiru kawai ya yi mata deep down na zuciyarsa tunanin wanne magani ne da har yake sata bacci? Da tunanin yadda zan ci uban Abuturab ba ruwansa da matsayinsa. Ya zame ta daga jikinsa ya juya mata baya domin bai fiya son ta gane ita ce weakness nashi ba, ya jima a haka kafin ya fita. Mutanen parlourn yaga sun ƙaro, Uncle Isma'il da Uncle Bello da Yaya Bilkisu har lokacin Latifa na nan. Ya nemi waje ya zauna can ya ce "Evening uncle's Aunties" Uncle Bello ya ce "Ibrahim kana son ɗaukar matarka, gashi har yanzu bamu mene problem naka da reason naƙin kawo mahaifinki ba, munsan kakanka David amma ko shi yaushe rabon da muji shi? Nama yi tunanin zai zo da yaji labarin auren, kuma kaga mu ba zamu so muga mun bada Majeederh inda zata wulaƙanta ba, ko kuma ba asali ba toshe, wannan shi ne babban kuskuren da iyaye suke, su bada yaransu hankali kwace basu san waye familyn miji ba, sai an tara zuri'a kuma al'amarin ya ɓaci, a yanzu mahaifinka yazo a yau zaka tafi da matarka" Kansa a ƙasa shi kam ya zai yi ne su fahimce shi? Ko cewa ya yi President babansa sam ba zasu yarda ba "Khalil magana muke?" Ba tare daya ɗago kansa ba ya ce "What's the problem Uncle? I have a house to keep her in and take care of her" Latifa ta ce "A'a yanzu fa kace baka gama haɗa kuɗin hayar gidan ba" Ya juya ya yi mata wani irin kallo ya ƙara cewa "Na maka al'ƙawari zan bata komai" Nan ma Latifa ta ce "Ko abincin da zaka bata baka da shi kuma....," Kafin ta ƙarasa maganar ta ji saukar lafiyayyen mari a fuskarta ta dafe kunci zata sake magana ya ƙara sauke mata wani yana huci ya ce "Na tsani Shisshigi, kin dame ni haba idan Jee kike son ta wahala to bata nan zaki bi ba" Ya nufa mata ƙofa ta miƙe da sauri ta ce "Wlh sai na haɗaka da mijina za kaji sammaci daga Curt mai yawo a titi bashi da ko sisi" Ya ɗaga ƙafa kamar zai bita ta kwasa da gudu tai waje jini har ya kwanta idanunta. Baki sake kawai suke kallonsa Yaya Bilkisu ta ce "Khalil ka rage zafin zuciya, kasan mijinta waye? Babban lawyer ne ba, uban mijinta kuma wani babban ƙosa ne a gwamnati kai da baka da kowa daga mu sai Allah da Manzonsa shi, yanzu me tayi maka wacce kalar wahala aminiyar Majeederh ce fa?" Maman Alpha ta ce "A bar maganar kawai Yaya" Uncle's ɗin kasa magana sukai, Khalil ya koma bedroom Uncle Bello ya ce "Me zakai?" Silently ya ce "I'll be back" Ya shiga da sauri yana saka key ya duba agogon hannunsa yaga it's too late, what should I do? Ya tambaya a zuciyarsa, ga babansa alrdy yana Naija rufe zuwan nasa kawai sukai a tunaninsu gobe zai zo, ga Uncle's da suka hana shi matarsa da sun bashi ba zai taɓa yarda Dad ya same shi a ƙasar nan ba, Majeederh tayi saurin tashi kanta a ƙasa tana tsaye taji ya kama hannunta ya zura mata hijabi har ƙasa, ya jawo flat shoe ɗinta ya saka mata, ya juya har zai bar wayarta ya yi tunanin tana da muhimman abubuwa a ciki ya ɗauki wayar ya saka cikin Aljihu, wayarsa ya ɗauka ya turawa Joshua Dm, ya shiga toilet ya kunna shower ya saketa tana zuba ita kaɗai, ya yi kamar wanka ake, ya ɗauki jotter da pen ya yi short note da sign ɗinsa ya ajiye saman bed Majeederh Kallonsa kawai take ganin yana abu cikin gaggawa ta ce "What are trying to do?" Ya ƙarasa inda take kamar zai magana sai kawai ya saka hannu ya sunkuceta ya buɗe ƙaton window ta zare idanu tana ƙanƙame shi jin kamar zata faɗa ta ce "Plx ka barni" Ya cillata ta window ɗin ya kama shi ma ya dira yana sakkowa ya kama hannunta ya riƙe gam cikin nasa a ransa yana jin gudawa da itan shi yafi kawai bai tsaya ɗaukan mota ta can ƙofar baya suka fita yana fita ya samu wata lafiyayyiyar mota parke tana jiran shi ya buɗewa Majeederh motar ganin tana neman juyawa ya ɗauketa cak ya sata cikin motar ya shiga motar ya rufe, Majeederh ta fara kokawa ya jawota da ƙarfi ya rungumeta a ƙirjinsa kamar zai kuka daidai kunnenta ya ce "sacrifice this for me plz" Joshua ya ce "Yanzu ina zaku?" A hankali ya ce "Saudiyya....
*#Good player*
Chapter 25 · 0% Book details