← Book details Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 90

Sashe 75

Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suna zuwa daidai ƙofar gidan Barrister Aliyu Sufyan Khalil ya ce "Stop the car" Ta juya da sauri ta kalle shi bai kalleta ba har zuwa lokacin gashinsa a zube yake a baya da gefen fuska ya fito, tana ƙoƙarin fitowa ya sakawa motar key ya nufi gate ɗin gidan Barrister Aliyu, ya ɗan tsaya, daidai nan kuma manyan motoci na ƴan sanda wanda Khalil yama IGP Latif Mahdi waya yana buƙata, kasancewar IGP yasan khalil ya kuma san ba zai iya cutar da kowa ba dole akwai dalilinsa na yin haka, ya sanya ya buga waya kai tsaye aka turo, Majeederh na cikin mota tana kallon ikon Allah tana addu'ar Allah ya sa ba wani abu Barrister yama Khalil ɗin ba, Khalil ya shiga gidan tare da knocking ba jimawa aka buɗe Aaliyyah ta yi wani fresh saboda cikin jikinta, ta zare idanunta ganin Khalil ta ce "Kspider, Yaya Khalil?" Ya ɗan fuske dole shi Yaya ne ta ce "Come in,ka shigo" Ya ɗan yi jim sai kuma ya shiga, banda wani irin ƙamshi babu abinda parlon yake komai gwanin sha'awa, ya nemi saman sabuwar kujerar dake parlon ya zauna, ta miƙe ta ce "Bari na kawo maka drinks" Ya ɗan murza yatsun yana ƙarewa parlon kallo ya taɓe baki speaking calmly ya ce "Ina...," Sai ya yi shiru ta ce "Yaa Aliyu?" Ya zuba mata idanu bai magana ba ta ce "Latifa?" Ya lumshe idanu ya buɗe ta ce "Tana bedroom ɗinta ta kulle, ai police ne suka zo kamata Yaa Aliyu ya hana tun daga nan ta shige bedroom ta kulle" Khalil ya miƙe yana zura hannu a aljihu ya zaro wani master key ya buɗe bedroom ɗin dake ta dawo down strairs da zama, yana buɗewa ya ce "come in" ba a ɗauki lokaci ba polices ɗin suka shigo, wasu manya guda uku amma mata. Latifa na ƙuryar gado taga an faɗo ciki hantar cikinta ya kaɗa ganin police ta fashe da kuka ta ce "Don darajar Allah da Annabi kuyi haƙuri ku yafe mini kuji tausayina don Allah..,” ɗaya daga ciki ta daki bakinta da ƙasan bindiga nan da nan jini ya fara zuba, suka damƙeta zuwa waje, Barrister Aliyu dake sakkowa ƙasa ya bi Khalil da kallo domin da farko bai gane shi ba, sai ya yi masa kama da actor's ɗin Nollywood, domin ko fuskarsa ba a gani sosai sai jajayen laɓɓansa. Latifa ta kalli Barrister Aliyu ta ce "Sweetheart don Allah don Annabi karka bari su tafi dani na shiga uku na lalace dame zan ji? Daman nasan hak'ƙin Majeederh ba zai barni ba, Khalil Oga sir kayi haƙuri saboda Allah Majeederh ta yafe mini itama" Khalil ya saka hannu ya tura sumar shi baya yana kallon Latifa ya ce "To bata yafe ba, idan ma haka ne ni mijin malama ban yafe ba" Ta dinga kuka tana turjewa tana kallon Zaki yaƙi kallonta ta juya ta kalli Aaliyyah ta ce "Aaliyyah ki taimaka mini idan na je gidan maza ni kaɗai kashe ni za su yi"
"Sanda kike zuwa wajen boka kina k'ulla sharri saboda kawai ki cutar da É—an adam, É—an adam É—in ma wanda ya yarda dake kin nemi taimako ne?" Aaliyyah tayi dariyar rainin hankali ta ce "Kinci uban É—an iska a rainin hankali, ai uban kuturu ya yi kaÉ—an balle na makaho, ita rayuwa daman juyin wainar tanda ce, kuma rawar Æ´an mata na gaba ya koma baya, duk wanda ya ce tukunyar wani ba zata tafasa ba, billahi tashi ko É—umi ba zatayi ba, ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta, maza gidan É—an kande na jira ko zaman can zai wanke miki zunubanki"
Latifa idanun na zubar da hawaye ta dubi Aaliyyah dasu ta ce "Aaliyyah ni kike faɗawa haka?" Aaliyyah ta saki dariya ta ce "Warr, ke awa karan kaɗa miya? Ina ruwana da girmanki? Ai Karen Bana Shi ke Maganin Zomon Bana, kin rufe idanunki kin cutar da rayuwar wacce take matsayin uwa mahaifiya , duniyata, kin raina wayonta saboda kina baƙin ciki da baiwar da Ubangiji ya yi mata, idanunki sun rufe kin manta Sara da sassaƙa ba sa hana gamji toho”. Lafita ta ce "Haba Aaliyyah sharrin shaiɗan ne na gane kuskurena ki bani dama na wanke laifukana, ni ban ɗauke ki kishiya ba, ki bawa Oga sir Yaya Khalil haƙuri muyi zaman amana ki yarda dani don Allah" Aaliyyah ta zare Idanu ta ce "Ina ganin Kura da Rana yaya zan yarda ta cije ni? Na shiga ban ɗauka ba, bata fidda ɓarawo, uhm wannan falsafar taki bata samu tunani mai kyau ba" Barrister Aliyu dai na tsaye, Khalil ya juya baya domin zai iya kaiwa Latifa duka shi kuma duk jikin da yake ɗauke da najasa da datti ba zai taɓa saka hannu akai ba, police ɗin suka ja Latifa har zuwa waje, Khalil ya juya zai fita Aaliyyah ta ce "Yaya Khalil Anti Jeederh fa? Ka zauna kaci abinci mana" Ya ɗan shafa kai clamly ya ce "No Thanks" Yana faɗin hakan ya juya saboda bashi da business da Aliyu, yana zuwa motar ƴan sandan na barin wajen kai tsaye kuma state C.i.d Khalil ya ce a shige da ita daga nan a shige da ita prison saboda yana da d'aurin gindi. Hankalin Majeederh ya tashi taso ko albarkacin baby khalil Latifa taci, ta dinga buga ƙofar Glass amma a rufe kafin a fitar da Latifa Khalil ya yi waya da gidan ƴan jarida na t.v dana redion Latifa tayi bayanin abubuwan data aikatawa Jee har yadda aka samu cikin da wanda ya yi shi, voice ɗin ya dinga zaga ko'ina dake live ne, abin ya yi trending cikin ƙank'anin lokaci, laifin Majeederh ya wanke a idanun jama'a da wanda suka aibatata da masu tsine mata, suka shiga neman yadda zasu ganta idanu rufe aka shiga tsinewa Latifa da mahaifinta Alhaji Bashir. Khalil na kallon yadda jee ke binsa da idanu bai kalleta ba taja motar bisa direction ɗin daya saita mata, babu inda kuma map ɗin ya tsayar dasu sai gaban wani haɗaɗɗan gidan mai masifar kyau da tsari ganin sunan Orphanage ta juya da sauri ta kalle shi, kafin tayi magana yara da yawa farare da baƙaƙe sun taho da gudu sun rungume Khalil, daga mai ɗane bayan shi sai mai riƙe hannunsa suna "We miss you Daddy" Majeederh taji idanunta ya cicciko da hawaye ashe ta wannan hanyar Ubangiji ke buɗawa Khalil ta rasa yadda a kullum arziƙin Khalil ƙara yawa yake ashe ga dalili, ta ɗan yi baya tana tuna sanda take kaisa orphanage ɗin shima when he was little, a hankali ta ce
"I love you gwarzona" Ya juya ya kalleta domin ya ji me ta ce hawayen daya gani a fuskarta ya sanya ya saki yaran, Alhassan tuni ya shige cikin yaran ya fara dambe dasu har an yaga masa riga, ya ƙarasa inda take a hankali ya buɗe bayan mota bata lura ba ta ji ta faɗa ya bi bayanta yana rufe ƙofar ya ɗan yi tafi driver yama motar key, Khalil ya yi ƙasa da glass suka haɗa idanu da Faɗimatu Majeederh ta dinga kallon yarinyar tana tuna sanda ta ganta a Vidcall ɗin Khalil, John ya ƙaraso yana yin ƙasa ya ce "Ranka ya daɗe" Khalil ya zubawa John Idanu ya ce "Nace maka me?" John ya jinjina kai ya ce "Kace yau tarihi zai maimaita kansa, zaka nunawa Malama Majeederh yadda kake sonta?" Khalil ya lumshe idanunsa speaking calmly ya ce "I love my wife John, kamar bata yadda ba amma zan tabbatar mata yau ɗinnan" Ya sake sauke numfashi yana buɗe zuciyarsa ya ƙara kallon John ya ce "Mun ɓata time, Sexy mama When will fasting begin?" Sexy Mama Majeederh ta maimaita a ranta tasan da ita yake, bata kalle shi ba ta ce "Today" Khalil ya ware idanunsa yana ɗan dukan kafaɗarta "Sexy mama!" Ta harare shi ya ɗage mata mata gira ya ce "But you didn't tell me" Tayi masa shiru ya saka hannu ya mintsineta a bombom da sauri ta ce "Ohh sorry!" Khalil ya juya ya kalli John ya ce "Kayi lists na komi ka turamin, ka bar su Alhassan wajen ka" Ya sauke glass yana riƙe numfashi da shafa ƙirji ya kalli Jee ya ce "Saboda na ɗan shafa ki?" Ta tura baki ta ce "Mintsinina kayi fa?" Ya damƙota yana ƙasa da murya ya ce "Bari mu ƙarasa yau za kiga asalin mijinki da yadda ake Mintsini"
[11/2, 20:11] Ummu: *MIJIN MALAMA*

*BOOK 2 PAGE 101*
Chapter 75 · 0% Book details