Sashe 51
Mijin Malama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta riƙe kanta ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Abuturab maganin Shaye-shaye? Me ya sa ka yi mini haka? Me ya sa zaka cutar dani ashe ba so na kake ba?" Gabaɗaya ɓari da kyarma jikinta yake ta miƙe tsaye duvet ɗin ya yi nasa wajen, tama mance cewa she has been naked, ba ko kyalle jikinta kuka take kamar ranta zai fita ta ce "Akwai Allah, ka cuce ni ka cutar da rayuwata ka sanya ni cikin Shaye-shaye ba tare dana sani ba, Allah ba zai barka ba, idan ka cutar da ƴar wani ka sani kana da zuri'a ba ƴar ka na kewa fata ba, kawai ka saka a ranka Ubangiji ba zai barka ba" His Excellency ya ce "Listen to me Jiddo, ban yi haka da nufin cutar dake ba, Depression has caught you unaware, You have been depressed at that time, ke da kan ki kin sani ba, kuma a dalilin tsinuwar da mahaifinki ya yi miki" Ya yi ƙasa da murya cike da rarrashi da tarin soyayya ya ce "Ina son ki, I still love you Jiddo ina saka ran zaki dawo gare ni In sha Allah, ko rabuwa ta dake destiny ne, ƙaddararmu ce wacce ban san dalili ba, na kasa jure halin da kike ciki shi ya sa na nema miki mafita kamar yadda ya faru dani a shekarun baya wanda har yanzu yake ɗawainiya dani, so I'm very sorry for that, ki bani dama na wanke laifina a idanunki Plz Jiddo ina son ki, kina so na kema na sani..." D sauri ta ce "Wlh bana son ka, ko a baya balle yanzu" Da ƙarfi ya ce "Liar, ke Malama ce kada ki nemi yin ƙarya wlh tallahi kina so na" Tayi saurin cillar da wayar tana sakin wani irin kuka, ganin har lokacin Khalil bai motsa ba, bai kuma ce mata ci kan ki ba, gently ya juya zuwa cikin bathroom tare da rufewa, not too long da shigar shi ta ji ƙarar fashewar wasu abubuwa da ƙarfi, Majeederh ta ƙanƙame jikinta da kyau ta ce "Ya Allah! Wai meke shirin faruwa, yaushe zan yi farin ciki ne?" Bata san fitowar shi ba, sai ji tayi ya sanya hannu ya ɗagota tsaye tare da juyo da ita gabansa, ta fahimci a yanayin da take na rashin suttura a jiki shi ma a haka yake, tayi saurin ɗauke kanta while hawaye na ƙara zuba daga cikin idanunta muryarta na rawa ta ce "am sorry, i knw nothing about it don..." Bai bari ta ƙarasa cewa abin da take son faɗa ba, ya yi saurin haɗe bakinsu waje guda tare da sunkutar ta zuwa cikin bathroom, all of them were naked yana shiga ya sakar musu ruwa a kasa sanyin ruwan ya sanya Jee sakin wata nauyayyiyar ajjiyar zuciya mai ƙarfi tana ƙara shigewa jikinsa, ta fahimta ba sbd yanayi na Soyayya yake kissing ɗin ta ba, ya yi hakan ne sbd ya yi controlling kansa, da kuma hukunta ta akan ɓoye masa da tayi tun farko, hannu ya sa ya ƙara gudun saukar ruwan, And he is still kissing her lips so madly har cizo yake sakar mata, ta runtse Idanunta hawaye na saukar mata, Tayi l nadamar ɓoye masa komai, she regretted knowing Abuturab in her life, she deserves any punishment that Khalil will give her. jin ya saketa tayi saurin rungume shi bakinta na rawa ta ce "I am sorry Khalil" Bai ce mata komai ba ya kalli gefen bakinta dake tsastsafo da jini a hankali ta sake ƙanƙame shi ta ce "I love you" Cak ya ɗauketa ya ɗora ta saman sink yana riƙe ƙafafuwanta da kyau.... [08/09, 9:07 pm] Sdy Auwal Gstc: *_Arewabooks@Nimcyluv_* _Follow my account_ https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv A rikice a cikin kuma tsakiyar daren sakaliyya gari ya yi shiru sai ƙarar kanaru da sauran tsuntsayen da suke makeken gidan na Dr Ibrahimul-khalil Abraham, ya ɗakko ta da hannunsa cikin hali na suma, yana jin ba zai iya yi mata komai ba, Despite the fact that he is a great gynecologist and psychiatrist amma kiɗimar da yake ciki na ganin Jee a halin da take da jinin dake zuba har yanzu yaƙi tsayawa, ga kiran da Uncle Isma'il ke masa babu ƙaƙƙautawa duk cikin tsakiyar daren ya sanya ba zai iya aiwatar da komai ba, ganin yadda Khalil ya taho da sauri ya sanya wani soja dake tsaye ƙyam! Kamar haka aka halicce shi ya yi saurin cewa "Oga do you need some help?" Ko inda yake Khalil bai kalla ba, ya shiga wata mota yana kiran driven sojan shi a gaggauce, ya zo da sauri lokacin tuni ya shige bayan motar yana ƙara rungume Jee gani yake kamar she will die and leave him, wannan ya ƙara bawa Khalil tsoro domin tabbas idan aka wayi gari babu Jee a duniya he most die, tunda shi ne ya zama silar mutuwar nata. Sai da suka ɗauki titi Driver ya ce "Oga ina muka nufa?" Khalil ya runtse idanuna ya ce "Aminu Kano teaching hospital" Ya faɗi hakan da ƙyar, hannunsa yana shafa sumar kanta, ganin kuma halin da Dr Ibrahimul-khalil yake ciki ya sanya driver take giyar motar yana wani irin azababben gudu kamar zasu bar garin, suna isa hospital ɗin Emergency suka amsheta Khalil da kansa ya rungume matarsa tare da ɗora ta gadon marasa lafiya aka nufi ciki da ita, gabaɗaya a birkice yake ya manta da yanayin shigar dake jikinsa, a hankali kuma ya ɗauki wayar Uncle Isma'il yana ɗagawa Uncle Isma'il ya yi magana, Khalil ya lumshe idanunsa muryarsa bata fita sosai ya ce "Ohk" Ta cikin wayar akai magana calmly Khalil ya ce "We are in the hospital, Uncle" yanayin yadda yake rausayar da kai ya sanya zaka fahimci Uncle ya ruɗe a taushashe Khalil ya ce "My wife is sick, she was admitted to the emergency room" Ya kuma cewa "Jee" Daga nan ya kashe wayar.... Washegari wajan 10 na safe a hankali yake tafiya cike da nutsuwa da kamalar dake kwance a jikinsa da kuma izzar daya ginu a kanta shekara da shekaru, sky blue ɗin shadda ce jikinsa wacce ya zauna masa ya ɗora hula jaddara sai ƙamshin turare yake bazawa, hannunsa zube cikin aljihu magana Jawaad ke masa amma baya fahimta slowly kawai yake jinjina masa kai, without even knowing what Jawaad say's, a harabar emergency ɗin suka tsaya Jawaad na ƙoƙarin kiran Uncle Isma'il yaga sun fito shi da Uncle Bello har suka ƙaraso bayan sun gaisa Jawaad ya ce "Uncle ya jikin Anti Jeederh?" Uncle Isma'il ya ce "Allhamd, wai jini za a saka mata" Jawaad ya jinjina kai, har sun kai wanda suke tare da Jawaad bai ce komai ba wayarsa yake dannawa a hankali, Uncle Bello ya juya zuwa gefe ya kalli Khalil dake zaune a saman kujera tun ɗazu ya kuma fi awa a wajan ya ce "Khalil kaje ka yi wanka kaci abinci, she'll be fine In sha Allah" Khalil ya kalli Uncle bai ce komai, domin ko kayan jikinsa da ƙyar yaje ya sauya ya dawo har yanzu kuma yaƙi faɗa musu komai da abinda ya sameta har tayi doguwar suma haka, baya fahimtar komai baya ganewa Uncle Isma'il ya ƙara cewa "Ibrahim ka je ka huta, kada wani abu ya sameka kai ma" Khalil ya sake ɗaga jajayen gajiyayyun idanunsa a taƙaice ya ce "My wife is sick, how can I get peace?" Sai a lokacin wanda ke tsaye tun shigowar shi emergency ɗin ya ɗaga kai ya kalli Khalil na wasu seconds yana ɗauke kansa gefe, Yaya Bilkisu ta ƙaraso hannunta riƙe da basket Jawaad ya nufeta da sauri yana amsa tare da gaisheta, su Uncle's suka gaidata ta nemi waje ta zauna ta ce "Wallahi tallahi a gigice na ƙaraso hospital ɗin nan, hankalina ya gama tashi jin Hawwa'u ba lafiya gashi babu wani driver a gidan ni na tuƙa kai na, ina tafe ina tunani saura kaɗan na bige wani yaro" Uncle Isma'il ya ce "Ayya ina da kin yi zamanki yaya" Ta ce "Ba zan iya ba Isma'ila" A hankali ta ji an ce "Morning Yaya" Ta ɗaga kai tana murmushi ta ce "Sannu General ya jikin naka?" A sanyaye cikin riƙe fuska Alpha ya ce "Good" Yaya Bilkisu ta ce "Ai naga har yanzu baka gama dawowa daidai ba, gashi dai wajan kwana uku fa kusan huɗu da dawowar ka, kai Ubangiji ka ƙara yi mana katangar ƙarfe da dukkan wani azzalumi Ubangiji ya bi maka hakƙinka" Shi dai bai ce komai ba, babu alamar ma zai ce, ta juya kan Khalil da yake ta yatsuna fuska alamar hirar ta dame shi ta ce "Mijin Malama zo ga tea mai zafi na san baka ci komai ba" Ya zuba mata idanu bai ce komai ba, Uncle Isma'il ya ce "Alpha zauna mana kafin Dr ya fito ku shiga wajan nata a gaisa" Yaya Bilkisu ta ce "Majeederh ta san ɗan uwan nata ya dawo kuwa?" Uncle Isma'il ya ce "Ranar dinner ɗin su da Khalil ya dawo cikin dare fa kamar korarre, cikin ikon Allah kuma a hankalinsa abinda ya sanya ban faɗa mata ba kinga ai babu dacewar ta fito daga shigarta ɗakin miji, to shi ne jiya da daddare na kasa jurewa na kira na faɗa mata sai nake jin suna asibiti a time ɗin" Yaya Bilkisu ta ce "Allah sarki, Allah kaɗai yasan murnar da za tayi" Ta ƙara juyawa ta kalli Khalil daya miƙe zai bar wajan ta ce "Ga shayin" A hankali ya girgiza kai, sai a lokacin Khalil ya lura da General dake tsaye cike da kamala kallon juna sukai ba tare da sanin kai ba, Khalil bai san Alpha ba shi ma kuma Alpha bai san Khalil ba, domin ko lokacin da yake yaro suna samun saɓani idan Alpha yana gari to Khalil na orphanage wajan Akeeth, General Alpha ya miƙawa Khalil hannu alamar musabaha yana cewa "hi" kamar zai share kuma ya zaro waya tare da ɗauke idanunsa yana cewa "Sannu" Yana faɗin hakan ya juya yana ɗaga kiran ganin sunan Ajlaal Sultaan a hankali ya ce "When?" ya yi shiru sai ya ce "Zan zo airport ɗin" Yana faɗin hakan ya kashe wayar daidai nan Dr ya fito