← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 57

Sashe 9

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin.mintuna ta isa gidan Anita saboda irin gudun da ta dinga fallawa tamkar ita kadai aka yiwa titin,ko murfin motar bata rufe ba ta yi cikin gidan cikin jan kafa tamkar zata kifa,a razane Anita ta sauke labulen dakinta lokacin da ta ga motar zahidan,kokarin saita kanta tayi tare da fitowa falon daidai lokacin da zahida ta fada saman kujerar tare da sakin wani irin nishi tamkar na me haihuwa saboda tsananin takaicin da yake ranta,a hankali Anita ta matso ta zauna kusa da ita tare da dafa kafadarta, kana cikin sanyin murya ta ce"zahida me kuma ya faru na ganki haka a dame?"zahida ta yiwa kanta alkawarin baza ta kuma yin Kuka akan damuwar aminatu ba, dan haka ta hadiye wanda taji ya tsaya mata a maƙoshi kafin cikin dakiya ta sanar da Anita abinda ya faru a cikin wannan safiyar,kafin ta dora da cewa "yanzu anita har nayi lalacewar da wata mace zata zo har gabana tana gaya min irin wannan magana,anita sirrin mijina ne fa wanda ni kadai ce mace daya tal a duniya da ya kamata a ce na san sashen jikin mijina ba wata tsinanniyar bafulatanar daji ba,me Mus ab yake so ya zama bayan nasan shi mutum ne me tsantsani da bin dokokin Allah,tabbas Anita akwai wani abu aboye kuma zan gano ko me ye saboda nasan mus ab farin sani shi ba manemin mata ba ne kuma bana jin zai fara akan wannan yarinyar" shuru tayi tana dan maida numfashi kana taci gaba da cewa "anita me kike tunani akan wannan lamarin?"a hankali Anita ta janye tagumin da ta zabga tana sauraron zahidar kana ta ce "zahida nifa ina tunani akan yarinyar nan ta san wani abu da kuke shiryawa akanta kamar yadda kika sanar dani akwai abinda su Abby suke shiryawa a kanta ko nace suke da dalilin daukota shi yasa take Miki wannan wasan kwaikwayon dan kawai ta juyar miki da tunani dan gaskiya Ni a gani na duk abinda take miki Shiri ne kawai"tunda Anita ta fara magana zahida ta zuba mata ido bata motsa ba har sai da ta kai aya,"anita maganar ki akwai kamshin gaskiya dan kuwa akwai alamomi da yawa da ta nuna mana wanda yasa muke zarginta da sanin wani abu daga cikin sirrinmu, dan haka zan yi bincike sosai akanta muddin kuwa na gane hakan to kashinta ya gama bushewa duk da cewa dama ba kyaleta zanyi ba",tana zuwa nan a zan canta ta mike tsaye ba tare da ta yiwa anita sallama ba ta fice daga falon.

Binta da kallo Anita ta yi, kallon da Ni kaina na diga masa ayar tambaya ,dan kuwa kallo ne wanda yake cike da ma anoni ma su tarin yawa,daga karshe kuma ta yi kwafa.

Aminatu da kanta ta gaji da zaman cikin wardrobe tasa khalid ya budeta, zama ta yi tana maida numfashi kafin ta mike ta fada bathroom ta yi wanka tana fitowa doguwar rigar atamfa ta saka ta fesa tirarukanta da sauran humrorin da humkum ta hada mata ta fita zuwa falon dan cikinta babu abinda yake sai kugin yunwa.

Tana cikin cin abincin Anne ta fito tana dan dingisa kafarta saboda danben da suka sha da bera jiya,aminatu na kallonta ta tuntsire da dariya kamar wata zararra,unbola kawai Anne ta iya yi mata tare da wucewa inda ta nufa,"su Anne an sha danbarwa wasan jiya yayi dadi saura na yau"ta fada tana mikewa daga kan dinning din,kai tsaye daki ta nufa da madarar ruwa a hannunta da Kuma wani dan kwano karami, tana zuwa ta leka karkashin gado ta janyo kwalin da ta boye yar magenta, zarota ta yi ta zuba mata madarar tasha ta koshi daga haka ta saketa a cikin dakin ta fice tare da rufo dakin,daidai lokacin zahida ta shigo falon fuskar nan har yanzu a suntume,da sauri aminatu ta ja baya tana rufe bakinta saboda dariya dake shirin kufce mata,Dan a hakikanin gaskiya wannan abu ba karamin muni yasawa fuskar zahida ba.ko kallonta zahida bata yi ba ta haye upstairs, a ranta tana jin tamkar ta dauki ran aminatu ta huta.

Aminatu kuwa ganin khalid yayi bacci yasa itama ta koma sama falon mus ab ta kwanta, ita sam ba ma bociyar yin baccin rana ba ce saboda gani take kamar a sara ce gara ta dauki kur'ani ta karanta ko tayi salatin annbi da sauran tasbihai,sai dai baccin yau ji take kamar an sata shi yasa tana kwanciya baccin ya dauketa.

Kamar a cikin bacci kamar ido bude haka take jiyo sautin matar da Kuma kallonta dishi dishi a cikin idanunta,sosai take jin muryar matar a cikin kunnenta kamar haka.

Aminatu me kike yi haka?wane irin shirme kike yi, da har yanzu baki fara binciken da zai taimaki Al umma da Kuma daukar fansa ba,haba aminatuwa ya kamata ki ajiye duk wani shirme ki tashi tsaye ki nemi hankali ta Karfi da yaji domin yin abinda ya kamata idan ba haka ba rayuwarki da ta Dan birninki har da ta kakarki duka suna cikin hadari,ban da sauran mutane da fansar rayuwarsu yake karkashin kulawarku, ki nemi dan birni, ki fara saninsa tun kafin su rigaki saninsa, sannan ki tabbatar da cewa kin nemi hanyar shiga dakin da yake bayan dakin Abby,da sauri aminatu ta ce,"wacece ke sannan kuma me zan yi a dakin idan na shiga kalan suce sata zan yi musu"murmushi matar da har yanzu bata ganin fuskarta tartar ta yi sannan,tace "idan kin shiga zaki ga abinda zaki yi kuma zaki samu haske akan babban aikin da yake gabanki"daga haka bat batar ta bace,farkawa aminatu ta yi jikinta duk jike da gumi, kalle kalle ta shiga yi ko zata ga matar dan ajikinta take ji tamkar ba mafarki ta yi ba a zahiri su kayi magana da matar,sai dai babu ita babu dalilinta, sosai aminatu taji zuciyarta ta karkata akan abinda matar take son ta yi da kuma tunanin baffanta da nasa sakon wanda take ganin tamkar duk sako daya ne suke bata, to wai ta ina zata fara neman dan birni ita da ba sanin sa ta yi ba kuma ba fita take yi ba bare ta gano shi?take zuciyarta ta bata amsa da cewa "to kin gwada ne bare ki samu ko kuma kina zaune zaizo ya same ki?.

Kamar wadda aka yiwa allura zunbur ta mike tsaye tare da duban agogo taga karfe uku har da arba in. dan haka sai kawai ta wuce dakinta na falon mus ab,wanda ya kaita tun tana yarinya,toilet ta fada ta yi wanka tare da dauro alwala ta zo ta yi sallah daga nan ta canja kaya wanda suke nuna alamun fita zata yi,har da yar bag dinta ta riko a hannu,duk da cewa ba tsayawa ta yi gaban mirro ta tsara kwalliya ba amma tayi masifar kyau babu abinda jikinta ke fitarwa sai sassayan kamshinta da tuni ya gama kama komai nata, ko guri ta zauna idan ta tashi kamshinta zaka ji yana yi.

Ba hill ta saka ba, Amma hakan bai hana ka jiyo karar sautin takalminta ba, zahida ce a hakimce a falon gabanta Dan karamin teburin cin abinci ne da kayan abinci akwaieda alama bata jima da gama cin lunch ba,sai hannunda da yake rike da waya ga kuma tv a kunne tana aiki, aminatu bata kulata ba dan tsoro take ji kar ta zauneta, dan haka sai ta wuce gun khalid, zama ta yi a gefansa kafin ta sunkuya daidai kunnensa ta yi masa rada,zai yi magana kenan kofar mai falon ta yi gefe alamun shigowa za a yi,tun kafin yayi sallama tirarensa da takunsa ya fallasa shi,gaba daya suka maida hankali kansa yana shigowa tankar wani saraki fuskar nan fes sai dai a tamke take babu fara a, da sauri khalid da aminatu suka hada ido kafin Kuma su hada hannuyensu ji kake raf karar sautin tafawa du kansu fuskarsu dauke da murmushi,khalid ne yayi saurin mikewa tare da rungume mus ab din daidai tsayinsa yana cewa "daddy na Dan halak barka da dawowa yanzu nake shirin sato wayar momyna na kiraka", da sauri zahida ta maida kallonta kan aminatu dan tabbas tasan abinda ta rada masa kenan,bata ce uffan TA maida kanta kan wayarta tana cu gaba da abinda take yi ba tare da ta dubi inda mus ab yake ba.

Aminatu kuwa dake tasan abinda take so yayi mata,karyar da kai tayi kana cikin muryarta yar karama wadda ke dauke da salonta na shawaba ta ce"daddy sannu da zuwa"khalid ne yayi saurin tararta da cewa adda aminatu ba haka ake welcome ba baki ga yadda nayi ba,kema kizo ki rungume daddy" cak zahida ta tsaya da abinda take yi tare da saurin kallon aminatu,bata gama tunanin aminatu zata aikata ko bazata aikata ba sai tsintar aminatun tayi a kirjin mus ab tana wani juyin shawagaba har da dan hawayenta tana cewa, "daddy sannu da zuwa dan Allah ka shirya ka kaimu shan icream kullum muna gida kamar wasu Anne da basu da kafa"khalid ma ya amshe da cewa "ey mana daddy da baka dawo bama kiranka zamu yi kazo ka kaimu yau dai mu bude ido rabonmu da fita da kai fa tun adda na ss1".

"Addar uwarka da ubanka shege dan iska asirtacce wallahi Khalid idan baka fita sabgar wannan me kama da Aljanar ba sai na saba maka ko kuma na dauke ka daga gidan naga da uban wa zata yi kiriniyar"
Chapter 9 · 0% Book details