← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 57

Sashe 23

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zahida na shiga dakin ta ta yi cilli da kome da yake hannunta kafin ta fara zarya a dakin, cikin sauri kuma ta nemo inda ta jefar da wayoyinta ta dauki daya tare da sanya kiran su Abby,sai dai kuma har yanzu babu wani kabari duka wayoyinsu a kashe suke,anya kuwa zata iya hakura har sai sun dawo akan maganar dan ladi,kai ita fa bata ki a wannan daren a fito mata da dan ladi ba,domin ji take tamkar shine mahaɗin rayuwarta tun da ya zama makullin warware al'amuran ta da mus ab,da kyar ta iya runtsawa shima din dan bacci ya kasance barawo ne.

****

A can kuma duniyar su Abby,suna can suna fafatawa da boka sunduki, tsananin iya tsafi da aiki da aljanu yasa sunduƙi bai yi kwanakin da ya ambata ba tuni har ya kammala aikin,sai dai kuma kash ya kasa ganin komai akan al'amarin bare har ya ga inda littafin yake ,aljanun da ya tura ma a kone suka dawo masa cikin azabar kuna ba tare da sun iya tunkarar inda aminatu take ba ma balle har su sa ta dauko littafin su kuma su samu damar kwacewa saboda su sun kasa ganin inda yake,haka ne yasa ran sunduƙi yayi matukar ɓaci wanda take kogon ya shiga girgiza tamkar wanda ake girgizar kasa ,dajin kuwa da kogon tuni ya dauki wani irin sauti mara dadin amo, dan acikin sautin babu kalar kukan jinnun da babu aciki,yayin da wani irin bakin hayaki me tsananin wari da yaji ya turnuke su Abby yana zagayesu da wani irin gudu,wanda hakan ya kuma tabbatar musu da cewa ba karamin fushi sunduki yayi ba domin wannan hayakin ba kowa ba ne sai shi, tsananin fushi da fusatar da yayi ne yasa yake jin tamkar ya cinye su Abby shi yasa yake musu wannan zagayen idan yayi niyar hadiyesu sai kuma ya fasa, gane hakan da su Abby su kayi ne yasa suka fara neman gafara tamkar wani ubanginsu.

Sun jima suna kasan da kansu ta hanyar wasu surutai da nuna girmamawa da tuba a garesa wanda hakan ya sanyaya sunduƙi har ya fara saukowa,a hankali komai ya dinga dawowa daidai, daga nan shima ya rikida ya dawo suffarsa ta tsohon sunduƙi, dukkansu kawunansu a duƙe suke babu wanda ya iya ɗago kansa ya kalli sunduƙi saboda tsananin biyayya,sai da shi da kansa ya basu umarnin kallonsa sannan suka ɗago gaba dayansu a tare suna masa kallo me cike da ladabi,bude baki yayi cikin amon muryarsa mara daɗi tamkar Juan jaki ya ce dasu "gobe zaku koma gida amma ba ta hanyar da kuka zo ba,zaku tafi a mota saboda duka iyalanku sun dawo gida kuma dukansu babu wadda zuciyarta take da kyakkyawan zato a kanku,dan haka ku yi tafiya irin ta mutane sai dai zamu gajarta tafiyar taku ta zama kun isa cikin sauri, abu na gaba shine Ni da aljanuna gaba ɗaya mun gagara dauko wannan littafin wannan shine abinda ya bata mana rai har muka kusa yin ajalinku anan,saboda a iya tsawon rayuwarmu babu wani abu da ya taba gagararmu sai a kan wannan yarinyar,dan haka idan kun yi naku muma ba zamu kyale ta ba domin irinsu ne suke kawo karshen mu a doron duniya,ku tashi kuje ku karbi littafi ta ko wacce hanya idan kunso zaku iya saceta ku boyeta ku yi gadinta saboda kar ta samu damar karanta littafin nan,ina mai kuma jaddada muku cewa kar ku bari ta karanta littafin nan idan hakan ta faru Ni babu sauran amfanina a wajenku da sauran mutanena ma baki daya dan haka wannan yaƙin banki kadai ya shafa ba muma ya shafe mu, dan dai abin ya gagaremu ne shi yasa muka barku domin ku din zaku iya dan naga wannan acijin bincike na shine ma ya bani kwarin gwiwar sanar daku,ku tashi ku tafi"daga haka wajen ya bace ɓat ya shafe gaba daya wajen ya koma fili fetal tamkar sahara.

*********

Tunda suka yi salla aminatu ta koma baccinta,dan ko sallar da jallabiyarsa ta yi ta, tana idarwa kuma ta zame ta ta koma ta kwanta ta ƙudundune cikin bargo saboda bazata iya barin jallabiyar a jikinta ba, dan ta yi mata yawa da tsaho sosai tamkar wadda za a naɗeta a ciki,nata kuma ta nemesu ta rasa da alama ya fita dasu daga dakin gaba daya,dole yasa ta kwanta ba tare da tasaka wani abu ba,shi kuma yana can dakin geaming,bashi ya fito ba sai wajen takwas, hannunsa rike da karamin towel yana goge fuskarsa ya shiga dakin,ganin har lokacin bata tashi ba yasa ya shige bathroom dan yin wanka.

A bangaren zahida kuwa ko da ta gama duk wani shirinta na fita dan neman su Abby bata yi niyyar shiga ko ina ba,dan har ta fara kokarin sauka sai kuma wata zuciyar ta bata shawarar zuwa duba mus ab ki dan ta ga wani irin kallo zai yi mata ,tunda boka ya ce zai yi aikin da zai rufe hanyar da mus ab zai iya gane wani abu akanta,kai tsaye ta shige falon ta nufi ɗakinsa da tasan anan yafi Zama ,ba tare da sallama ko knocked ba ta faɗa dakin kai tsaye,idanunta kuma basu tashi sauka akan kowa ba sai kan aminatu da take baccinta hankali kwance jikinta gaba ɗaya cikin bargo fuskarta ce kawai a waje ta yi fes da ita zara_zaran gashin idon sun yi luf kai kace na kanti ta saka,wani irin jiri zahida taji yana neman yarda.ita amma tuni ta yi karfin halin tsayawa akan kafafunta zuciyarta kuwa ta kasa dakatar da ita daga tsananin bugun da take yi,kafin ta shiga takawa har zuwa gaban gadon ta tsaya akan aminatu tana yi mata kallon kin mutu yarinya,cikin wani irin zafin nama ta sanya hannu ta warce bargon da aminatu ta ke ciki,lokavi daya taji nunfashunta na neman daukewa sabida yadda taga aminatu babu kome ajikinta daga ita sai dan fant,wata irin fincika ta kaiwa aminatu tare da yin wurgi da ita tamkar wata kaza,tuni aminatu ta farka tare da dafe goshinta da tuni ya fashe ya fara zubar da jini saboda gwara kanta da zahida ta yi a jikin katakon gadon,kuka ta saka me karfi wanda hakan ya fito da mus ab daga bathroom ba tare da ya gama tsane fuskarsa da towel din da yake hannunsa ba,cikin hanzari da rashin nutsuwar da ya fara bayyana a tare dashi ya janyo aminatu jikinsa tare da yi mata rumfa yana kareta daga kallon baƙin ciki da hassada da kuma tsana me ƙarfi da zahida take yi mata.

Wani irin zafi ne ya dinga tasowa daga maƙogaransa yana bayyana saman haibarsa da tuni ta rikiɗe ta koma wata kala,zahida kallonsa ta koma yi cikin tsananta al'amarin da yayi matukar muni a gareta ,wai yau mus ab ɗinta ne rungume da wata mace babu kaya a jikin ta, yau mus'ab ɗinta ne take kallon tsananin damuwa da tashin hankali akan an taba wata mace acikin idanunsa da saman fuskarsa,mus ab din da duk abinda za kayi ba zaka fahimci damuwarsa ko rashin nutsuwarsa ba,amma yau shine ya ke kokarin birkicewa akan ta fasawa kucaka ballagazar yar kauye talaka goshinta,wani rin miyau me kauri ta hadiye tare da kawar da fuskarta daga kansu saboda ganin mus ab din ya juya bayansa yana daurawa aminatu towel din da ya riƙosa a hannunsa.

Cikin kakkausar murya zahida ta kuma figo amiantu daga hannunsa tana cewa "zo ki fita daga dakin nan yar kunama tun kafin na kashe ki na kashe banza, raunanniyar ballagazar karuwa sheda iya ta karu......."ke"wata irin raunanniyar tsawa mus ab ya mata wadda hatta aminatu da take jikinsa sai da jikin ta ya hau kakkarwa yana ɓarin tsoro,"wallahi muddin kika kuma kiran aminatu da karuwa sai na miki abinda har a cikin kabarinki sai kin tuna dani"mus ab ni matarka kake kora akan wannan abun?musu ab ka dawo hankalinka mana kasan wannan din ita wacece kuwa?"hannunsa yasa yana tare jinin da yake zuba daga goshin aminatu kafin ya bata amsa da kalmar da ta kashe ta a tsaye cikin wani irin razani da tashin hankalin da bata taba tunanin akwai makamancinsa a duniya ba..

"Ni nan na fi kowa sanin wacece aminatu MATAR ƊAN BIRNI kuma nine namijin da ya kamata na kare hakkin ta da martabarta saboda ita din ta kasance ɓangare biyu matsayi biyu ruwa biyu a wajena,ita din AMANATA ce kuma MATATA""""""

Zahra✍🏽
[4/30, 3:05 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page44*``

Ba tare da ya kuma sauraren ta zahida ba ya dauki aminatu cak ya fice da ita daga dakin ya maida ta dayan dakin ya rufe kofar,zuciyarsa na jin ɗacin kallon tsiraicin Aminatu da zahida ta yi, tabbas ba dan ya kasance mutum me tsananin danne fushi ba to da tabbas yau yadda zahida ta bata masa rai zai iya karyata baras,

Da sauri zahida ta dafe ƙirjinta da take jinsa kamar zai fado, zuciyarta kuwa zafin da take bata ga da abinda zata iya misalta shi ba,gaba daya ta kasa sarrafa hankalinta ji take ma kamar ta zauce, dan haka sai kawai ta shiga wani irin ihu tana yi tana jifa da duk abinda ta ci karo dashi,gaba daya ta shiga hargitsa dakin tana yi tana kuka me haɗe da ihu,hatta da madubi sai da ta fasashi gaba daya ta fita hayyacinta banna take kawai tana jiwa kanta ciwo, da gudu Nana da Anne da larai suka hayo saman ,cikin tashin hankali suka fara kokarin dakatar da ita ta hanyar kokarin kamata, sai hakan ya gagara,hatta Anne da ba shiga sabgarta take ba yau ta tsorata da yanayin zahidar,gaba daya sun kasa dakatar da zahidar hakan yasa Nana ta shiga kokarin kiran mus ab dan a tunaninta ko ya fita ne,zahida kuwa har falo bata saurara masa duk abinda bai fashe ba sai dai idn ta kasa fasashi ne ko kuma ba na fashewar ba ne, hannunta ba abinda suke sai zubda jini kamar wadda aka yanka.
Chapter 23 · 0% Book details