← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 57

Sashe 4

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kasancewar zahida a gajiye take shi yasa bata damu da kulasu ba, kai tsaye hayewa ta yi bangarenta Anita na biye da ita da hand bang da sauran TARKACEnta tamkar dai wata hadimarta. kuma hakan baya damun Anita ko kuma nuna wa ne bata yi Allah masani, Anita na zaune a falon zahida har ta je ta yi wanka ta shirya ta fito, a ƙalla ta dauki sama da mintuna talatin amma hakan ko a ƙwalar rigar Anita,sai ma tararta da ta yi cikin fara a da nuna kulawa,tana zama larai ta shigo dauke da kayan abincin da ta gama haɗa musu bayan ta tabbatar da dawowar zahidan,tana ajiyewa ta fice ta bar su. Anita da kanta ta zubawa zahida abinci da lemo daidai yadda tasan tana bukata daga nan itama ta zuba,fara cinsu ke da wuya Anita ta ɗan dakata da kai lomar da take shirin yi bakinta tare da duban zahidar da take cakular abincin kadan kadan cike da yauki,kana ta ce"wai Ni ko Dr ya labarin majnunin kine har yanzu ba wani important issue with him?"uffan zahida bata ce ba sai da ta mula dan kanta kana ta ce,Anita me ye damuwarki da maganar dan ladi ne kullum baki da tambaya sai nashi?me kike so ki sani bayan na gaya miki cewa ban san ina yake ba ban san ya a kayi ba, hasalima rabona da shi tun wannan daren da aka raba Ni da shi dakyar",ta karasa maganar tana zuƙe ragowar lemon da ke cikin cup din hannunta,Anita ta ce,amma ai kin gaya min cewa ya zo da safe bayan kin fito asibiti har an yi masa dabara an kullesa an hada shi da hotonki?"da karfi zahida ta daki goshinta kafin cikin tsawa ta ce"Anita ya isheki bana bukatar wannan maganar ya daga dawowata baki tare Ni da komai ba sai da batun wani kazamin me wanki"anita ta kwantar da murya tare da cewa haba zahida ni fa kawarki ce kuma aminiyarki abokiyar shawararki ni ce me warware miki matsala duk lokacin da kika shiga damuwa amma akan abu daya sai ki manta ki rufe idanunki ki ta fadar abubuwa marasa dadi"duban ta zahida ta yi fuskar nan a kwabe babu annuri kana ta ce,"anita ba ko mai ne kike da hurumi dashi a cikin rayuwarta ba to dan me zaki dinga min wasu kalar tambayoyi wanda suke sirrina?"cike da mamaki anita take kallon zahida kafin ta buɗe baki ta ce,wai zahida kina nufin har yanzu baki gamsu dani a cikin rayuwarki ba?kina nufin tun tsawon lokacin da muka hadu har zuwa yau baki yadda kin ji cewa zaki iya faɗa min ko wane irin sirrinki ba?"girgiza kai zahida ta yi tana duban Anita ido cikin ido kafin ta ce"Anita har yaushe muka hadun da kike batun na saki jiki dake? Nifa in gaya Miki KO uwata bata isa jin sirrin rayuwata ba,mutum uku ne nayi musu yaddar da za su iya jin wani babi na cikin sirrina bayan su kuwa babu wani mahaluki a duniyar nan, dan haka tun wuri ki cire a ranki cewa dan kina kawata kawar ma da muka hadu a titi Zan iya baki amana ko sirrina, kuma ina gargadinki daga yau kar ki kuma yi min batu akan dan ladi, kar kuma ki kara yi min wata tambaya da ta danganci rayuwata idan ba haka ba zan cireki daga cikin rayuwar tawa gaba daya ba abinda ya dameni ba ne wannan"daga haka ta fice fuuu ta bar falon ta bar Anita da sakin baki tana binta da kallon mamaki.

Jiki a sanyaye Anita ta baro bangaren zahida duk da cewa bata ji a ranta zata iya rabuwa da zahidar ba amma dai ta ji ciwon abinda ta yi mata,lokacin da ta sauko tuni an yi Isha dan haka a can bakin gate ta samu aminatu ita da mudan wanda ya cika alkawari ya kawo mata kyliyarta a ɓoye ba tare da ya bari yan gidansu da securities din sun gani ba,Anita tana daga cikin motarta take kallon aminatu wadda sai yau din ne ta ke yi mata kallon tsaf, sosai taga rashin lefin zahida na yadda ta daga hankalinta akan AMINATU, wucewa ta yi bayan an bude mata wangamemeiyar kofar gate ɗin zuciyarta cike da sake sake akan lamarin GIDAN zahida.

Yau mus' ab bai samu dawowa da wuri ba saboda kansa ya fara daukar zafi ta ɓangarori da dama,sai karfe goma ya shigo gidan, ko da ya dawo ɗin ma kai tsaye upstairs ɗin bangarensa ya wuce bayan ya shirya kuma ya shige room dinsa na sirri da babu wanda ya san aikin da yake gabatarwa a ciki,yana shiga ya bude na urorinsa yana duba saƙonnin da suka shigo ta email address dinsa na sirri,sako guda da ya ja hankalinsa ya zubawa ido hannunsa tallafe da habarsa, sako ne da aka yi shi a sakaye tare da wasu kalmomin da aka sakaye su cikin HAUSA wanda hakan yaja shi tsawon lokaci dan son gano abinda hausar take nufi amma hakan ya faskara,ya tabbata wannan hausar a wajen cikakkaken bahaushema zata yi wahala bare kuma shi da hausar ba zauna masa ta yi ba, daga karshe dai haka ya hakura sai dai kuma ya kwafe kalaman a cikin kwakwalwarsa domin rubutasu ya ajiye zai iya zama wani abu da zai iya kawo masa matsala cikin aikinsa,fita yayi daga dakin ya koma bedroom ɗinsa, ya dauki karamar wayarsa ya kuma fitowa,kai tsaye dakin su aminatu ya nufa dan duba su.

Yau dake aminatu tasan abinda ta shirya sai da tasan yadda ta yi tasa Khalid yayi bacci da wuri, ita kuma ta yi lamfo kamar me bacci,tana jin lokacin da mus' ab din ya shigo,ya jima yana musu addu'a ya shafa sannan ya sumbaci Khalid,har ya juya zai fita sai kuma ya dawo da baya a hankali ya zauna gefan fuskarta ya zuba mata ido kafin ya fara matsowa da fuskarsa daf da tata,zuciyar aminatu kuwa har wani fat far take saboda tsoron abinda zai yi matan dan idan yayi mata irin na dazu to tabbas shirinta zai wargaje dan zai gane cewa bata yi bacci ba,dakyar ta yi yaƙi da zuciyarta da take kokarin tona mata asiri saboda dogon ajiyar zuciyar da taja na ganin ya sumbace ta kamar yadda yayiwa Khalid ya tashi tare da fucewa, yana fita ta saki numfashin da saura kirin ta sake shi tana dafe kirjinta.

Ga mamakinsa a dakinsa ya samu zahida, sai dai bai nuna mata ko mai ba kamar yadda itama bata ga komai akan sakarsa ba, kwanciya yayi bai ce mata komai ba, kamar yadda ita ma bata ce masa ba, sai da taga da gaske muskulancinsa ya take nata sannan ta tanka masa da maganar da kullum bata tauna ta kafin tayi masa,"kana kallona na dawo ba zaka tarbeni cikin kauna kayi min maraba ba?" Kai tsaye ya bata amsa da cewa sanda kika tsallake gidanki kika tafi in da ranki yake so kin nemi izini bare sallama?" Jin maganar da ya maida mata yasa ta yin shiru dan yau a bukace take dashi ba zata yadda ta biye masa ba dan taga shi idan zasu shekara a haka ba damuwarsa ba ce.

Zahra✍🏽
[4/13, 5:40 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page33``*

A can Abuja kuwa bangaren su Abby ke nan,bayan sun sauka a gidajensu, da matansu kamar yadda suka saba,barin su su kayi suka koma hotel inda anan ne zasu yi tattaunawarsu,wadda a wajen matansu tattaunawar kasuwanci ce, to suma a wajensu kasuwancinne .me lasisi ma kuwa,ba ko mai ne yasa suke zuwa da matansu lokaci loci ba sai dan kawai basa so ko kaka su bude kofar zargi tsakaninsu da matannasu shi yasa a ko da yaushe suke ƙoƙarin dai-daita kasuwancinsu da na kowa tare da shigo da matan nasu ta wata fuskar da babu wadda zata kawo zargin wani abu a Cikin harkokinsu.
Chapter 4 · 0% Book details