← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 57

Sashe 10

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tasowa ta yi ta janye aminatu daga jikin mus ab din tana cewa,"matsa dan ubanki na daji wallahi dole ki rabu da dana dan ba kaki lalata min yaro tun bai san komai ba,shi dai da ban Isa da shu ba yaje yayi amma indai ina da hakki sai Allah ya saka min"daga haka ta wuce sama da sauri tana kokarin maida kwallar kishin da yake neman kasheta,jikin aminatu ne yayi sanyi ganin yadda zahidan ta yi, duk da cewa babu wani abu da tayi dan ran zahidar ya baci Amma taji tausayinta,dakakkiyar muryarsa ta ji yana cewa "give me ten minutes" Khalid da bai damu da abinda uwarsa ta yi ba yasa ihun murna yana cewa ye yau zamu fita da daddy zamu ji dadin mu"anan ne itama aminatu ta saki jiki suka ci agab da murnar zasu fita,sai dai wani bangaren na zuciyar aminatu cike yake da tunanin maganganun matar mafarki da Kuma aiyukan da suka Sara da tunanin ta inda zata fara su,ta Ina zata fahimci abinda suke nufi?sai kin sawa zuciyarki nutsuwa kin ajiye shirme, zuciyarta ta bata amsa daidai da abinda matar mafarki ta fada mata,har mus AB ya sauko am in natu Tana nan cikin zurfin tunani Wanda hakan yayi matukar bashi mamaki sai dai Babu alamun hakan a fuskarsa, let's go"ya fada yana wucewa Khalid da shima tuni ya cake cikin gayunsa ya kamo hannunta yana cewa "zo mu tafi daddy ya fito"wanda hakan ne ya sa ta ankara da kamshinsa da ya hade da nata ya bada wani yanayi me dadi.

Har zata shiga baya Khalid ya janyo hannunta ya turata gaba,shi kuma ya shiga baya,duk yana kallonsu bai ce musu uffan ba,a hankali ya Kunna motar tare da yin ribas,tuni security ya bude wawakeken gate din su kawai yake jira su fita,a hankali mus ab ya cigaba da silala motar har suka fice daga gidan ya dauki hanya kan titin anguwar da kamar yau aka gama shi saboda kyansa da laushinsa.

Tsawon mintuna goma motar shuru sai daga can Khalid ya fara leka waje yana surutu da aminatu wadda ta kasa tanka masa,hannun mus ab da ya dauka akan nata ne yasa ta Dan waigawa inda yake ta kallesa sai taga hankalinsa na Kan hanya,idanunta ta maida kan hannunsa da ya sarke da nata kafin ta yi magana, ta ji saukar muryarsa a kunnenta cikin tsitstsinka kalamansa kamar me koyan magana,da wata damuwa ne?"girgiza kanta ta yi tare da kwantar da shi jikin makarin kujerar tana lumshe idanunta a natse,can kuma ta bude da sauri kamar wadda aka mintsina tare da zubawa hanya ido tana kallon duk mutumin da yazo wucewa a kafa ko a mota ko mashinan da suke wucewa wai ko Allah yasa ta ganesa ta kamshinsa ko takunsa,Dan karamin bakinta ta tura da tuna cewa kamshinsa iri daya ne da na MUS'AB. dan haka ko ta gansa in dai MUS'AB na kusa da ita bazata gane ba.

"Wa kike nema?"ya tambayeta tamkar bashi yayi maganar ba,tura baki ta kuma yi tana kara zura kanta ta window hadi da toshe hancinta dan wai ta daina jin kamshinsa da ya riga ya zauna a hancinta, Amma sai dai tamkar kara feso mata shi ake yi, dole ta koma ta zauna tana gunguni da kebe baki, a haka suka karaso wani hadadden wajen cin abinci.

Tunda suka fito aminatu take baza ido tana addu'a Allah yasa na hadu da Dan birni, bata sani ba har maganar ta fito fili, sai ji tayi mus AB ya ce"waye dan birni"dan murguda bakinta ta yi tana farfara idanunta kana ta ce,baka San ni MATAR ƊAN BIRNI ba ce hasali ma saboda shi muka zo BIRNI gashi Kuma har yanzu ban gansa ba, Amma daga yanzu zan fara nemansa ba zan dakata ba har sai na gansa",dauke kai yayi tare da kama hannun khalid ba tare da ya kuma tanka mata ba.

Zaman mintuna biyu su kayi aminatu ta fahimci kallon da wani saurayi ya cika ta da shi kamar zai cinyeta,a ranta Babu abinda take yi sai tsaki,sai Kuma ta yi wani tunani idan fa bata kula su ba zata gane Dan birni ba dan haka take ta fara tunanin hanyar da zata samu kusanci da wannan saurayin ta ji kamshin tirarensa kuma hakan ba zata yiwu ba dole sai mus ab baya gun,to yanzu ya zanyi?" Ta tambayi kanta,kafin ta samo amsa an yi Kiran mus ab a waya wanda hakan yasa shi fita daga wajen gaba daya dan da alama wayar tana da matukar muhimmanci..

Zahra✍🏽

500 only

Account number 8064537048

Fatima yusha'u Adam opay
[4/17, 7:33 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page36``*

Kamar jira wannan saurayin yake mus ab ya tashi,sai gashi ya mike ya tashi daga gunsa ya dawo wajen su aminatu,tun daga tafiyarsa aminatu ta tabbatar cewa ba dan birninta ba ne,dan haka take ta hade fuska ko da ya karaso ba tare da ya nemi izininta ba ya zauna, sai wani kokkobarewa yake kallo daya za kayi masa kasan cewa irin yan bana bakwai din nan ne makaryata masu kayan opay da wayar opay,ta kalminsa khalid ya kalla da hularsa ya ji kamar yayi dariya saboda su kansu bai iya sa su ba,yana zama ya fara karya murya cikin salon iyayi yana yi yana wani kashe ido,sai kace wanda ya warke daga makanta,abin ba karamin dariya ya bwa aminatu da khalid ba amma sai suka kanne dan take aminatu ta fara lissafin yadda zata yi maganinsa,"yan mata me kyau me za a kawo muku ne?"take amiantu ta gyara zama sannan ta karbi menu din da aka kawo musu ta fara tuk abubuwa masu yawa da tsada kamar wadda zata bude gidan abinci,ba tare saurayin yasan abinda aminatu tabyi ba ya wani saki murmushu tare da duban Khalid ya ce abokina kai ma ka fada abinda kake so ko nawa ne zan biya"caraf amiantu ta kuma karbar menu din ta dinga tik wasu abinci ma bata taba jun ko sunansu ba,sai da ta gama sannan ta ya fito waeter din ta yi masa rada a kunne, saurayi sai yashe baki yake khalid kuwa dariyarsa neman kasa rikuwa take dan tuni ya ga abinda aminatu take shiryawa saurayi dan karya,aminatu kuwa ta dake sai murmushi takewa saurayi shi kjma.yana ta zuba yana lissafa mata kadarorin mahaifinsa da filaye da gidajen da yake dasu da guraren da ya je a kasashen duniya, kai zance dai barkatai ba sama ba kasa.

Dake wajen babban guri ne dai wane da wane ne suke zuwa wajen shi yasa babu yawan mutane,kuma duk wanda suke wurin jikakku ne sun fi karfin a siya musu abinci , shi yasa aminatu ta radawa weter din ya rabawa almajiran da suke bakin wajen abincin da zai ishesu wannan saurayin zai biya.

Har lokacin mus ab yana waje yana waya.

Cikin kankanin lokaci aka cika gaban aminatu da kala kalan abinci da snacks da drink's,GA Kuma Wanda ake ta fita dashi ana rabawa almajiran dake harabar gun suna jira a fito da na zubarwa ko wani me tausayi ya zo ya basu sadaka ko abinci,tunda aka fara zubewa aminatu abinci a gabanta saurayin nan ya kame, tuni bakinsa ya mutu babu abinda yake sai zare ido cikinsa kuwa tuni ya shiga juyawa saboda tsananin tashin hankali, ba dai wannan abin duk shi zai biya ba?"aminatu da ta karance shi tsaf tuni ta yiwa weter inkiya, sai ko gashi ya taho hannunsa rike da lissafin kudaden da za a biya,yana zuwa ya mikawa saurayin da yake ta sharce gumi yana son tambayar aminatu fafa ta hanasa dan kar ya tambaya ba haka ba ne ta rainsa.

Kallon farar takardar da ake mika masa yake ba tare da ya sa hannu ta karba ba,har sai da weter din ya Kuma cewa yallabai GA list din duk abinda aka ci aka sha",karba yayi da suari yana dubawa hannunsa har rawa yake yi, cikin tashin hankali ya yi wurgi da takardar tamkar wanda ya kama kunama, kafin cikin rawar baki ya ce"ku mahaukatan Ina ne yaushe muka ci wannan kudin?"aminatu ta yi zakal ta ce"au sorry ai jin kace babu damuwa shi yasa nace ya rabawa almajiran dake waje suma suci ai ka samu lada"a gidan ubanwa nace miki ina son lada ?" Saurayin ya fada yana mikewa tsaye tare da cire hular kansa da tuni ta jike da gumi kamar wanda aka wanke da ruwa,tsugunawa yayi ya tattare kafar wandansa yana cewa wallahi baki isa ba sai dai ki biya su kudinsu amma ni ab zan biya ba,idan nayi niyar kyautar sanda zan yi sani kika yi,bana son shihsshigi dan haka ba zan biya ba kinga tafiyata",da sauri ami.atu ta ce kai ku rikesa ya biya ku kudinku babu ruw ana"aiko tuni securities din wajen suka cafke saurayi yana shirin artawa, ganin bashi da mafita yasa ya fara rokonsu, dan Allah ku rufa min asiri aradun Allah bani da ko sisi rigar jikina ba ta opay ce kai komai na jikina opay ne dan ku yi hakuri".
Chapter 10 · 0% Book details