Sashe 31
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata irin zufa ce take jika su ba tare da su kansu sun sani ba,zahida ce ta kuma yi masa tambaya cikin karfin hali,"waye boka ko shima fake dinne?"dariya dan ladi ya kuma sheƙewa da ita har yana buga ƙafarsa da kasan gurin kafin ya dan tsagaita ya dubi zahida yana cewa,"komai da kika sani ƙarya ne,kwallin bita zaizai duk karya ne ,kuma duk yana daga cikin shirin mu,tabbas da ace kun kasance irin ko wace mace da miji to da mus ab ya fahimci labarin tun lokacin da a kayi dramar kwallin bita zaizai"wani marin Abba Kabir ya kuma sheka masa har sai da yaga tartsatsin wuta,shi ko Abby har yanzu ya kasa motsawa saboda tsananin tashin hankali,to amma samun saukin su daya ne na jin cewa har yanzu mus ab bai gane komai akansu ba,dan haka dole su yi hanzarin samun littafin nan dan shine matakinsu na karshe na samun tabbacin ci gaba da rayuwarsu kamar baya....
Da sauri ya mike tare da yin Ball da Ahmad yana cewa,ku tashi mu tafi yaki zama bai ganmu ba,da fari dai bari na fara neman wayar isma saboda na bashi aikin bi min bayan mus'. Ab ɗin "gaba daya suka fita ba tare da sun damu da dare ba dan dama su namun dajin dawa ne basa fara farautarsu sai tsakiyar dare,sai da suka tabbatar sun bar dan ladi cikin tsaro sannan suka shig mota suka bar dajin.....
Zahra✍🏽
Kin san dai na kudi ne ko?
8064537048
Opay Fatima yusha'u Adam
[5/4, 7:22 PM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page48``*
......kai tsaye Anita gida ta koma ta fara adana takardun hannunta sannan ta kira mijinta ta sanar masa duk abinda ke faruwa,hankalin cp Musa ya tashi ainun, yanzu kina ina kuma ina Ahmad?"cikin jan ajiyar zuciya irinta wanda yasha kuka ya koshi ta ce ban sani ba tun da ya fito da kai kawai yayi waya bai kira Ni ba,bare nayi tracking nomber da ya kira"ya isa haka ki bari zanzo kawai sai musan abin yi"a'a kar kazo yanzu ka bari a kira sallah sai ka fito ka ji"shike nan karki damu amma ina dai kin san zamanki a gidan nan akwai damuwa kawai na zo na dauke ki yanzu"?a'a babu wata damuwa ai ba tasan ban mutu ba shi yasa yanzu hankalinta ba zai kawo kaina ba ko zuwa gida ba dan haka ka nutsu idan an yi sallar sai kazo mu tafi"ok ki kula sosai zainab kinji"in sha Allah babu abinda zai faru" ok by"suna yin sallama ta yi saurin rufe gidan tare da adana takardun daga nan ta fada bathroom dan tsaftace jikinta daga dattin wahala.
Washe gari kowa ya farka ne da abinda ya kwana dashi a ransa,su Abby gaba dayansu babu wanda yayi bacci ko da gyangyadi ne,ko wannensu kullawa yake yana kwancewa ,Abby ya dora hope dinsa akan isma gashi isma kuma.ya bace masa bat, Babu irin kiran wayarsa da bai yi ba amma a kashe,dole ya koma neman wata mafitar atunaninsa ko isma ya tafi sharholiyarsa ne.
Zahida kuwa itama tana daka tana saka da warwara ta rasa abin kamawa itama so take ta iya sarrafa harshenta akan mus ab ta kirasa ko zai fahimceta ya dawo inda take, wannan nisan da yake da ita shi yake sanya ta cikin kaduwa da tashin hankali, ta dauki waya dan jarraba kiransa ya kai sau dari amma ta kasa,kwarjininsa da haibarsa take ganowa wanda yake cika mata ido ta ji sam ba zata iya tunkararsa da wata magana ba.
Tunda amunatu taga mus'ab yana shiryawa ta fara rau rau da ido, duk inda ya bi binsa take da kallo, zuciyarta cike da tsoron kar ya ce zai fita ya kuma barinta ita kadai a gidan,har ya gama shiryawa tsaf bata daina kallonsa ba saima hawaye da ta fara saukarwa, gabanta ya karaso ya tsugunna tare da kama hannunta yana kallon cikin idonta da ya cika da hawaye,hannu yasa yana share mata su kafin cikin taushin murya ya ce " babu abinda zai faru in sha Allah,babu wanda yasan ina da gidan nan bare yazo shima biyo bayanmu yayi dan haka ki dena damuwa kinji,kuma yanzu nake kadai bace akwai masu gadi mutum uku da tun jiya na kirasu.gyada kanta ta yi tana kokarin maida kukan da yake son kwace mata,"kin koshi dai ko?ya fada yana shafa shafaffen cikinta da kamar ba a sa masa abinci,nan ma gyada kanta tayi,daga haka bai kuma magana ba ya miƙe ya fita daga dakin ya barta da shaƙar kamshinsa,tana jiyo sautin motarsa da fitarsa da kulle gidan har da Muryar mutane daga haka kuma bata kuma jin motsin kowa ba, a hankali ta miƙe kamar wata barauniya cikin sanɗa ta bude dakin ta fita, sai da ta yi dan diri_diri kafin ta gane dakin,zuciyarta na bugawa ta bude dakin tana fatan Allah yasa isma baya ciki, babu kowa a dakin hakan yasa cikin sauri ta fara duba inda ta ajiye littafin zuciyarta na aiyana mata cewa yau in sha Allah sai ta bude littafin nan taga abinda yake ciki,bata fatan wani abu ya kuma katseta kamar yadda yake faruwa duk sanda tazo budeshi,can karkashin gadon ta gano shi abinda ya so bata mamaki tunda Ita dai tasan a kan gadon ta barsa,bata zurfafawa kanta tunani ba ,ta yi saurin dauka ta fita daga dakin.
****
Gaba daya lissafinsu Abby ya gama kwancewa hakan yasa suka nemawa kansu mafita akan gwara su koma ga sunduƙi ya taimaka musu da neman inda aminatu take idan yaso su sai su karasa aikin karbar littafin, wannan tunanin da su kayi yasa suka hadu guri daya sannan suka yi siddabarunsu na zuwa wajen sunduƙi.
A maimakon haske sai duhu da ya mamaye dajin da kuma cikin kogon, duk da cewa safiya ce amma a wannan waje zaka yi tunanin sulusin dare ne,ko tafin hannunsu basa iya gani,haka suka yi gurfane a inda suka san sunduƙi yana wajen,babu motsin komai a wajen sai duhun da kuma kukan tsuntsayen da ke shawagi a cikin dajin,sun jima a durƙushe a wajen kafin su ji saukar Muryar sunduƙi me kama da kukan jaki yana cewa, na rantse da abin bauta idan har kuka ci gaba da yin sake a cikin wannan aikin har yaran nan suka ci galaba akanku to ba zan kyaleku ba domin Nima kunja min babban tashin hankalin da zai iya sanadiyyar raina,dan haka ku kalli nan"ya fada yana kunna wata wuta da take ci tamkar ana kona taya,ga tsananin mamakinsu aminatu ce zaune a saman gado ta kurawa bangon littafin, a zabure Abby ya yunkura tare da kai hannunsa zai kama wutar dan shi gaba daya ya sha afa gani yake kamar iminatunce a gabansa,bige hannunsa da daddyn zahida yayi ne ya ankarar dashi halin da yake ciki dan haka sai ya koma ya su sunkuyar da kansa wata irin zufa na shekowa tun daga saman kansa har zuwa kirjinsa da yake wani irin bugu fat fat,dariya sunduƙi ya sheƙe da ita kafin ya maida wutar ya kashe ɗif suka daina kallon aminatu,muryarsa ce ta kuma garwaye kogon yana cewa,ku yi sauri ku je gidan ku hanata karanta littafin nan duk da cewa zan yi nawa kokarin daga nan amma bana ganin cewa hakan ya wadatar, ku karba wannan ku dinga dannawa duk bayan sakon biyar shine zai kaiku har gidan da kuma dakin da take, cikin hanzari da rawar jiki Abby ya kai hannu zai karba amma sai sunduƙi ya ya hanashi yana cewa "baka da sa a a wannan karon dan haka ka bari yan uwanka su gwada tasu sa ar"dole Abby ya janye hannunsa Abba Kabir ya mika masa ya karba yar guntuwar layar,daga haka sunduƙi ya sallamesu, shi kuma ya shige baƙin Kogonsa dan fara nasa aikin.
***************
Anita tuni ta dankawa cp Musa duk wasu takardu da ta dauko a office ɗin zahida,daga nan ya dauketa suka bar gidan, kai tsaye lauyansu ya turawa da bayanan halin da ake ciki.
Mus ab na zaune a office yaji shigowar sakon imail ta wayarsa hakan yasa ya ajiye abinda yake ya shiga duba sakon, murmushinsa me tsada yayi kafin ya ajiye wayar yana mai jingina bayansa da kujerarsa, ya tabbatar da cewa ko yanzu yana shedar kama su zahida sai dai ba zai yi hakan ba har sai ya bude littafin wajen aminatu yaga meye a cikinsa domin yana tunanin akwai wani babban zunubin acikin wannan littafin,yana jin nauyin zuciya a duk lokacin da ya tuna waye mahaifinsa, ba zai iya irga casa casan da suke hannunsa ba wanda duk wanda aka bashi idan ya duba sai yana kaso mafi yawa akan asibitinsu ne,ya jima yana cikin zargi da taraddadi,sai bayan karbar case din su Anita ne ya kuma tabbatar masa da abinda yake zargi da kuma abinda ya faru da innawuro,a baya baisan Anita da ɗan ladi sune ya karba case dinsu ba,har sai da Anita ta kawo labarin yarinya me suna aminatu da take cikin rayuwar zahida ita kuma take.son ganin bayanta saboda ta fuskanci akwai wata alaƙa me girma tsakaninta da mijinta,ba kome ne yasa ya kawo musu shirin boka batun boka ba sai ɗan yana so ya tabbatar da su dinne,sai kuma hakan ta tabbata,aka samu akasi kuma ɗan ladi ya shiga hannunsu, alokacin dan ladi yana tare da camarar da yake amfani da ita a cikin gidan,to yanzu kuma gashi ya kuma samun tabbaci ta hanyar decomment din da Anita ta dauko, numfashi yayi tare da mikewa tsaye zuciyarsa cike da son ganin ya aminatu take,key ya dauka ya fice daga office din cikin hanzarin da zuciyarsa kesa shi yi.