← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 57

Sashe 3

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sai da ta yi sabon wanka ta canja doguwar rigar atamfa wadda aka yi mata dinkin Captain ta yi daram a jikinta dirarriyar kiranta ta fita tamkar ita ta zana kanta,fuskarta babu komai sai kwalli da ta zizara da lips glow sai ta yi wani irin sassanyan kyau tamkar ka sace ta ka gudu,saukowa ta yi daga saman dai-dai lokacin Nana ta fito daga dakin Anne cikin shirin fita da alama ma sallama ta je ta yiwa annen,cikin murmushi take duban aminatu da burgewa ta ce,"kai masha Allah ɗiyata tafi ta kowa kyau da burgewa, dama yanzu zan leƙo ku dan tafiya ta kamamu nida Abby dazu ya Kira ni yake sanar dani cewa na shirya kafin ya shigo",ta na rufe bakinta suka ji tsayuwar motar Abby,dan haka aminatu ta yi raurau da ido kana ta ce,yanzu nana bari na zaki yi a tsakiyar maza kalan a shigo a yi min fyade",salati nana tasa kafin ta dora da cewa yanzu aminatu ba zaki dinga yiwa bakinki linzami ba, ina cewa ban jima da yi miki fada ba amma har kin kuma",hawaye aminatu ta fara yi daidai shigowar Abby falon kallonsu yayi sannan ya shige yana cewa "sai ki sauri ki gama rarrashinta kafin na fito dan wannan tafiyar ba ta ku ba ce dole ku zauna a gida,zahida ma tana nan tafe yau din nan".

Zama Nana ta yi tana kwalawa Khalid kira, sai gashi ya sauko yana murza ido da a alama bacci ne ya fara kamashi,Nana me kika yiwa adda aminatu take kuka?"Khalid ya tambayi Nana lokacin da yake kallon fuskar aminatu da ta yi jage jage da hawaye kamar wadda aka yiwa duka,kama hannunsa Nana ta yi tana cewa wai dan na yi mata faɗa kuma nace zamu yi tafiya da Abby ba jimawa za mu yi ba, ina ga bai fi mu yi kwana uku ba"hakan da Khalid ya ji sai shima ya kwaɓe fuska zai yi kuka, zaunar da su Nana ta yi tana faman lallashinsu kamar wasu ƙananun yara ko nace kamar wata karamar yarinya,babu jimawa Abby ya fito lokacin tuni sun hakura dan dama ita aminatu kukanta bai kai zuci ba dan dama tana jiran irin wannan ranar ne da babu wanda zai dakatar da ita daga bawa Anne da isma kashi a gidan,har wajen mota suka rakasu, basu shigo gidan ba sai da suka ga fitar su daga gidan.

Suna shigowa aminatu ta dubi Khalid ta ce,zaka raka Ni gidan su rahila amma duk abinda ka gani kayi shiru babu ruwan ka da tambaya ka ji ko?"amsawa yayi da to mayafinta ta dauko ta yafa suka fice ba tare da sun sanar da anne ba.

Gida ne irin na masu karamin karfi, mace daya ce da yaransu kusan shida ga shi gidan bashi da yalwa shi yasa ko ina zaka samu kaya a jibge,kuma irin wannan gida beraye da sauran kwaruka sun fi takura musu,shi yasa kai tsaye aminatu ta zo nan dan neman bera,mannira ce ta ce "ke ko Amina me zaki yi da bera?"haɗe fuska aminatu ta yi kafin ta ce babu ruwanki idan zaki samo min kawai ki samo min", shike nan kamar nawa kike so?"anzo gun aminatu ta fada tana gyara zamanta akan kujerar tsugunnon da take ,kana ta ce "kamar guda biyu ma sun isa",tom shike nan bari nasa mudan yanzu ya kama miki su dan ba ya.tsoronsu kuma gasu nan ko ina yawo suke baza su yi wuyar kamuwa ba,sai dai kuma ina zaki saka su tunda kince a raye kike sonsu?"mannira ta tambayi aminatu tana mai lekawa dakin su mudan din dan kiransa,tunanin inda za a saka mata su ta shiga sai kuma ga mudan din ya fito yana cewa,"in dai zaki dawo min da dan karamin kejina da na hada zan saka tantabara sai na ara miki",da sauri aminatu ta amsa da cewa zata dawo masa dashi, dan haka kai tsaye mudan ya dauki kejinsa ya shiga dakin tsohuwa inda anan ne beraye suka fi yawa ya kamowa aminatu beraye guda biyu ya saka cikin kejin, cike da farin ciki aminatu ta karba suka bar gidan, jin ranta take yi yau fes ko ba komai zata yi kallon rawar tsoffi.

Har za su fita daga gidan aminatu ta ji kukan mage, cikin sauri ta juya sai ko idanunta suka sauka kan wata karamar mage baka idanunta ne kawai suke sheki, bata yi magana ba suka fita mudan yana rike da kejin da ya saka mata berayen, sai da ta ga Khalid yayi gaba yana yin ball da ball dinsa dake hannunsa, sannan ta kalli mudan cikin yin kasa da murya ta ce"mudan magen da na gani a gidanku ta ku ce?"gyada kai mudan yayi tare da cewa ai saboda berayen ake Yaya ya samo mana ita amma kuma gashi bata iya kama beran wata kila sai nan gaba idan ta girma"kuma yin kasa da murya aminatu ta yi Sannan ta ce"za ka bani ita?"shuru mudan ya danyi kafin ya kalli aminatun yana cewa "to ai ba tawa ba ce"kar ka damu ko siya ne sai na yi amma kar ka fadawa kowa ni ka bawa ka barsu kawai a zuwan ta bace kaji"mudan ya ce "to shi kenan,yaushe za a kawo miki ita?"dan daga kanta ta yi sama alamun tunani kafin ta ce "yauwa ka bari sai anjima da dare, amma fa kar ka bari securities din bakin gate su ganta idan kazo kawai ka ce musu sako zaka bani, da ka fada musu haka za su kyaleka ba za suyi maka bincike ba"dai-dai lokacin suka ƙaraso bakin gate ɗin gidan, karbar kejin da ya ke a lulluɓe aminatu ta yi tana cewa to mudan sai anjima da an yi sallar isha ka kawo min sakon kaji"mudan ya amsa da to daga nan ta shige gidan ba tare da ta kula securities din da suke sankame kamar wasu gumaka ba.

A falo ta samu Khalid da tuni ya rigata shiga gidan,bata kulasa ba shima ta wuce dakinta ta dauro alwala sannan ta kwalawa Khalid din kira shima yayi alwala suka yi sallar Azhar daga nan suka wuce dinning room suka ci abinci, aminatu tuni ta yiwa berayenta maboya lokaci kawai take jira ta kaddamar da shirinta.

Ƙarfe biyar daidai Anita ta je filin jirgi ta dauko Zahida,babu abinda Anita take sai zuzuga kyawun da zahidan ta yi wanda kuma a zahirin gaskiya babu abinda ta kara sai uwar ƙibar da take neman hanata nutsatstsan numfashi,sai dai fatar ta da ta yi kyau wanda dama kowa ya san wannan dole ne ga duk mutumin da ya samu zaman waje ɗaya musamman kasashen turawa,har suka zo gidan zahidan bata tanka mata ba, hasali ma idanunta a rufe suke kamar wadda take bacci,sai da ta tsayar da motar sannan ta dubi zahidan tana cewa to "Ms mus' ab zaki iya bude idanunki domin mun zo gida"sai a lokacin zahida ta bude idanunta tare da dago kanta daga kwanciyar da ta yi jikin kujerar me zaman banzar, a hankali ta tura ƙafafunta waje sai da ta dauki sakonni kafin ta fita gaba daya, kallon gidan ta yi kamar tana tunanin abinda zata shiga tarar a gidan,anita ce ta nuna mata hanya sannan ta fara yin takunta as usual kamar wata sarauniya tana yi tana faman buda hanci da yatsina fuska,a haka suka shiga main falon in da anan aminatu da Khalid suke ta wasan guje gujensu kana kallonsu kasan basu da wata damuwar da ta zauna a ransu.
Chapter 3 · 0% Book details