← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 57

Sashe 50

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan dalilin yasa anne ta zama wata iri dan ma akwai larai tana taimaka mata wajen kwantar mata da hankali amma da abin yayi mata yawa,kamar yau din da suke cika kwana uku da fara shiga wannan tashin hankalin, Anne na zaune a falon ita da larai saboda yanzu gaba daya sun daina zaman daki, dan muddin suka matsa daga Falon Abby ko zahida zasu iya ficewa daga gidan,su fita waje har ragowar securities din bakin gate su san halin da ubayen gidansu suke ciki,shi yasa basa matsawa daga falon, suna zaune cikin jimami suka jiyo karar fashe fashe hashen glasses da sauran abubuwa na karau ga kuma karar zahida a waje daya tana yi tana surutai da magiyawa kananun yaran da suke mata kuka acikin kai,da gudu suka haura saman, kai tsaye bangaren zahifar suka nufa inda tun daga kira suka fara cin karo da abubuwan da ta farfasa kama daga kan showglas tauraruka da dai duk wani abu me amfani ko da ba mai fasuwa ba ne,turus su kayi daga bakin kofar a tsorace suna kallon zahidar da hannayenta da duk ta ji musu ciwo,tana kallon anne ta nufi ta da gudu ta riketa tana wani irin gunjin kuka,kama ta larai da anne su kayi cikin tsananin tausayawa anne ta ce "me yake damunku ne zahida me yake faruwa da ku ku hudun nan? tabbas akwai wani abu da ku ne kaɗai kuka sani, shin haukacewa kuka yi ko kuma cikin hankalinku kuke yin duk abinda kuke dan wannan abinnaku ya fi kama da masu hauka sabbin shiga?"girgiza kai kawai zahida take kafin dakyar bakinta ya samu ya buɗe,cikin haki da rawar murya ta ce"Anne da ace zan yi hauka na fita daga hayyacina na daina jin Abinda nake ji na daina ganin abinda nake gani da na fi kowa farin ciki domin nasan sassauci ne Allah ya kawo min, amma wannan halin da nake ciki ba hauka ba ne tsananin masifa ce ji nake komai ma zan iya yi in dai zai sa na daina jin abinda nake ji, wallahi anne baki dacen ɗa ba, tabbas ba dan rashin iyaye na gari da nayi ba da wata ƙila halin da nake ciki bai kai haka ba,duk abinda nake aikatawa ban taba nadama ba ban taba dana sani ba ban kuma taba tunanin wannan rana zata iya zuwa min ba, sannan ban taba tunanin mutuwa a cikin rayuwata ba,anne ina cikin masifa da bala inda ba zasu iya faduwa ba, ya zan yi ku gaya min ya zanyi?"ta karasa fada tana mai ƙanƙame anne da kuma sakin wani irin kuka me ƙarfi.

******

Suna karasowa estate din aminatu ta yi saurin fita, bata jira kowa ba ta isa har dakin Nana,cikin farinciki Nana ta daga kanta tana kallon aminatu da take rahowa gareta da gudu,bude mata hannunta ta yi ta shige ciki, tana cewa my love I miss you "cikin dariya Nana ta amsa mata da cewa "me too yar gidan Nana,dagowa ta yi daga kafadar nana tana cewa ina innawuro?mikewa su kayi a tare Nana na bata amsa da cewa "tana kichin wallahi wai yau biski da miyar kubewa zata yi mana shi yasa tun dazu suka shige kichin ita da kaka sabuwar me aikinmu nima yanzu nake kokarin bin bayansu"aminatu ta ce "ai gara da baki bisu ba da yanzu kina kauri, amma dai Nana ya kamata a dauko Anne da larai daga wancan gidan ko?"nima abinda yake raina kenan dan barin nasu zai iya zama haɗari"Nana ta fada tana kama hannun aminatu,binta aminatu ta yi tana cewa,"babu wani hadari dan wanda zasu sasu a hadarin suma gudun ceton ransu suke yi"dan duban aminatun Nana ta yi, daidai suna karasowa falon, bude baki Nana ta yi dan tambayar aminatu dalilinta na fadar hakan, amma sai bakin ya tsaya a tsaka tsaki, ma ana shi ba a bude ba kuma shi ba a rufe ba,idanunta kuwa tsaye kyam akan Abba sule,tsawon minti ɗaya kuma sai ta juyo ta kalli aminatu kafin ta kumamjiyawa ta bi taguwar da suke zaune a falo da kallo,da karfi ta kuma damke hannun aminatu da yake cikin nata,kara aminatu ta saka tana cewa "wayyo daddy Nana zata karya maka hannun shalelenka duk dan taga nata masoyin"da karfi Nana ta kuma rike hannun Aminatun tana cewa "nima razananin zaku yi saboda baku da kirki to zan karya hannun gaba daya idan ya so a kulle ni ko ya rama miki"kuka aminatu tasa tana tsalle da son kwace hannunta daga cikin na Nana tana cewa wallahi nana da gaske ba fatalwa abba yake miki ba shine da gaske bai mutu ba ki tafi kawai ki rungume abinki ki yi kukan farinciki idan yaso daga baya sai ya fada mana yadda a kayi ya tsira daga mutuwa a wancan lokacin"sakin hannun aminatu Nana ta yi tare da fara takawa a hankali tana isa gabansa ta sanya hannu ta taɓa shi sai taga yayi dariya hawaye na zuba daga kurmin idanunsa,take Nana ta durkushe a gabansa tare da sakin wani irin kukan farinciki dan kuwa a yanzu ta gama tabbatarwa da shi din ne,hannu yasa ya dagota, wanda hakan yasa gaba daya suka watse daga falon.

Aminatu na shirin fadawa kichin inda su innawuro suke mus ab yayi sautin kama hannunta ya hanyeta zuwa lokon corridon da zai maida kai kichin zuwa falon,dan ware idanunta tayi dan bata yi tsammanin ya biyota ba,"kai n.....bata kara ba ya hade bakinsu ya shiga aika mata sakonninsa da suke dauke da wutar zalama, ji yake kamar kamar akan aminatun,yar yarinya me barkwanci da shiga rai ta sanya shi farin ciki ta sanya iyayensa,ko yadda ta yiwa Nana abun ya kayatar dashi, dan tabbas da bata yi mata haka ba da zata iya shiga cikin tsananin shock din da zai iya haifar mata da wata cuta, a hankali ya kai bakinsa kunnenta kana cikin muryarsa da ta bayyana mata faruncikinsa ya ce"ke ta musamman musamman din musamman ce,kin cika yar gidan kara yar gidan baffa Yusuf, Allah yasa na ajiye me kama dake anan"ya fada yana shafa cikinta, runtsue ido aminatu tayi saboda yanayin da ta tsinci kanta a ciki, muryarsa ta kuma ji ta daki kumennta ta wuce ta daki zuciyarta kai tsaye ta kuma.yi balancing cikin jini da gangar jikinta,da ƙwaƙwalwarta"ina sonki matata ina kaunar ki ina miki sonso, kauna kololuwar kauna,kin zama mahadina farincikina,ki yi hakuri dani cikin ko wane yanayi ki kasance tare dani cikin ko wane hali ba zan iya rayuwa babu ke ba,dan Allah aminatu ki soni ko da kwatankwatan son da nake miki ne alfarma Please"ya fada cikin jan kalmar, sannan ya dauke numfashi yana mamakin daga inda wadannan maganganun suka fito dan bai ma yi zaton shine ysl3 fadar su ba,har sai da yaji aminatu ta sanya fatar labbanta akan kirjinsa tare da bashi wata zazzafar sumba sannan ta ce,"daddy ina sonka fiye da kaina da rayuwata, bani da kowa bani da wanda zan so sai kai shi yasa ka zama kololuwa kuma makura a nan"ta fada tare da dora hannunsa akan kirjinta,bakinta ya sumbata da goshinta da hancinta har zuwa idanunta kana ya kalleta tare da dage mata gira daya sannan ya furta "na gode"juyawa ta yi tana murmushi, da saurin ta juyo da kallon ta kansa tana dan rufe ido alamun jin kunya, shima kallon inda ta kalla yayi kana ya ɗan saki wani miskilin murmushi me sanyi da burgewa abinka da basabanba,rada masa ta yi a kunnensa "mu gudu daga gidan nan tun kafin Abba da Nana su yi abinda zasu hanamu hada ido da su"kunnenta yaja ba tare da ya ce komai ba,wucewa su kayi wajen innawuro ,inda suka samu su anita har sun kwashe komai sun fada mata, kuka innawuro ta ke yi lokacin da su amintu suka shigowa dan haka sai kawai ta hada su ita da mus ab ta rungume tana sa musu albarka tare da yiwa iyayen aminatu addu'ar neman gafara da samun aljanna.

Anan dai suka baje suka ci biskin innawuro ga kuma girkin aminatu da suka taho dashi, kowa ka kalla fuskarsa wasai,aminatu kuwa sai zuba shagwaba take tsakaninsu,tana sakin bakinta cikin yarinta da tabara,wani ayi dariya wani kuma a yi shiru saboda kunyar barambaramar da ta yi.

*******

Zaunar da zahida anne ta yi sannan suma suka zauna fuskokinsu dauke da tausayi,Anne ta ce "me kuka aikata me girma irin haka da har zunubinsa ya kai yasa sanya ku cikin wannan halin?"girgiza kai zahida ta yi tana cewa Anne ba zan iya fada anan ba, dole sai dai naje gidan jaridu da talabijin nasanar da su abinda muka aikata ko da hakan zai zama izna ga masu irin halinmu,da masu tasowa domin su guji aikata mummunan hali irin namu"larai ta ce"zahida abinda kika gani fa kadanne ko na ce so min tabi ne akan azabar lahira, wannan a duniya ne domin Allah ya nuna misali akanku da kuma tsoratarwa ga masu mummunan hali ko wane iri ne,nasan dai ba zai wuce akan dabi arki ta wulakanta dan adam ba wanda kuma dama can kuskure babba kike aikatawa domin kuwa ko wane mutum da kika gani akwai irin darajar da yake da ita wadda ke baki da ita, Allah subhanahu wata a ala yana cewa wa lakad karramna bani adama......kinga Ubangiji da kansa ya karrama dan Adam bare kuma mu yan adam ɗin,shi mulki ko kudi da kike gani ba wai zaba Ubangiji yayi ya bawa masu su ba, sannan talaka ba wai dan Ubangiji baya sonsu ya barsu cikin talauci ba,kowa ya bashi ne dan jarraraba karfin imaninsa,arziki da talauci duka abu daya ne domin Ubangiji yayi su ne dan jarrabawa,game arziki ya gwadasa ne yaga shin zai yi amfani da arzikin ta hanya me kyau kamar taimako sadaka zakka tausayawaq da dai sauransu,shi kuwa talaka ya jarabasa da talauci ne dan ganin imaninsa akan juriya, ma ana shin zai iya hakuri da babunsa , sannan bai biyewa zuciya akan jefa rayuwarsa cikin neman haram ba, wannan kadan ne daga cikin ikon Ubangiji akan bawansa,amma wasu daga cikin masu kuɗi sai su dinga ganin kamar su din na daban ne a wajen Ubangiji,to zahida ki sani cewa babu wanda yafi wani wajen Ubangiji face me tsoron Allah da gudun saba masa".
Chapter 50 · 0% Book details