← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 57

Sashe 28

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da karfi ta fizge hannunta jikinta na karkarwa fuskarta kuwa tuni ta dame da ruwan hawaye,"me ya kawo ka nan me ka zo yi?"dariya yayi irin ta rainin wayon nan, sannan ya kuma kai hannu zai taba ta ,tayi saurin ja da baya tana girgiza kanta zuciyarta sai bugawa take da ƙarfi,kuma matsawa yayi gabanta tare da cewa "ko me zaki yi sai na yi abinda ya kawo ni ke ko da mutuwa kika yi wallahi sai nayi dagawarki kinji karewar zance dan haka ki gyara min nayi cikin salama tun kafin wancan mijin ƙaryar taki ya dawo"hannunta ta haɗe biyu tana nuna alamun roko dan bakinta ya mutu idan ta bude ta yi magana ma zata iya yin aman zuciyarta,jin jina kai yayi fuskarsa dauke da murmushin mugunta ya tunkarota gadan gadan tare da kai hannunsa zai cafkota,ita kuwa runtse idanunta ta yi tare da makurewa guri daya jira kawai ta ke ta ji me faruwa ta faru,amma a maimakon haka sai karar wani abu taji kamar ta karyewar katako ko itace har sau uku,ƙas ƙas ƙassss,sai kuma ihun isma me haɗe da karaji wanda yake fitowa tun daga kasan zuciya yake nuna tsananin azabar da mutum yake ji, da sauri ta bude idanunta guda daya kafin cikin wani irin yunkuri me karfi ta yunkura ta yi kan mus ab da yake rike da hannun isma har yanzu bai sakeshi ba,isma kuwa fitsari ya sake a wando saboda tsananin azaba kafin ya sume daga tsayen, sai a sannan mus ab ya sake hannun nasa suka tafi kasa tare da hannun da tuni ya rabe gida biyu fata ce kawai ta basu damar yin reto ba tare da sun rabu da juna ba.

AMINATU kuwa tunda ta rungumesa ta baya ta kasa motsawa kukan ma yau ya gagagreta yi,a hankali ya juyo da ita gabansa yana kallon fuskarta da idanunta da suka yi wani haske da girma saboda tashin hankali,wani irin tausayinta ne ya tsarga masa tare da wani abu me girma kuma na musamman da yake ji akanta tun lokaci me tsayin da ba zai iya tantance shi ba, ta ngumeta yayi sosai a jikinsa yana kuma shigar da ita tamkar zai maida ta ciki,cikin kukan da ta samu damar yinsa ta dago fsukarta tare da cewa"daddy ya zan yi nan ma sun biyo NI?dan Allah ka nesanta Ni da Garin nan bana son zama a cikinsa na tsanesu bana sonsu"ta karasa fada tana mainda kanta ƙirjinsa, bai ce komai ba sai wayarsa da ya dauka ya danna jim kadan ya ajiye,daga nan ya dauketa cak suka bar dakin,a tunaninta fita zasu yi daga gidan amma sai taga ashe daki ya canja mata.

Sosai ta saka masa rigima akan ita fa ba zata kuma zama a garin ba bare kuma gidan gaba daya,duk.ya birkice ya rasa ta inda zai fara rarrashinta ga kukanta da yake matukar sosa masa zuciya ji yake tamkar ana kartar naman zuciyarsa,cikin mutuwar jiki da azabar da yake ji na damuwarta da kuma azabar kishin isma da yake ji tamkar zai masa illa,ya kuma janyota jikinsa da take ta zamewa tana kukan ita ya barta ta tafi inda duk zata ba zata zauna a garin ba,riketa yayi sosai yana kokarin ce mata wani abu ko zata sauraresa amma ina ,sai ma duka da ta shiga kai masa tana CEWA "Ni ka rabu dani tunda kaima baka sona so kake su kasheni shi yasa ka bari wancan kwartan ya biyo NI zai ci min mutunci, dan haka wallahi ba zan zauna......da wani irin zafi zafi ya haɗe bakinsa da nata ya shiga aika mata da wani irin hot kisses, wanda tun da yake bai taba yiwa wata mace shi ba,hatta da ita aminatun bai taba kwatanta mata makamancinsa ba,sai dai yau din komai ya zama na musamman,domin da dukkan zuciya da ruhi yake yinsa,,tun aminatu na turesa har dai abin ya fi karfin tunaninta ,dan haka ta fara yin laƙwas wanda hakan ya kuma juya ƙwaƙwalwar mus ab ya shiga nuna mata kala kalan zafafan salo na musamman da aka tanadesu dan abincin zuciya,a hankali ya shiga zame rigar da ta yi masa shinge daga duk wani abu da ya zama halalinsa,a wannan karon aminatu kasa hanasahi ta yi saboda bata da wannan zarrar,damshin miyansa da sanyin harshensa ta fara ji tun daga kasan tafin kafarta yana tahowa har zuwa saman cikinta inda yayi birki akan dan ramin cibinta,wani irin yunƙuri aminatu ta yi tare da riƙe kansa tana fitar da wani irin numfashi me zafi wanda har tsatstsayawa yake tamkar wadda ake shirin zarewa rai,yadda yake tsotse ramin cibinta kai kace alewar madara ya samu,gaba daya mua ab ya kwance tamjar ba wannan miskilin mara fara a da kamewa ba, dan hatta da numfashinsa sai da ya sauya salon fita,kiran sallahr magriba da aka kwalla a cikin wayarsa ne ya yi masa burki,kuma.ahi kadai ne ya dawo dashi hankalinsa,sama yayi da.kansa tare da kifawa kan kirjinta yana maida numfashinsa.

A can kuma dayan dakin tuni mutanen da yayiwa waya suka shigo suka janye isma suka tafi dashi inda ya basu umarni.

******

Anita tana rungume da takardunta tamkar rayuwa, tana yi kuma.tana duba bayanta tare da leƙawa waje,idan ta leka sai ta kuma bawa me nafef din damar kara gudu,a haka har suka zo wani raod da babu yawan mutane sai jefi jefi saboda kamar hanyar barun gari ce,su dai basu ankara ba sai ganin mota suka yi ta yo kansu gadan gadan,duk yadda me nafef din yaso kaucewa motar abin ya gagara take motar ta tunkudasu cikin ramin da yake gefen titin,kara Anita tasaka tana ambatan innalillahi wanda daga karshe nafef din ya kai karshen ramin tare da kamawa da wuta tamkar wadda aka kunna,

Zahida da take tsaye bakin ramin tana kallon wutar da take ci daga jikin nafef din ta yi wani irin murmushin mugunta duk da cewa har yanzu bata cikin kwanciyar hankali dan kowa zata kashe idan har ba aminatu ta kashe ba, to tabbas bazata taba yin farin ciki ba,juyawa ta yi ta koma cikin motar tare da barin gurin da mugun gudu, tana jin cewa ta dan rage aiki amma babban aiki na gaba.

Kai tsaye gidan da su Abby suke ta nufa tana zuwa ta tarar suna fama da ɗan ladi akan ya gaya musu meye alaƙarsa da mus ab,dakatar da su ta yi tana zama dirshen a gaban ɗan ladi har da tankwashe kafafunta, sannan ta dago habarsa da yatsanta manuniya tana masa wani irin kallon kaskanci,kafin cikin Marmara idanunta ta ce masa"kai waye?"shima kallonta yayi kadan kafin ya kawar da kansa daga gare ta yana cewa,da alama kin fi iyayenki kaifin ƙwaƙwalwa dan tun tuni wannan tambayar ya kamata su fara yi min kafin ko wacce tambaya ta biyo ba"hannu abby ya kai zai shaƙeshi zahida ta yi saurin dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu, sannan ta ci gaba da cewa "ina jinka bani amsar tambayata"murmushi dan ladi ya yi tare da cewa tabbas ke ce jika biyo ta hanyar da zan baki abinda suka kasa sawa na basu sabida kin fisu dabarun aiki irin na jami an da suka samu kyakkyawan horo,su kuma aiki suke yi irin na jahilai kuma yan alfarmar jami'ai,dan haka kunci jarajarta yanzu zan baku amsa da iya abinda na sani,amma da fari ku fara gaya min inda yayata Anita take?".

Kallon juna su kayi mamakinsu da kaɗuwarsu na kuma nunkuwa,zahida ce ta ce "ka bani amsa kawai saboda yayarka ta kufce min a halin yanzu ban san inda take ba,amma fa hakan ba yana nufin ba zan nemeta dan ta karɓi hukuncinta ba ne"murmushi ahmad yayi tare da fadin "Allah duk inda yayata take ka kareta ka zama gatanta ka shiga tsakaninta da azzalumai,daga haka ya fara da cewa....Ni sunana Ahmad wanda kuka fi sani da ɗan ladi amma ɗan ladi ba shine ainihin sunana ba, Ahmad shine sunana da yanka,dan lardi kuma sunan da aka sauya min ne yayin shigowa cikin rayuwarku....
Chapter 28 · 0% Book details