← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 57

Sashe 30

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukkansu sun bada hankalinsu wajen ji da sauraron Ahmad dan ladi,shi kuwa sai da ya ɗan ja numfashi sannan ya ci gaba da cewa,mu mun kasace yan cikin garin Basrah ne wani kauye dake cikin yankin jahar gombe. mahaifin mu da mahaifin mu da mahaufiyarmu duka basu da kowa sai mu yaransu guda uku ,yayata zainab wadda kuka sani da Anita sai kuma Ni Ahmad sai kaninmu me suna haidar,mun taso cikin kulawa da tarbiyya gami da kwanciyar hankali,dan rayuwarmu muke yi simple babu zafafawa duk da cewa mahaifin mu babu lefi yana da rufin asiri na gonaki manya guda biyu da yake matukar ji dasu saboda gadon mahaifinsa ne,kuma da su yake amfanuwa ta bangaren noma da fidda hatsin da zai siyar kuma muci, so dayawa mutane suna kawowa gonayennan hari ta hanyar yi masa tayi da manyan kudade masu yawa amma duk da haka mahaifin mu yaƙi rabuwa da ko guda daya daga cikinsu,a haka muka ci gaba da rayuwa muna karatu dai dai wadatar mahaifin mu,kuma hankalinmu a kwance babu me wata damuwa a cikinmu,kwatsam muna tsaka da gudanar da rayuwar mu cikin kwanciyar hankali ba tare da wata mummunan ƙaddara ta ratsa mana ba,sai wasu mutane su uku suka shigo cikinta da wata fuska da bamu taba zaton zata juye ta zama abin tsana da ƙyama a wajen mu ba, da fari sun zo ne daniyar bawa manoma tallafi,wanda mahaifinmu shine jagoran tafiyar,sun bada tallafin musamman ga masu karamin ƙarfi,hakan yasa duk kauyenmu da kewansa babu abinda ake magana sai maganar karamcinsu, su kuma da wannan damar su kayi amfani suka ci gaba da zuwa suna yaudarar mutanenmu a hankali a hankali suka dinga karbe gonakin mutane da sunan za a yi musu birji tare da fadada ta dan kawar da annobar fari da suka fara cin ye mana gona,

Ana cikin haka ne layi yazo kan maiahina inda ya nuna sam bai yarda da batun su ba,duka ta dabara da aikata sun yi masa amma basu samu kan mahaifina ba,da suka ga taurin kansa yayi yawa sai kawai suka fito masa a mutum suka nuna masa asalin fuskokinsu na azzaluman da suke tara dukiya ta hanyar kwace da mallakar abinda ba nasu ba ta karfi, anan fa suka shiga fafatawa da mahainmu inda daga karshe suka dauke mahaufiyarmu sannan suka yi masa barazana da rayuwarta akan indai bai sa hannu a takardun gonakin nan ba zasu kasheta daga ita har yayansa,duk da cewa alokacin ba mu da wani wayo sosai ma.hakan bai hanamu fahimtar tsananin tashin hankali da damuwar da mahaifinmu ya shiga ba,daga karshe dole yana ji yana gani yasa musu hannu a duka takardun ya basu amma memakin su sakar mana innarmu sai kawai ganin gawarta muka yi a kofar gidan mu inda a take shima mahaifinmu ya fadi kasa a sume,tun daga nan ne kuma bai kara yin lafiya ba ciwon zuciya me karfi ya kamashi daga nan shima yace ga garinku nan,sai ya zama daga ji sai yayata da kanina haidar dan shekara uku a duniya,tsananin tashin hankalin da muka shiga ba zai fadu ba, gashi ba mu da kowa bare mu koma wajen yan uwa,dan haka sai kawai muka rungume rayuwarmu a haka muka ci gaba da gurgurawa, mun sha wahala matukar wahala mun sha gwagwarmaya ga yunwa ga talauci ga kuma rashin ilmi dan gaba dayanmu karatun mu ya tsaya cak saboda rashin kuɗi to cikinmu ma dakyar muke samu mu bashi,a haka har muka ja shekaru biyar da rashin iyayenmu zuciyarsu kuwa kullum ya fasa take wutar daukar fansa na ruruwa a cikinta,a haka ne Allah ya kawo wani bawan Allah me suna Musa cikin rayuwarmu da sunan yana son aunty zee, da farko bata yarda ba sai kuma da ma baya ta amince saboda yadda ya nuna kulawarsa a kanmu ya nuna mana kauna da daukar alkawarin zai inganta rayuwarmu tamkar ta ya'yan da ya haifa a cikinsa,a lokacin aunty zee ba wani kaiwa budurwa tayi can ba dan bata wuce shekara sha huɗu ba a lokacin amma haka ta amince wa Musa su kayi aure duk saboda mu,sai daga baya da muka dawo cikin birnin Gombe ne muka fuskanci cewa su din babban dan sanda ne wanda muna tare ya dinga samun karin girma har ya kai matakin cp,a inda ya samarwa anty zee gurbi na yin karatun jami'ar sirri kamar yadda ta bukata Ni kuma na ci gaba da karatu inda na ke karantar low,shi kuma haidar aka saka shi a primary 2,mun ji dadin zama da uncle Musa sosai dan mutum ne da yasan hakkin dan Adam,shi yasa muke matukar sonsa da girmamashi.

Rana ta biyu da ba zamu manta ba,mun tashi da rashin lafiyar haidar,.inda duka hankalinmu ya tashi muka dauke shi sai asibitin gjk,inda likitoci suka karbe shi cikin gaggawa aka shiga dashi dakin da ake duba marasa lafiya,fuskar ki tana daga cikin wadanda suka tarbemu duk da cewa baki da fara a da son mutane amma kin tsaya kin kula da haidar har ya fara samun samun sauki kuma shirin sallamarmu ne, haidar ya kuma birkicewa da wani irin ciwon ciki, a nan ma kin tsaya tsayin daga gurin kulawa dashi inda daga karshe kika tabbatar mana da cewa haidar yana bukatar koda saboda kodarsa duka biyun sun samu matsala idan har muna son rayuwarsa sai dai mu siya ko mu nemo wanda zai bada koda a saka masa,hankalinmu ya tashi inda anan ne uncle Musa ya bada shawarar a nema kawai a saka masa saboda dukanmu yara ne bai kamata ace an tabawa wani koda ba,da farko ban amince ba sai daga baya ya fahimtar dani abinda yake nufi sannan na amince"

Ɗan shuru ɗan ladi yayi yana jan numfashinsa zuwa cikinsa inda ya ci gaba da cewa,ranar da aka shiga da haidar tiyata a ranar ne na shiga office ɗin zahida Dan amsa kiran da ta sa ayi min bana nan sai bayan nazo ne zainab take gaya min shi yasa na tafi ba tare da na yi tunanin bata office din ba ko kuma ta shiga wani aikin,ina zuwa da hotunan mutum uku nan na ci karo wanda sam ban taba kula dasu ba,sai ranar cikin firgici na juya zan fita dan ba zan taba manta fuskokinsu ba,duk da cewa ina yaro ne abin ya faru,na juya kenan zan fita sai naji alamun motsi a bathroom din office din hakan yasa na dan karasa bakin kofar tare da kai kunnena dan jin abinda ake fada,sai kawai naji Muryar zahida tana cewa kar ka damu daddy tuni mun yi yadda muka saba yanzu haka har mun cire lafiyayyun mun dasa matacciyar fito dashi kawai ya rage a yi"cak na nemi numfashi na na rasa take kaina ya fara juyawa, jin kamar za a fito yasa Ni saurin fita daga office din, kafin na cewa aunty na komai an fito da haidar a sankame a kamun babu rai"zubewa kawai nayi na kasa cewa komai na kasa kuka na kasa hawaye sai zuciyarsa da take wani irin tafasa, ban tsaya na saurari kukan da zainab take yi mijinta na rarrashinta ba na sunkuci gawar nayi waje da ita,da gudu suka biyo ni suna kirana amma babu wanda na saurara, dole sai hakura suka yi suka biyoni gidan inda a nan muka yi masa wanka muka kaisa makwancinsa,to tun daga nan ne nasha alwashin daukar fansa daga karshe na sanar da zainab da mijinta abinda na sani da kuma abinda nake zargi,mun jima muna neman lauyan da zai tsaya mana amma hakan ya gagara daga kasrje dai muka samu wani bawan Allah,bamu taba ganinsa ba sai dai ya yi mana magana ta email address dinsa shine ya tsara mana hanyiyin da zamu bi don nemo shaidar da zai iya kwatar mana yanci, baku taba ganinsa ba kuma bamu taba jin muryarsa ba amma baya bamu gudunmawa me tarin yawa ya dora mu akan hanyar kaiwa ga gaci duk abinda zamu yi ko mu kayi shine yake tsara mana ta hanyar sakonsa da shi kadai muke gani yake nuna mana alamar cewa yana tare damu"

Cikin mamaki zahida ta fesar da iska daga bakinta tare da cewa,"me yasa ban gane Anita ba lokacin da ta waɗo rayuwata da niyar yaudara?"dariya Ahmad yayi tare da cewa,ai ba zakintaba ganeta ba sabida girmankanki da jin cewa ke isashshiya ce yasa baki tsayawa kiwa talaka kallo daya ma bare a kai ga batun ganewa,duk sanda zaku hadu da Anita bakya duban fuskarta haka Nima bakya kallona,na sani ikon Allah kadai yasa ko kallon rainin da kikewa talaka mu baki tsaya kin yi mana shi ba kinga kuwa baki taba kallonmu ba,kuma wannan ne ya bamu damar shigowa rayuwarku ba tare da kun gane mu din su waye ba,yau har gashi rayuwarku ta fara tangal tangal"ya fada yana tuntsurewa da dariya!mari daddy ya sharara masa kafin cikin tsawa ya ce"dan ubanka ka fada mana waye mus ab me Kuma ya sani game damu?"dan ladi ya ɗago kansa tare da watsawa daddy wani banzan kallo kana ya ce"ku matsiyata masu ci da gumin wasu wanda komai nasu ya kasance haramun wallahi kunyi karya a wannan lokaci baku isa ba karshenku yazo, kuma karamar ƙwaƙwalwarku bata gano muku waye mus ab ba a cikin labarin da na baku,tunda bata gano muku ba to bari nayi muku Gwari wari yadda zaku fi fahimta,wato MUS'AB dan Alhaji jamilu shine lauyan da muke tare dashu ba tare da mun sani ba,kuma shima bai san mu su waye ba saboda bai taɓa ganin daya daga cikinmu ba, sannan bai san wane gida ya turo mu ba,kar ku damu har yanzu danka bai gane komai a cikin wannan wasan ba amma fa ku fara gudu dan hakan na gab da faruwa wallahi dukkanninku sai kashinku ya bushe".
Chapter 30 · 0% Book details