← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 57

Sashe 41

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lallashin da da daddy yayiwa zahida yayi tasiri dan har gashi ta shirya fita office,duk da cewa zuriyarta tana ta yi mata raye raye akan shiga asibitin saboda tun baya kafin wannan abubuwan su fara faruwa da su ta fahimci cewa ABM hospital ya riga da yayi shuran da ta tarar dasu zai yi wuya,wani lokacin har mamakin karbuwar asibitin take saboda ko su lokacin da suka yi shura basu yi sauran da ABM yayi ba, take zuciyarta ta raya mata wani abu akan asibitin,tabbas akwai wani kasuwanci makamancin nasu da asibitin take yi, sai dai ga dukkan alamu sun fi su iya taku dan basu taba jin ance an mutu bisa ganganci a cikin asibitin ba,dole ta nemi me asibitin nan ko mace ko namiji dole ne suna bukatar temakon irin wannan mutanen a cikin tafiyarsu ta bangaren asibiti, anan ta yadda cewa muddin tana son daga darajar asibitinsu to dole sai ta kama hannun director na ABM hospital,da wannan tunanin ta gama shirinta ta bar gidan.

Tunanin zahida da Abbas dinta yazo daya dan lokacin da ta isa asibiti waya ta yi da Abby tana neman shawararsa akan tunanin da ta yi, sosai ya bata goyon baya kuma yaji dadin wannan mafitar da ta samo musu yasan muddin suka yi nasara akan su mus ab asibitinsu zata tsira har su samu damar ci gaba da harkallarsu cikin kwanciyar hankali kamar baya.suna gama waya da abby zahida ta fara binciken ABM hospital da mamallakin asibitin, a yau dai bata samu wani impomation ba amma tasan idan tasa naci zata da ce.

Lokacin da su ɗanturque suka fahimci cewa dan ladi ya gudu ba karamin tashin hankali suka shiga ba ,dan sun san lefinsu ne,hakan yasa suka nadama nemansa ba tare da sun sanar da iyayen gidansu ba,dan sun kudiri niyar ba zasu bari su sani ba tunda suna da kwarin gwiwar samo dan ladi a duk inda yake.

******

Hankalin dan ladi ya tashi lokacin da me nafef ya saukesa a gidan cp ya samu ba sa nan sai saƙo da me gadi ya bashi,karɓa yayi ya duba sai yaga adireshi ne na inda zai samesu,ajiyar zuciya ya ɗan sauke, kafin cikin sauri ya haye nafef ɗin yana cewa"dan Allah ka kaini tasha"lokacin da yaje tasha babu motar da ta cika dole sai zama yayi yana jiran su gama lodi,daga ƙarshe dai dole sai safiya suka tashi,har a lokacin ɗan ladi hankalinsa bai kwanta ba,sun ɗau hanyar barin gari ke nan sai ga wata bak'ar mota tasha gabansu,sosai ɗan ladi ya firgita dan ganin wanda suka fito daga motar, babu hanyar da zai ɓuya hakan yasa ya miƙa kansa dan kar yajawa na cikin motar,tunda ya fito daga motar suka tasa ƙeyarsa har cikin motar su suka ja bai ƙara sanin inda kansa yake ba,lokacin da ya farka mamaki ne ya kamashi ganin wasu sabbin fuska daban sannan su danturqui a ɗaure ta mau da alama dai sun shiga sabon hannu ne daga shi har su,to waɗan nan su waye haka?"bashi da mai bashi amsa,dan haka ya gum da bakinsa,bai iya cewa komai ba saboda kwarjinin mutanen yafi gaban a kallesu,bayan girmansu hatta da fuskarsu babu sukunin annuri bare har ya iya yi musu tambayar da take kewaye a cikin kansa,hakan yasa ya maida kansa ƙasa tare da dan motsa hannunsa da yake tunanin a daure yake kamar yadda nasu ɗanturqui yake a daure,amma ga mamakinsa sai yaji hannunsa a sake,sai kawai ya gyara zamansa ya jingina kansa yana ci gaba da kallon su,abinci yaga ɗaya daga cikinsu ya garo masa a cikin robar take away,bai yi ƙasa a gwiwa ba ya ja gabansa ya buɗe dan yunwa yake ji sosai,abinci ne me rai da motsi ga danƙwaleliyar kaza a kai ga kuma ruwa da lemo, ɗaga kansa yayi ya kalli mutanen, sannan ya mayar kan abincin tare da yin Bismillah ya fara ci.

****

Tunda suka yi salla suka koma,bacci suka yi wanda yasa zazzabin jikinsu ya sauka,kananun kukanta ne ya farkar da shi,dago fuskarta yayi yana ɗan zubawa cikin idanunta idanunsa da suke yi masa wani sakayau,kawar da kanta ta yi tana ɗan turesa daga jikinta,matsawa yayi daga jikinnata, sai dai kuma tana kallon yanayin da suke ciki daga shi har ita ta kwalla ƙara tare da mannewa a ƙirjinsa, sosai fuskarsa ta nuna murmushi me sanyi wanda ya fito tun daga ƙarƙashin zuciyarsa,tare da sanya hannunsa a wuyanta yana shafawa a hankali,ɗora hannunta ta yi akan nasa tana son cirewa, sai dai kuma bata wani kuzari hakan yasa ta tura fuskarta a ƙirjinsa tana cewa"daddy dama kai mugu ne ban sani ba?dama duk girman ciwon nan naka Ni zaka sany.......gum ta yi da bakinta saboda jin abinda take korafi akansa yana kokarin maida mata shi,hannu tasa ta turesa tana fashewa da kuka dan bata manta azabar da ta ci yan awowi da suka wuce ba,janye jikinsa yayi ba tare da ya tanka mata ba,doguwar farar jallabiya ya saka sannan ya shiga bathroom brush yayi ya sake fitowa ya fice daga ɗakin,tana jin alamun fitarsa ta miƙe a hankali tare da ɗaura towel, sannan a hankali kamar wata me jin tsoron taka ƙasa ta shige bathroom din, ruwa ta kuma shiga kamar yadda yayi mata ɗazun, aiko sosai ta kuma jin daɗin jikinta daga nan ta yi brush ta fito.tana fitowa ta samu ya kawo mata wasu dogayen riguna masu kyau, bata saka kayan ba har sai da ta gyara jikinta da ƙamshi duk wani loko da daƙo da tasan yana bukatar ƙamshi sai da ta bazaza masa,kana ta ɗan goga lips glow da kwarri a idanunta take idanunta suka ƙara yin wani haske abinka da fara,simple makeup ɗin da ta yi ba karamin fito da ita yayi ba,kayannta dauka zata saka sai kuma.ta dakata tana kallonsu,basu da nauyi dan gaba dayansu siririn hannu ne da su gasu kuma shara shara idan ta sa babu abinda ba za a gani a jikinta ba,ajiye kayan ta yi tare da riƙe ƙugunta kamar me shirin yin dambe, ƙamshinsa ne ya fara yi mata sallama kafin takunsa me cike da nutsuwa da izza irin ta sarakai,sai kuma kwanciyarsa da ta ji a gadon bayanta, janye jikinta ta yi tana tura ƙaramin bakinta da yasha lipstick yana ta shiening kamar zai ɗiga a ƙasa,cikin iananun shagwaba ta kallesa da idanunta masu haske da ƙyalli kamar an ɗiga musu maiƙo, ta ce"hana daddy wannan ai kalan iskanci ne ya za ayi na saka wa annan kayan knduba fa kaga“ta faɗa tana daga rigunan tare da cilli da su a saman gadon kana ta ɗora da cewa kalli fa kai kayi shiga ta mutunci amma Ni sai ka kawo min kayan ƴan iska to ai gara ma na zauna da towel ɗina aradun Allah"ta yi maganar tana ƙosƙarin gyara guntun towel ɗinnata da yake gab da yin ƙasa.

Duk abinda yake fada yana tsaye yana bin ko ina nata da mayen kallonsa da yake ratsata,shi yasa duk maganar da take ta kasa kallon idonsa,hannunta yayi saurin rikewa wanda hakan yasa ta tsorata har ta saki towel din yayi ƙasa,zata rungumesa yayi saurin zaunar da ita a gefen gadon yana ci gaba da kare mata kallo abinda bata so ɗin,rufe idanunta ya yi ta ana mis mis da bakinta dan maganar ma ta ki fitowa saboda tsananin kunya da ya rufeta,da kyar kalmomin bakinta, cikin in ina,dan Allah da daddy kayi hakuri since idan mutum yana kallon tsiraicin wani makancewa yake ni kuma bana so ka makance ka baka abbanmu ba a zahiri ba,Ni kaga na taba ganinsa a mafarki"tunda ta fara suritunta ya zubawa bakinta zuwa ƙirjinta ido kafin a hankali ya zauna kusa da ita yana mai sakata cikin jikinsa dan ji yayi yana neman kasa sarrafa kansa,itama shiru ta yi jinta a kirjinsa,daƙyar ya iya haɗiye abinda yake ji akanta ya daure ya sanya mata rigar dan yasan tana jin yinwa sannan suna da abubuwan da zasu yi daga kan ci gaba da karatu zuwa kan binciken da yake kan duk wani abu da ya shafi su Abby ɗin,yana gama sa mata ya mikar da ita tsaye tare da kan hannunta zuwa falo,dole tasa ta bude idonta babu shiri ta kuma mayarwa ta rufe saboda kayan da ta ci karo da su a jikinta,wai dama haka daddy yake bai da kunya?"ta tambayi kanta tana ci gaba da maida kafarta duk inda ya cire tasa.

"Bude idanunki"ya fada yana zaunar da ita a wata kujerar me taushi wadda aka yi mata kwalliya da wasu irin furanni masu kamshi da burgewa,bude idanunta ta yi tare da ba zasu a ko ina na wajen, karamin falo ne me dauke da set din kujeru ɗaya,,sai wani irin ado da aka yiwa falon da kalolin balums da suke dauke da tambarin i love You,ga teburin gabanta cike da kayan dadi dai dai cikinsu babu banna bare almubazzaranci gefe daya kuma sautin qira'ar sheik Muhammad sudais ce take tashi abin gwanin tada tsigar jiki,wani irin farin ciki ne ya lullbe aminatu,bata san lokacin da ta mike ta rungume mus ab ba tana dariyar farin ciki,shina mrmushi ne dauke a kan fatar bakinsa,wanda yayi sanadin janye War numfashin aminatu na yan sakanni,bai yi zato ba ya ji daukar tattausan lips din aminatu akan nasa lips din ta bashi wata irin kyautar sumba kyau mafi soyuwa da ya taba samu daga mace macen ma matarsa ta sunna abinda bai tana tunanin zai same sa ba rayuwarsa,dan haka ya tarbeta cikin farin ciki da bata abinda ya fuskanci tana matukar so a garesa wato murmushinsa,zaunar da ita yayi a kan cinyarsa ya shiga ciyar da ita daga cimar da ya tana da mata wanda duk abinda take so ne.

A wannan lokaci ne kuma yaron Abba Kabir ya samu damar shigowa gidan har cikin falon farko da zaka tarar a gidan,yana cikin canki in canka din dakin da yake da tabbacin zai samu littafin idanunsa suka yi masa kyakkyawan gani,take ya yi dariya me bayyana haƙora kana ya tunkari wajen tare da sanya hannu ya dauki littafin, sai da ya duba litattafin a kan wayar da ya tabbatar da shine sannan ya fice ta hanyar da ya shigo salin alin ba tare da kowa ya gansa ba,

******
Chapter 41 · 0% Book details