Sashe 46
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mus ab suna fita daga ɓangaren nan, kai tsaye Dr Idris ya kira, yana zuwa ya ce "yallabai wannan mutumin yau ne za a sallamesa kuma yana nan yace ba zai tafi ba har sai ya ganka ido da ido yayi maka Godiya"dan jim mus ab yayi sannan kuma ya jinjina kai tare da wucewa hannunsa cikin na aminatu da duk mamaki ya ishe ta akan abinda ya faru tsakaninsu da zahida,tunaninta ne ya katse lokacin da suka shiga wani daki me dauke da gadon majinyaci daya sai kujera doguwa guda daya da cafet da fringi, kana kallon dakin dai kasan cewa v I p ne,duk da cewa su nan basu da wani v i p sun dauki me kudi da talaka duk daya ne ba wani banbanci dan haka inda za a kwantar da me karamin karfi nan za a kwantar da me babban ƙarfi,kallonta ta mayar kan majinyacin da tun shigowarsu miyan bakinsa ya dauke, yunkurin da yake dan tashi tuni ya fasa, fuskarsa tuni ta nuna wata irin firgita da dimauta,aminatu ma zuba masa ido ta yi kafin cikin sauri ta dauke ta maida kan mus ab da bai kalli kowa a cikinsu ba,kafin ta yi magana ta ji muryar Dr idris yana cewa "to malam baffa wuro ga mutanen da kake ta son gani nan kuma sune masu wannan asibitin da duk wani abu da ya danganci sunan abm gaba daya, sai kayi musu godiya duk da cewa su ba ita suke bukata ba "daga haka ya juya ya fice daga dakin tare da rufo kofar ......
********
Alhaji Jamil Alhaji Garba da Alhaji Kabir, suna zaune a falonsu na gidan gona suna ta haɗa haɗar hada sabbin customer,baka Jin komai sai a falon sai dariyarsu cikin farin ciki da nishadi,Abba Kabir ne ya fara tsagaita wa da dariyar da suke akan tsoron da su mus ab suka ji suka janye karar da suke shirin shigarwa ya ce"amma fa ina dan jin shakka akan yaran nan wallahi gani nake kamar da wani abu da suka taka"Garba ya ce "kai ba wani abu da suka taka mun riga mun karɓe komai daga garesu, bakinsu kuma ba zai wadatar da su a ko tun ba kunga kuwa dole su janye,Abby ya ce "bari ma ku gani yanzu na sa su ɗanturqui su kashe yaron nan dan yanzu shi kadai ya rage mana gara mu aika shi tun kafin ya samu dama ya kufce ya dawo mana da aiki baya"cike da gamsuwa suka hada hannu ji kake fas fas sun tafa, daga nan abby ya sanya kiran danturqui,kira daya kuwa ya daga yana masa irin gaisuwarsu ta yan shaye shaye, dakatar dashi Abby yayi da cewa "ku kashe yaron nan kawai ku dauki gawarsa ku jefa ta can rami,idan kun kashe shi ku ɗauki vidon ka turo mana dan mu tabbatar"an gama oga kabar wayar ka a kusa da kai yanzu zaka ji sako"daga haka Abby ya kashe wayar suna ci gaba da kyalkyala dariyarsu.
Kwace wayar dake hannun danturqui wani basamude yayi, kana ya dubi na kusa da shi ba tare da ya ce masa komai ba, amma tuni ya gane me yake nufi cikin sauri ya fita jim kadan sai gashi dauke da kaza a hannunsa, mikawa danturqui yayi yana cewa "maza saka kanta gabas ka yankata akan wuyan Ahmad"zaro ido dan ladi yayi a tunaninsa shi za a yanka, to su su waye wadan nan ɗin?tambayar da yayiwa kansa kenan bai samu amsa ba yaji daya daga cikin mutanen yana cewa "yi sauri ka kwanta bamu da lokaci"kwanciya dan ladi yayi yana salati da fatan Allah ya kawo masa ɗauki,yanka kazar yayi wanda take ta fara tsartar da jini me uban yawa, saitata yayi saurin yi a wuyan dan ladi jinin na zuba a wuyansa yana gangarawa kasa kai idan ka ga dan ladi sai ka yi zaton yankashin a kayi da gaske,wanda ya fuskanci shine ogansu ne yayi magana ya ce"ka rufe idanunka ka yi kamar ka mutu za a yi maka video"kafin ya rufe bakinsa ma tuni dan ladi ya rufe idonsa tare da mirginar da kansa kamar matacce, video suka yi masa har da wukar da suka yanka kazar sannan suka turawa su Abby daga nan suka kwance dan ladi, tare da bashi wasu kayan ya saka,su kuma su danturqui suka tasa keyarsu bayan sun nuna musu ID din su,take jikinsu ya shiga rawa hankalinsu ya tashi ashe duk zaman nan da suke yi da jam'i an tsaro suke yinsa, ankwa suka sanya musu suka tasa keyarsu,dan ladi kuwa kai tsaye babbansu ya bada umarnin inda za a kai shi daga haka suka rufe gidan suka bar wajen.
Lokacin da videon ya shigo musu ba karamin farin ciki su kayi ba,dan haka take su ka hada shagali a daren ranar wanda suka dinga kiran abokan hulɗar su suna basu goron gayyatar,abunka da masu iko tuni suka saka oder duk abin da suke bukata kama daga kan abun sha da ci har zuwa kan kayan maye nau nau'i,har da mata saboda bakinsu masu bukata, to anan dai shima garba ya ce dole dai dan tuna kuruciya ko da na ranar ne.
Tunda aka kai zahida aka kwantar babu likitan da ya bi ta kanta saboda dama yawancin likitocin duk sun gudu saboda matsalolin da ake fuskanta a asibitin,dama ta bari ne idan sun hadu da abm sai su dauki sabbin ma aikata gigaggu kuma akan aikinsu,dan haka bata samu wata kulawa ba a matsayinta na wadda take tafiyar da asibitin, dan kanta ta farfaɗo daga doguwar sumar da ta tafi.
*******
Da sauri aminatu ta juya zata fita daga dakin,mus ab yayi sautin rikota yana kallon idanunta da suka sauya kala babu abinda suke fitarwa sai wani irin ruwan bakinciki da takaici wutar daukar fansa na ci a cikinsu,da ido ya shiga yi mata magana wanda hakan yasa ta tsayawa sai dai bata kuma kallon inda baffa wuro da iyalansa suke ba,kukansa ne ya karade dakin yi yake tamkar ba zai daina ba,kafin cikin kukan da ya ɗan rage sautinsa yake cewa"kaicona kaicona kaicon rayuwata wallahi nayi nadama na yi da na sani ba sai yanzu da na ganki a gabana na yi nadama ba,wallahi tun lokacin da na fahimci yaudarar da su jamilu su kayi min, Aminatu ki yafe min a madadin mahaifinki da mahaifiyar ki duk da nasan cewa hakkin ragowar jama'ar rigarmu ba zai barni ba,dan shine ya fara kamani tun yanzu, kallon yaransa da matarsa yayi kana ya ce"ko ba yan raina ina so ku guji taba mutum hakkin mutum ko da na dabbane da kuke gani ba karamin bala I ba ne dan hakki tun a duniya yake fara taba ka wala dukiyarka ko lafiyarka, wato hakki da kuke gani wani abu ne da baya taba barin mutum yayi gaba,ko bashi da kuke gani idan har mutum yana sane ma ana saboda mugunta ya hanaka to wallahi hakkinsa zai iya taba arzikinka duk abinda ka taba zai iya lalacewa, wannan nasiha nake muku a karo na farko a kuma matsayina na mahaifinku, kuma ina rokon yafiyarku dan Allah d....ya kasa karasawa saboda kukan da ya ci karfinsa,take zuciyar aminatu ta yi rauni nadamarsa da ta ganu tun daga zuciyarsa yasa ta ji ta yafe masa,kadan kenan daga cikin sakamakon Ubangiji akan tubatun nasuha,tuban da da kayi sa domin Allah daniyar ba zaka sake sikatashi ba, dan haka ta kallesa duba na Rahma ta ce "baffa wuro Allah gafururrahim ne me gafara, domin kullum kofofinsa na karbar masu tuba a gareshi a bude su ke,dan haka nima na yafe maka sai ka ci gaba da istigfar ga Ubangiji Allah ya baka lafiya ya kiyaye gaba"bata tsaya sauraron godiyar da yake mata tare da shi da iyalansa ba ta fice tana goge kwallar idanunta,shima Mus ab kallonsa yayi tare da cewa daga nan nasa a maida kai gidan ka saboda yanzu ya dawo hannunka daga wancan hannun da ka siyar kaga kenan yanzu zaka ci gaba da zama cikin gidanka hankali kwance saboda babu haram a cikinsa dan karar da haram din, yanzu kuma sai ka yi kokarin gina halak dinka dan haka idan ka yi tunanin sanar da zaka yi ka kira Ni kai tsaye"ya fada yana mika masa katinsa me ruwan gold, babban dansa ne yayi saurin karba yana zuba godiya, anan mus ab ya kuma yi musu albishir da cewa za su ci gaba da karatunsu dan ya dauke nauyin wannan bangaren.