← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 57

Sashe 52

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar jira Abby yake Abba sule ya rufe bakinsa ya yi wata irin zaburowa cikin wata irin shammata da basu taba zato ba ya janye aminatu tare da hankadata cikin dakin da suke kusa dashi ya rufe yana cewa "idan har kun isa ku kwace ta daga mutuwarta a yau dan sai na yanka makogaronta"ya fada yana saita kakkaifar wukarsa da baya rabo da ita a jikinsa a wuyan aminatu ,babu wanda a cikinsu ya kawo Abby zai iya tunkarar wani a cikinsu da niyar cutarwa duba da halin da suka tsinci kansu, shi yasa har ya samu dama akan aminatu,idanun mus ab kawai zaka kalla ka tabbatar da cewa a wannan karon ya kai kololuwar fusata da bakin ciki kuma zai iya aikata komai a cikin wannan yanayin da yake ciki,innawuro da Nana har da su anita da Hajara kuka suka sanya dan dukkansu sun shaida rashin imanin Abby sun san in dai ba ayi hanzarin balle kofar nan ba to tabbas sai ya yanka aminatu.abba Kabir kuwa ganin abinda yake faruwa a cikin asibiti yasa shi fita da gudu ya nufi a sibitin dan taimakawa Garba da suke neman cinna masa wuta ,tunda asibitin suketa zazzagawa fetur ciki da bai dinsa dan sun sha alwashin sai sun kona duk wata kadara da suka san ta gjk ce tunda da jinin iyayensu da yan uwansu a ka siyeta,Hajiya zahida kuwa ganin idan ta tsaya ta ce lallai sai ta ceci Garba za su hada da ita yasa ta su lale ta gudu abinta,daidai Abba kabir yana karasowa suna cinnawa asibitin wuta,da gudu ya shiga ya tattago Garba da ko tafiya me kwari baya iya yi suka fara kokarin fitowa , sai dai ina tuni wuta ta fara shanye fiye da rabin asibitin har ta fara taba inda suke,kasancewar kofar da zasu bi itama ci take ganga yasa suna ketota wani bangare na jikin kofar ya fado a bayan Garba,shi kuma Kabir barin jikinsa, lokacin da suka samu fita ta bayan asibitin wannan kofar da mus ab yasa aka fitar da innawuro, tuni wuta ta gama cinye gaba faya asibitin,su kansu basu yi zaton zasu tsira ba,suna fita yan sanda suka kwashe su,ko da suka isa devition din tuni likitan da zai duba su ya kara so,dan haka ana dan yi musu dressing aka watsa su cikin su danturqui da idan ba farin sani ka yi musu ba ba zaka iya gane su ba.

***

Sai da abby ya gama tabbatar da cewa sun rasa hanyar ceton Aminatu sannan yakyalkyale da dariya yana cewa, ba zan taba mutuwa ba tare da na bar muku tarihi ba,na san cewa a yanzu wannan yarinyar kawai zan kashe na jijjiga duniyarku dan na tabbata wasu daga cikinku sai sun bita, dan haka basu sakon karshe yarinya dan ina ga ma rai biyu zan kashe wata kila kina dauke da ɗan so"daga haka ya fallawa aminatu mari sai da bakinta ya fashe da hancinta daga nan yasa wukar akan wuyanta yana wata shegiyar dariya irin ta rikakkun azzalumai wanda suka yi hannun riga da imani,ya fara tamkar fatarta kadan yaji an yi wani irin yin sama da shi kamar wanda mala ika ya daga,ji kake hif ya fado daman kofar da mus ab ya ƙaryata da karfin kaunar aminatu, dan shi kansa Abby saboda yasan irin kofar da yayiwa gidan ne yasa ya yi wannan lissafin.

Kafa ya daga zai take kan Abby Abba sule ya dakatar dashi da cewa,"mus ab kar ka yi kisa, kabarsa da Ubangiji zaka ga sakamakon da zai yi masa"wannan furucin yasa mus ab ya rabu da Abby tare da ɗaukar Aminatu ya fice da ita,a bakin kofar suka hadu da zahida, wuceta zai yi ta tare hanyar tana cewa mus ab ka yi hakuri na yi nadama ka tafi da Ni duk inda zaka zan zauna da kai a ko wane irin hali kuma koda mata dari za aura zan zauna da s......wata irin hambara aminatu ta kaiwa bakin zahida da kafarta tana cewa Wallahi ba zamu zauna dake ba ahlin mugaye kije can kiji da masifar da bakin zunubinki ya jawo miki"kallon mus ab ta yi tare da sa kuka har tana kokarin sauka da ga jikinsa,ganin haka yasa shi saurin barin wajen bayan ya zaro wata farar takarda a aljuhunsa ya cusawa zahida a hannunta,babu wanda ya kula da abinda ya bawa zahidar sai ita, zubawa takardar ido ta yi, kafin ta warware ta a hankali, rubutun mus ab ne me kyau da tsari yana sanar da ita cewa ya sake ta saki biyu daga yau kar ta kuma bari ya hadu ko da da inuwarta ne,hannu ta ɗora aka ta zunduma ihu kafin ta fadi a wajen, lokaci daya bakinta ya karkace barin jikinta ya shanye.anna ce kawai ta yi kanta yayin da su nana suka bi bayan mus ab gaba dayansu hatta da larai bata tsaya ba, sai ya zamana daga Abby da yake kwance ya kasa matsi sai zahida da ke shimfide cikin rai kwakwa,sai kuma Anne dake kanta tana kokarin taimaka mata amma ta kasa saboda itama bata da wani karfi girma ya zo,shigowar isma ce ta sanya Anne farin ciki duk da cewa shi din ma hannunsa daya daure yake da ƙafarsa daya da duk suka sha bandeji da ga dukkan alamu ma dai kawo shi a kayi,da dan din gishiri ya karaso yana cewa Anne,"Ina Abby yake wallahi duk halin da muka shuga shine sanadi ashe dama zahida yarsa ce ashe dsma mus ab ba dansa ba ne?nima fa mus ab dinne ya sa wasu karti suka biyeni kuma dan rashin mutunci duk abinda ake ciki sai ya tiro musu sun sanar dani,yanzu ma su suka kunna waya suka nuna labaran da daddy Garba ya bayar akanmu Kum....hayaniyar da suka biyo daga waje da kuma karar jifa shine ya hana isma karasa maganarsa,cikin sauri ya kama hannun anne yana cewa"maza mu bar gidan nan dan nima yanzu da kyar nasha a hanya da tuni mutane sun kasheni da jifa" Anne ta ce babanku fa da zahida yana ciki kwance da alama mus ab ya karya kashin bayansa"haba anne da kanki kike janyo mana masifa kin san cewa kubutar da mutanen nan daidai yake da jefa tamu rayuwar cikin Bala i,mu ji ma da wanda suka jawo mana"yana gama fadin haka ya janyo hannun Anne suka yi waje da gudu.

Shima abby kokartawa yayi ya mirgina daga kwancen da yake tare da jan ciki dan fa da alama mus ab ya karya kashin bayan abby kamar yadda anne ta fada ɗin.yana fitowa da jan ciki ya samu zahida a yadda su isma suka barta,kuka ya saka a karon farko yana kallon kansa da zahida babu yadda zai yi ya taimake su,yana cikin wannan halin ne mutane suka samu damar shigowa cikin gidan baka jin komai sai iface iface da karar duwatsu,sun balle kofar falon kenan suka ji jiniyar yan sanda wanda hakan ya taimaki su Abby daga kisan wulakancin da mutane suka shirya yi musu,dauke zahida da abby su kayi aka nufi asibitin da yake karkashin hukuma, a take bincike ya nuna zahida ta samu matsalar shanyewar barin jiki sauki kuma sai Allah ya kawo,shi kuma Abby ya samu karaya a kashin bayansa, shi da zama sai dai yaga ana yi in dai ba aiki aka yi masa ba,babu abinda yake sai ihu da zage zage dan yana kallon tv da ke cikin dakin tana haska irin barnar da mutane su kayi musu, dan sun bi duk wani Company ko asibiti sun banka masa wuta, yayin da a gefe daya wasu daga cikin matasan da suka far musu suka dauke wayoyinsu tare da kutsawa cikin account din su suka kwashe miliyoyin kudaden da suke ciki kai tsaye suka mika ga gidajen marayu wasu aka rabawa talakawa musamman wanda duk ya kawo kokensa akan shima an taba cire masa koda a cikin asibitin ko kuma wani nasa,lokaci daya komai na su Abby ya zama tarihi, kallon wannan yasa abby ya zare babu abinda yake sai zagi da tsinuwa da tonawa kansa asiri har dq abinda mutane basu san ya aikata ba,daga karshe dai da kyar aka samu allurar da tasa shi baccin awa ɗaya.

*****

Suhaima da sule karami babu abinda ba su gani ba, tunda gaba daya duniya aka haska barnar su Abby,sun sha kuka iya kuka daga nan suka godewa Allah da ya tsamesu daga sharrin halin ubansu,sun yi masa addu'a saboda shine yayi sanadin da suka samu uwa kamar nana da kuma dan uwa kamar mus ab,ko iya haka sun yiwa Allah godiya, Khalid dai bai san komai ba saboda makarantar su cike take da matakan tsaro ta ko ina dan babu abinda suke sai karatu basu da wani lokacin kallo ko amfani da waya,tun da hakan doka ne,duk wanda zai yi waya daga gida a ofishin directer zaka yi wayar ka ka gama ta cikin katon laptop kuma video kana magana da mutum tamkar kuna a waje daya ne.

Mijin suhaima yayi kokari sosai wajen kwantar mata da hankali saboda yaron cikin da take dauke da shi, wanda Allah ya basu a yanzu bayan shekarun da suka dauka basu samu ba,da yaso kiran mus ab to kuma sai ya bari hankali ya gama kwanciya dan yasan su kansu suna cikin damuwa.

*******
Chapter 52 · 0% Book details