Sashe 42
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin ihu farin ciki zahida ta saki tana duba sakon email din da ya dawo mata bayan tsawon lokacin da ta ke ta jiran amsarsu, glass ta sanya tana kuma duba sakon dan dai ta tabbatar ba gizo yake mata ba,wai yau ita me wannan sa'ar?to idan hala ne lallai sa'ar kasuwancinsu tana gab da dawowa tunda har ta samu rana da time na haduwarsu da ABM hospital director,har ta daga waya zata gayawa Abby sai kuma ta fasa tana cewa bari mu fara haduwa mu tattauna idan yaso sai nayi musu surprise din da zai tashi kansu"...
Zahra✍️
8064537048 opay
Fatima yushau Adam
[5/12, 8:10 PM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page55``*
Tunda suka gama cin abincin ya koma gefe yana shigar da wasu muhimman sakonni ta cikin computer dinsa,a hankali aminatu ta matsa kusa dashi tana lekawa,"rufe computer yayi tare da matsar da ita daga kusa da shi, fuskarta ya shafa kafin ya ɗan sumbaci kumatunta yana cewa "yaya jikin hope dai yayi sauƙi?"rufe idonta ta yi tana ɗan mulmula bakinta, murmushin gefen baki yayi, kana ya ce"muje mu ci gaba da karatun ko?"dan jim ta yi kafin ta janye daga jikinsa tana shirin tashi,daga ta yayi cak ya dora a kafardarsa yana cewa nasan abinda kike jira kenan"tura baki tayi tana kwantar da kanta a ƙafadarsa,suna shiga dakin ya direta akan kujerar hutawa sannan ya dauko littafin ya dawo ya zauna kasan kafafunta, itama zamowa ta yi kasan tare da dora kanta a kafaɗarsa tana kallon shafin da mus ab ya bude, wanda hoton baffanta ya bayyana akai kamar yadda hoton abban mus ab ya bayyana,zuba masa ido mus ab yayi dan ba zai taba mantawa da fuskar da ta nuna masa kauna ba, a nutse ya bude musu shafin da rubutun ya ke.
*******
YUSUF LAMIDO.......
Yusuf lamido dan asalin garin Gombe ne,wanda yake rayuwa tare da mahaifiyarsa da matarsa a cikin rugar da suke kira da rigar malam Yusuf,malam Yusuf mutum ne me mutunci da son kyautatawa na kusa da shi,yana da ilmin addini matuka gaya dan shine yake koyar da duk dattinjan rigar da yara matasa,baffa Yusuf yana da tarin arzikin dabbobi da na gonaki da shanaye wanda shi kansa bai san kimarsu ba,dan wani lokacin ko satar dabbobi aka yi masa baya fahimta sai dai idan ya gansu saboda shedar da yake gane dabbobinsa da su,duk wata dabbarsa tana da shedar sunan aminatu da Hausa ajami, shi yasa da wuya ko za a yi sata a saci dabbar baffa Yusuf saboda ko ka sata idan ka kai cikin gari sayarwa to fa suma sun san kayan baffa Yusuf sai dai kaji an yi ram da kai,daga karshe ma sai satar ta yi sauki saboda yadda baffan ya dauki nauyin matasa a kan duk wata sabgarsu, sana a zaka yi aure zaka yi karatu ne duk abinda yake da amfani baffa Yusuf ya dau nauyinsa,shi yasa mutanen rugarsu suke kallonsa kamar wani waliyi,baffa wuro makocin baffa Yusuf ne wanda aminci ya shiga tsakaninsu,duk wata ɗawainiyar gidan baffa wuro baffa Yusuf ne yake yinta.
Mahaifiyar sa me suna zainabu amma suna kiranta da innawuro ta dauki baffa wuro tamkar da,ita kuma matar baffa wuro me suna fatsima ta dauke shi yaya, dan haka baffa wuro yana da babban matsayi a cikin ahalin Yusuf , duk wata yardarsa ya dorata akan wuro,shi yasa wuro yasan yawan arzikin da Allah yayi wa Yusuf.
Matarsa Fatsima ta jima bata haihu ba,sai kuma lokaci daya Allah ya kawo mata karuwa,haihuwar aminatu ta zo da abubuwa masu tarin yawa wanda suka shafi arziki,baffa Yusuf a duniya babu abinda yake so sama da aminatu, bai sani ba ko dan bai taɓa haihuwa ba ne, amma shi kansa ya san yana kaunar aminatu,kai ko ga sauran mutanen rugarsu, aminatu me farin jini ce,duk da cewa ta taso da yawan tsokana a cikin kuruciyarta,inna wuro ita ce kome na aminatu tun tana karama,shekarar aminatu uku a duniya, a wata ranar Laraba baffa Yusuf ya kwashe iyalansa gaba daya suka fita birnin Gombe dan siyayyar abubuwan amfani,kafin dawowarsu ne cikin yammacin ranar,wasu mugayen mutane da aka rasa suwa ye suka shigo rigar su kayi sata me tarin yawa kama da kan kwace takardun gonaye da filaye har zuwa kan dabbobi,daga nan suka kama wasu daga cikin yaran garin suka tafi da su lokacin da baffa Yusuf ya dawo ya shiga tsananin tashin hankali,take yan uwa suka bashi shawarar ya saida kome ya tattara ya bar rigar dan a ko da yaushe mutane zasu iya dawowa saboda duk wata gona me girma idan suka bukaci takardunta sai baffa wuro yayi tsagal ya ce ta yusufa ce,duk yadda mutanen garin suka so boyewa hakan bai samu ba sai da mutanen sun san waye Yusuf ta hanyar baffa wuro wanda shi acewarsa ya fada ne saboda tsoron kar su yi musu wani abu.
Baffa wuro ya dauki shawarar mutanensa amma ya tabbatar musu da cewa ko zai canja ruga dole sai idan zasu bishi,to dake a tsorace suke kuma baffa kamar shine shugabansu a komai,Dan haka suka amince, washe gari baffa ya tattara dukiyarsa wadda zata tattaru suka tasa shanayen baffa suka kuma nausawa cikin jeji, basu suka tsaya ba sai da suka tabbatar sun yi nisa da rugarsu ta baya, sannan suka yada zango a cikin jejin, inda cikin lokaci kankani suka sauya shi ya koma cikakkiyar riga dan hatta da makaranta da masallaci sai da suka yi,daga nan suka fara rayuwarsu cikin kwanciyar hankali a karkashin arzikin baffa Yusuf,saboda kowa sai da ya bashi sana ar da zai yi saboda temakon kansu,ko sarin kaya za a fita cikin gari mutum biyu suke wakiltawa suma ta boyayyiyar hanya suke fita haka ta wajen dawowa suna taka tsantsan da duk wani bakon fuska.
Sun dauki shekara guda cir a cikin sabuwar rigar su,suna rayuwa cikin farin ciki,dan har sun fara farfadowa daga tashin hankalin rashin kadarorinsu,dabbobin su sun fara yalwanta dan Allah ya sa musu albarka acikin wannan riga,kwatsam rana tsaka suka kuma samun sumamen wadan nan mutane wanda hakan ba karamin mamaki ya basu ba,dan su sun tabbatar da cewa suna matukar taka tsantsan da fita da shigarsu,haka suka kuma kwasar dukiya da wasu daga cikin mata suka fice dasu,ba tare da kowa yaga fuskarsu ba bare ya shaida ko su waye.
Amma abin mamaki duk abinda mutanen nan suka kwasa bai girgiza dukiyar baffa wuro ba,wanda har mamakin hakan shi kansa yake yi,dan wani lokacin ma sai yaga kamar ba Adauki kome ba,ko kuma yaga an dawo masa da wani abu daga cikin abinda suka karba,a wannan lokacin ba su canja riga ba har sai da hakan ta kuma faruwa sannan suka kuma yin hijira zuwa gaba,daga nan ne kuma suka fara bincikar junansu dan sun tabbatar akwai me fitar da sirrinsu zuwa ga wannan mutanen,sai dai duk yadda suka so ganowa basu gano ba, wannan karon yalwal arzikinsu yafi na waccan rugagen da suka baro, baran ma arzikin baffa Yusuf da ya kuma nunka na baya.
Acikin haka ne wasu baki suka yi musu tsinke,da farko sun tsorata a tunaninsu ko wadancan mutanen ne da suka addebesu,sai da suka yi musu bayani akan cewa su masu binciken dajika ne,sun zo ne dan daukar yanayin wannan dajin saboda da farko bai nuna musu da mutane a ciki ba, wannan bayanin yasa suka amince da mutanen har da yi musu sauka ta mutunci babu abinda baffa Yusuf bai ajiye musu na jin dadin rayuwa ba.
Kwanansu goma suna binciken yanayi a cikin rugar babu wani abu da ya faru, sai a cikin kwanansu na sha daya ne, aka fara tashi babu wasu daga cikin mutanensu,tun suna ganin abin kamar me wucewa ne har abun ya fara isarsu,saboda rashin da suke yi ya yi yawa,a cikin rashin da suka yi har da na mahaifiyar aminatu,wanda hakan ya kuma tashin hankalin baffa Yusuf take ya fara binciken wadannan bakin mutanen ba tare da sanin kowa ba, har Allah ya sa ya gano cewa sune mutanen da suka dinga kawo musu hari, yanzu sun canja salo ne shi yasa suka zo musu da wata fuska,kuma sune suke dauke mutanensu suna kaisu can cikin gari suna amfani da wani sashe na jikinsu,kama daga kan zuciya zuwa ƙoda ko dai wani abu da ake bukata daga jikin ɗan adam,lokacin da baffa Yusuf ya gane hakan ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba, cikin hikima da sirri ya fara janye mutanensa yana fitar da su daga rugar,tashi kawai mutanen su kayi suka ga babu kowa cikin rigar,a lokacin daga baffa Yusuf sai baffa wuro dan hatta da iyalan baffa wuro ya fitar da su,ajikinsa ya ji bai yadda da baffa wuro ba,amma dan ya tabbatar da abinda yake zargi sai bai nuna masa komai ba,cikin dare suka sulale suka bar rugar shida wuron.
Sabuwar rayuwa suka bude a sabon wajensu,sai dai basu saki jiki kamar yadda suka saba ba,kowa a darare yake dan sun tabbatar akwai munafikin da yake tare da wadancan mutanen a cikinsu,baffa Yusuf bai baza dukiyarsa yadda ya saba ba,dan haka kowa cikin kaffkaffa suke da junansu,dukiyar baffa Yusuf kuwa a tsare take dan ko sun kwace in sha Allah washe gari zai ga abinsa ya dawo kuma gaba daya gonakinsa babu abinda yake taba su,ba ko mai ne yasa hakan ba,sai wata bafulatanar aljana da take tare da shi tun yana cikin tsumma, tun baffa Yusuf bai san da ita ba har dai ta bayyana a gareshi yasan ta da kuma irin temakonta a garesa,ana cikin haka ne baffa Yusuf ya kwanta matsanancin ciwo wanda ya debesa watanni, gashi kuma ya hana a kaisa asibiti,daga karshe dai baffa wuro ya lallaɓasa akan ya yarda ya kawo likitan da zai duba sa amma baffa Yusuf yaƙi dole baffa wuro ya rabu dashi.