← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 57

Sashe 17

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sosai take kuka tare da tada ikama tana jin wani rin imani na tsarga mata,tana jin kamar daga ita sai Ubangijinta ne a duniyar, take ta kadaice Ubangiji daya ta kuma yi yakini ta fuskance shi da bukatun da ita bata sansu ba amma tasan shi ne mafi sanin komai, saboda shine makaginta masanin gaibu dan haka ta yi imani zai ji kukanta,saboda tsananin miƙa wuya bata jin komai sai kiran Ubangijinta shi yasa har mus AB ya jeru da ita bata sani ba.

Shima din ba bacci yayi ba duk abinda aminatu take.yana jinta yana sauraronta,a ransa yaji cewa damuwarsa dan haka shi dinma ba bukatar baccinsa a wannan lokacin.Allah Ubangijia ya bamu ikon cinye dukkan jarrabawar rayuwarmu ka kara mana kusanci da shugaba masoyinka da babu kamarsa a duniya da lahira Annabi Muhammad s.a.w, Allah ka amsa addu'ar bayinsa ka gafarta mana zunubanmu ba dan halinmu ba

*****

A daidai wannan lokacin da nagartattun bayi suka mikawa Ubangiji dukkan lamuransu domin sun san idan yayi riko da hannayensu babu wanda ya isa ya kama domin ganin bayansu,a lokacin ne kuma wanda suka juya masa baya suke ganin waninsa zai iya ije musu lamarinsu su kayi gurfane agaban waninsa,(wa iya zubillah).

Abby daddy Abba,mutanen da suka nutse cikin kasa tamkar an shafe bakinsu a duniya sune gurfane gaban wani yamutsetstsen tsoho da ko ƙashi babu ajikinsa,tabbas ba dan tsananin ƙarfin iko na Ubangiji ba to da tabbas tsohonnan ba zai iya koda motsi ba saboda yadda yayi yaushi fata ce kawai take buga zamaninta a jikinsa,

Yunƙurin tashi yayi daga kwancen da yake tamkar wani jiƙaƙƙen tsumma yasa suka kuma ƙankan da kansu,ga tsananin mamaki na yana tashi wata irin guguwa ta shiga kadawa a cikin kogon har wajen kogon,yayin da bishiyu suka shiga rangaji tamkar wanda zasu fado daga jikin reshinansu namun daji da tsuntsaye kuwa tuni suka fara yin takansu iblisan aljanu kuwa take suka fara haniniyar farinciki saboda sun san lokacinsu yazo, gaba daya kogon ya turnuke da wani rin ɓakin hayaki ko tafin hannunka baka isa gani ba,take wani irin gurnanin zaki ya fara tashi a cikin kogon da haniniyarsa, kafin kuma lokaci daya hayakin ya washe sai wani rin jan haske wanda a cikinsa na gano wani turmushshen zaki bakiƙirin idanunsa kuwa sune suke bada wannan hasken jan, abinda zai baka tsananin mamaki babu ɗaya daga cikin mutanen nan uku da ya razana, har yanzu suna nan durƙushe agaban wannan yamusheshshen tsohon arnen bokan wanda a yanzu ya rikiɗe ya koma baƙin zaki me jajayen idanuwan da yake bawa kogon haske..........

Zahra...
[4/25, 6:45 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page40``*

Bude bakinsa yayi zai yi magana sai ga wani irin ɓakin hayaki yana fitowa daga bakin me shege wari, amma duk da haka babu wanda ya damu a cikinsu,

Karar sautin maganarsa kadai abin razanarwa ne da ace da me imani a gun tabbas zai iya sumewa saboda jin sautin maganarsa.

"Kunzo akan lokaci da ace kun bari se bayan wani lokaci to da babu abinda zan iya yi muku,jamilu ka yi sake tabbas ka yi sake kaima Garba kayi sake,dukkan ku masu kuskure ne Kabiru ne kawai bai yi wani abu ba a cikinku,amma ku da kanku kune kuka jawo matsala cikin tafiyarku,me yasa kuka haka?"ya tambaye su yana kallonsu da siffarsa ta zaki da idanunsa masu hasken ja,"abby ne yayi Magana cikin ƙankan da kai"ayi mana afuwa hakan ya faru ne ta sanadin sharaxin da ka bamu na nisantarka tsawon wannan lokacin"cikin wata irin gigitacciyar tsawa tamkar saukar aradu ya ce"to yanzu me ya dawo daku?"gaba dayan su suka.hada baki wajen cewa,saboda lokacin yayi daidai da lokacin da ka kwatanta mana na dawowarmu gareka"girgiza kai yayi ransa a matukar ɓace ya ce Kum yi kuskure ba wannan lokacin na misalta muku na dawowa ba,lokacin tuni ya riga ya shude,sai dai hakan ba yana nufin zan ƙi taimaka muku ba ne tunda kuna da sauran dama"

Daga haka ya yi wata girgiza ya koma suffarsa ta ya musheshshen tsoho sannan ya shige wani waje dake can ƙuryar kogon, ya jima kafin ya fito hannunsa rike da wani jan ƙoko yana zuwa ya miƙa musu ƙoƙon yana cewa da farko dai dole sai mun fara dauko wancan littafin da AMINATU ta dauke a dakinka idan ba haka ba babu wani abu da zan iya yi muku saboda ruhinku da ruhin mutanen da kuka sha jininsu da duk wani tarihi na baya da ya shafi rayuwarku yana cikin wancan littafin kuma karanta shi shine makullin bude masifun rayuwarku da mu ka sa a ciki muka kulle"a razane suke kallon juna kafin cikin madaukakin mamaki ,abby ya ce idan aminatu ta dauki littafi shi kuma wanda na gani a dakin fa meye?ya akayi ta shiga bangarena da yake da matukar tsaro?babban abin mamakin ya aka yi ta iya daukar littafin a hannunta bayan kai da kanka ka sanar damu cewa idan ba daya daga cikinmu ba babu me iya daga littafin nan a duniya?"wata irin muguwar dariya sunduƙi ya shiga ɓaɓɓakawa babu ji babu gani kai baka yi tunanin zai dakata da dariyar ba sai kuma lokaci daya tamkar an dauke nefa yayi ɗif idanunsa sun koma na zaki sai wani rin duhu da ya mamayesu,cikin tsawa ya ce "ku kalli idanuna"take duk suka zuba masa ido tsawon sakanni hamsin sannan ya basu umarnin janyewa, ya dora da cewa me kuka gani a cikin idona?" Babu ko mai sai duhu"suka hada baki wajen bashi amsa,dariya ya kuma sheƙewa da ita kana ya ce,to Nima abinda na gani kenan dan haka bani da amsar tambayarka,lokacin da na baku littafin nan Ni nasan cewa babu abinda ya isa taba shi ko ɗaga shi, sai kuma yanzu ga shi an samu wadda ta daga shi daga jinsin mata, sannan littafin da ka gani shima bashi ba ne an sauya shi ne domin janye hankalinka Ni kaina sai da nayi da gaske wajen fahimtar bashi din ba ne, wannan dalilinne yasa na shiga kogon duba amma abinda kuka gani a idona nima shi na gani wato banga dalilin da yasa ta iya dauka ba ban kuma ga ta yadda ta shiga dakin ba,banga kuma ta yadda kayi aka sauya littafin da irinsa ba,abu daya ne ya bayyana a cikin duhun shine fuskarta, dan haka zaku zauna anan na tsawon kwana uku zan yi aiki tare da ku dan dawo da littafin amma muddin hakan bata yiwu ba to sai dai kaje kayi mata ta karfi ka karɓa littafin sannan ka tabbatar bata fara karanta ko wane shafi ba duk da cewa duk shafin da ta karanta zata dakata akansa ne har sai ta warware matsalar shafin Farko sannan zata kuma bude wani shafin dan haka sai ku daura damara"daga haka ya ɓace ɓat a cikin kogon ya barsu cikin tashin hankali da rabuwar tunani,duk da cewa sun yadda da sunduƙi amma suna cikin tashin hankalin abinda ya fada,tabbas aminatu ta karanta littafin nan shike nan ta bude makullin masifun rayuwarsu, komai da suka aikata akan mahaifinta se ta gani a ciki ,kai hatta da sirrin da suka binne a junansu sai aminatu ta karanto shi.....

******

Washe gari da safe zahida da ta farka bata ga iyayenta ba,sai kawai ta shirya ta wuce gidan Anita,duk cewa har yanzu bata ji zata iya bude mata cikinta ba,amma dai tasan idan ta je ɗin zata samu nutsuwa da wasu shawarwarin daga gare ta.

....

Aminatu kuwa lafiya kalau ta tashi duk da cewa ba wani bacci ta yi me yawa ba,dan basu kwanta ba har sai da su kayi sallar asuba daga ita har mus ab din,tana zaune a falonsa ya fito cikin shirinsa na office, kallo daya ta yi masa ta dauke kanta,shima kallonnata yake saboda ganin har yanzu jikinta a sanyaye yake gaba daya aminatu ta sauya lokaci daya abinda bai taba tunani ba ke nan anan kusa,so yake kawai yaga mood dinta ya dawo , a nutse ya zauna gefenta har kafadarsu na gugar juna,matsawa ta yi tana dan tura bakinta sai dai bata ce komai ba,a hankali ya kai yatsunsa saitin idonta kamar zai tsokane idon,aiko da sauri ta zabura tare da juyowa ta fuskanceshi fuskarta a kwaɓe alamun kiris take jita ta fashe da kuka,dage girarsa daya yayi tare da yi mata maganar bebaye wai meye na kukan, kawar da fuskarta ta yi tana tuna fuskar mahaukacin nan wanda duk wani motsinta tunaninsa ke karuwa a ranta, sosai ya fahimci yanayinta, yana so ya rarrasheta yasa ta ta yi farinciki sai dai bai san ta ina zai fara ba, a hankali ya lumshe idanunsa tare da kamo hannunta daya ya ɗora a kan ƙirjinsa, sai kawai ta bude idanuna sosai tana kallon fuskarsa da gashin idanunsa da su kayiwa idanun rumfar saboda lumshesu da yayi ta bangare guda kuma tana sauraron bugun zuciyarsa da yake bugawa akan tafin hannunta.
Chapter 17 · 0% Book details