← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 57

Sashe 45

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna juya baya sunduki yayi bindiga ya fashe tamkar wani bom haka kogon ya tashi da wuta,wutar na gama ci wajen ya shafe ko alamun wutar babu bare tokar sunduki,(Allah ya shirya mu ya bar mu kan tafarkinsa Allah yatsaremu gogayya da makusantan irin wannan mutanen , Allah yaranmu masu tasowa ka kare mana su ka shirya mana su ka basu halak komai kankantarta ka kuma basu hakuri da kankantarta ka saka musu wadatar zuci, wallahi duniya ba bakin kome take ba,duk wanda yayi hakuri wata rana sai labari, wani ma arzikin da dako ya fara ya sameshi wani kuma da jan kurarruwa, idan fa za mu tsaya mu nutsu mu yi nazari zamu ga cewa duk wanda su kayi arzikin nan ba haka suka samesa ba, tabbas sai da suka sha wuya kuma su kayi hakuri idan ka lissafasu ko a cikin dangi ko a wani gurin da kuka san asalin me kudi zaku ga duk yawancinsu yan kauye ne wanda basu sakawa kansu girman kai ba,ko kuma wadanda suka yiwa iyayensu hidima cikin rashi ko samu wanda basa kyashi ko jin kunyar tallafawa na kasa dasu masu kyakyarwa niya da son aikata alkairi,idan kuma kuka ci karo da akasin haka to lallai ishara ce daga Ubangiji zuwa garemu, domin hausawa sunce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah,mu yi kokari mu cire son ya'ya mu tsaya akan tarbiyarsu tare da addu'a akan Ubangiji ya taya mu ya shirya mana su kan hanya madaidaiciya,rayuwa ta lalace musamman a wannan zamanin dan haka kar mu zauna mu saki baki muce wai Allah ya shirya, ey dama ke kike shiryawa Allah ne me kome amma komai akwai sanadi dan haka ki tashi tsaye da addu'a da kwanji da kuma nasiha ki ceci rayuwar iyalanki, Allah ya shirya mana dan alfarmar shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w).

****

Yau ne kwanakin da ABM suka bawa zahida na haduwa da su,dan haka tun safe bata je ko ina ba,hatta da larai da anne sai da suka gane cewa zahida na cikin farinciki,ban da kaiwa da kawowa babu abinda take yi,ta yi shiri ta sauya ya kai dau goma,duk dan kar taje su rainata, saboda a kwanakin da take zaman juransu sosai ta yi musu kutse cikin al'amuransu dan bayan asibitin ta kuma.gano wasu boyayyayyun asibitocin kusan uku da kuma gidajen mai masu irin sunansu wanda bincike ya tabbatar mata da nasu ne,ga kuma companies da suka tashi kanta lokaci daya arzikin ABMs ya tashi kanta ya nemi kusan zarar da ita,tabbas ABMs sune irin mutanen da ta jima tana nema domin ta yi mu amala dasu ta bussiness sai gashi ta da ce cikin laluben da bata tsammaci haka daga cikinsa ba.

Karfe biyar saura mintina a sharin ce ta yi mata cikin hamshaqin asibitin da duk zagayenta na yawon duniya bata taɓa cin karo da me kyau da tsarinsa ba,tun daga harabar asibitin zaka san cewa an kashe mata kudi bana wasa ba,kuma wai ace duk domin talakawa kuma ɗan Allah,kai dole akwai wani abu a kasa makamancin nasu,abinda zahida take sakawa ranta ke nan tana faman bin ko ina na asibitin da kallo,tana nuna shedar da aka turo mata a waya, taga wani babban mutumin yaiso gare ta tare da nuna mata hanya bayan sun gaisa,yana gaba taba binsa a baya ,tana kuma da da shan mamakin asibitin ko ina ja a ne ,masu jinya da masu lafiya suna hadagadarsu cikin tsari da kwanciya hankali, likitoci kawai take cin karo da su jar fata da bakar fata suna faman zagaye suna duba marasa lafiya cikin kula da tarairaya,a ranta ta ce dama nima tun farko na saki raina na nuna musu kauna da yanzu asibiti mu ce akan wannan matsayin,amma yanzu ma lokaci bai kure ba zan gyara kasuwanci ne ta yadda sai na rufe babin abms a duniya,daidai lipter ta sake su a hawa ba bakwai,inda mutumin ya bude mata wata hadaddiyar kofa ta shiga,take jikinta ya kuma mutuwa zuciyarta kuwa cike take da zumuɗin ganin wannan mutumin da ya bawa raywarta wahala.

Nuna mata wajen zama mutumin yayi tare da dan russunar da kai sannan ya koma daga wajen kofar ya kame kamar wani gunki,

Takun da zahida ta ji tare da kamshin da yake kusanto ta ne yasa ta maida hankalinta saitin wajen da ya raba inda take da wasu shegun labulaye ido, yayin da zuciyarta ta shiga wani irin bugawa da karfi, duk takun da za a yi yana tafiya da bugun zuciyarta ne,wai waye ABMs din nanne?ta tambayi kanta daidai lokacin da aka dage dogon labulen da yayi shinge da tsakaninta da ABMs.............

Zahra✍️✍️

Opay Fatima yushau Adam
8064537048

Decommen is coming

Payment is 1k
[5/14, 3:31 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page57``*

Cikin wani irin azabar bugun zuciya da hanzarin da ya wuce hankali ta miƙe tsaye bakinta sake,idanunta a buɗe ƙofofin hancinta gaba dayansu a bude, numfashinta kuwa take ya fara barazanar barin ƙirjinta,cikin fitar da numfashi sama sama kamar me asma ta bude bakinta da yake wani irin karkarwa cikin in ina ta ce"ke ce"?a hankali kuma cikin nutsuwa da takun birgewa ta ƙaraso ta zauna cikin kujerarta da take juyi kamar fanka,a hankali ta ɗauki ƙafarta ɗaya ta ɗora akan ɗaya tare da zare glass ɗin da yayiwa kyakkyawar fuskantarta kawanya, sannan cikin sanyin muryar ta ta ce"nice mana kin yi mamaki ne?"wani irin kallon tashin hankali da fitar hayyaci zahida ta yiwa AMINATU tana cewa "Wallahi ƙarya ne ni za a mayar 'yar iska? maza ki kira min ABMs din ko yanzu na ɓaɓɓallaki a wajen nan dan wallahi sai na huce fushina na tsawon rayuwar da muka yi da ke,shegiya me kwacen miji,yanzu kuma kin bar ƙwacen miji kin koma kwacen dukiya ko?"aminatu ta ce "eh mana da ke kin san abin gado ne daga uba"sharaf zahida ta yi a dandagaryar kasan wajen tana kallon aminatu cikin sarewa kana ta ce"wai da gaske kike ke ce ABMs?"

Muryar da ta ji yana bata amsa da cewa "tabbas" ne ya sa ta suman zaune, Bala i kan Bala i kenan wane irin mafarki ne wannan,ya Allah ka gaggauta farkar da Ni daga wannan mummunan mafarki"ta fada tana kallon MUS'AB da yake takawa a hankali cikin kamewarsa da wannan asalin fuskar tasa da ta sani mara fara a da rashin daukar raini ga kamshinsa da ya cakude da kamshin aminatu da tun shigowarta office din take jin kamshin yana ratsa kofofin hancinta, bayan aminatu ya tsaya tare da zura hannunsa ta cikin wuyanta yana gyara mata zaman sarkarta,aminatu kuwa bulhakki ta sanya masa kukan tabara wai dan me zai fito,cikin kananun hawaye ta sanya karamin hannunta ta janye nasa da yake wuyanta yana shafa zaunannen wuyanta da yayi dabas babu rama bare kuma wajen da kashi zai zauna,ta ce "cewa nayi fa karka fito daddy har ka bari ta tafi"a hankali ya ɗan sunkuyo da kansa saitin wuyanta ya sumbata kana cikin dakakiiyar muryarsa wadda ya tausasata ingantata wajen rarrashin gimbiyarsa ya ce"Ni bana tsoro akan duk abinda zai same Ni, amma ina tsoro akan duk abinda ya shafeki duk abinda zai kusance ki indai na cutarwa ne to na yi alkawarin shiga tsakani nayi alkawarin kare rayuwarki d dukkan karfina da zuciyata da kuma numfashina, addu'a ta kullum ita ce Allah ya bani dama ya bani ikon kula dake fiye da zinaren da aka hako cikin tsananin yunwa da ishi,ya bani ikon riritaki fiye da jaririyar da ake da tabbacin cewa daga ita ba kari ita ce ta farko kuma ta karshe,to ta yaya kike tunanin zan barki tare da kurar da ta jima ta na farautar namanki eh?"kalamansa ba karamin sanyin jiki da na zuciya suka saka mata ba,idanunta tuni suka fara zubar da kwalla,cikin sauri ta mike ta rungumesa tana wani sakin marayan kuka kafin cikin wani 4iin shaukin da ya bayyana tun daga kasan zuciya ta ce"daddy i love....shiiiii ya katseta bayan ya dago kanta da ido yayi mata alamar cewa ba anan ba ta adana kalamanta domin suna da tsadar da ba zai iya sharing din junsu da wani ba,da karfi ta kuma rungumesa tana sakin wata yar sassanyar dariya, och ya fada yana dan yatsuna fuska cikin sauri ta sakesa tan tambayarka lafiya cikin rushewa da bayyana tsananin damuwa,kanta ya nuna sannan ya nuna saitin zuciyarsa da wuyansa sai kuma alamar mutuwa,dukan kirjinsa ta yi tare da shigewa cikinsa tana fidda wani irin murmushin da ya kusa sumar da dan gidan Nana.

Kukan da zahida ta fashe dashi ne ya sasu kallon in da take,hango ta su kayi har ta kai bakin kofa cikin rarrafe, numfashinta da kyar ya ke fita kamar zata mace musu anan,zamewa aminatu ta yi zata nufeta ya yi saurin riketa yana girgiza mata kai,waya ya dauko yayi yan danne dannesa sannan ya janyo aminatu suka fice daga office din,wani uban ihu zahida ta kurma tare da zubewa wajen a sume,cikin sauri Dr ele ya kira mus ab ya sanar da shi,kai tsaye ya ce su kai ta can Asibitinsu gjk kar su sake su kwantar da ita a nan,cikin bin umarni Dr ele yasa aka ɗauki zahida kamar wata gawa aka saka ta a mota ,kai tsaye asibitinsu aka nufa da ita.
Chapter 45 · 0% Book details