Sashe 37
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babban asibiti suka gida suka fara da taimakon mutane da basu magani kyauta, kai duk wata hanyar yaudara sai da suka yi ta akan asibitin nan, inda kuma suka samu nasarar kama.kutame a hannunsu,da wannan damar su kayi amfani suka yaye kansu daga hannun ubangidansu, suka suka gina kansu ta hanyar zama masu gidan kansu,lokacin da zahida ta dawo da nata halin da kuma burinta sai abin yayi musu dadi, sai da suka dan yadda su kayi suka hada aure tsakaninta da mus' ab, sannan ta fara aiki a asibitin gjk,babu wanda suka.yadda dashi akan kasuwanci su shi yasa basu sake jiki ma aikatan asibitin sun san me suke aikatawa ba,likitoci biyun da suka san me ake yi suma siyansu su kayi da kudinsu kuma suka basu ilimin da kudinsu,dan haka basu taba kokarin tona musu asiri ba.
Sunduƙi da kansa ya basu hutu ya kuma yin musu misalin lokacin da ya kamata su dawo gareshi, wannan shine ka idar aikinsa baya so ka kuma waiwayarsa sai masifa ta tunkaroka.
Nana da mus' ab kuwa tamkar an goge musu tarihin rayuwarsu a cikin kwakwalwarsu ne,dan kuwa basa tuna kowa a matsayin uba da miji idan ba Abby ba.
Cikin nutsuwa aminatu ta dago da kanta ta kalli mus ab da idanunta suka yi ja sai dai tas ya shanye baki cikinsa da damuwarsa,hannunta ta kai saman dogon hancinsa ta ɗan ja tare da cewa, wannan shine tarihin abbanka daddy,a yanzu na riga da nasan yadda zuciyarka take zafi, sai dai kuma Ni nayi farin ciki saboda na tabbata Abba bai mutu ba kuma in sha Allah sai nayi addu'a akan Allah ya bashi ikon sanar da Ni inda zan samesa kamar yadda take son sanar dani"jinjina kansa kawai yayi tare da maida bayansa jikin makarin gadon yana rufe idanunsa da suke masa wani irin yaji.........
Itama kwantar da kanta ta yi a jikinsa tana jin wani irin mugun tausayinsa da shi da babansa har ma da Nana.
*******
Su Abby kuwa tunda su aminatu suka.fara karanta shafin nan suke ganin Bala U kala kala,daga inda zasu ji ana kiran sunansu, sai inda zasu dinga ganin inuwa tana gifta musu,kai har da kukan jarirai,ga wani irin azababban ƙaikayi da jikinsu yake yi babu abinda suke sai soshe soshe,gaba dayan su suna tare dan basu yarda sun rabu ba dan a halin yanzu dukkansu sun fara shiga cikin tsoro da firgici na halin da suka tsinci kansu,basu suka dawo hayyacinsu ba har sai da su aminatu suka gama karanta labarin sule,wanda hakan yasa su hanzarin komawa wajen sunduƙi dan nemo mafitar da ya ce musu zai yi idan shafin sule ya kare.
Tunda Ahmad ya samu ya subce daga wannan gidan yake gudu ba tare da waiwaye ba,duk da cewa babu kuzari a jikinsa amma haka yayi ta maza ya ci gaba da gudu,bashi ya tsinci kansa a titin ba sai da gari ya fara duhu, daga nan ya samu me nafef ya kwatanta masa gidan cp Musa.
A bangaren kasuwancinsu fa komai ya tsaya dan tunda suka fara shiga wannan matsalar harkallar da ake a cikin asibitin ta tsaya cak, to dama ba mutum ne yake kawo kansa ba sune suke kawo mutum cikin sigar yaudara, shi yasa yanzu da basa cikin hayyacinsu asibitin ya zama kamar makabarta saboda shurunsa.
Halin da suka tarar da sunduƙi shine abin da ya fara girgizasu tun tsawon rayuwarsu,tabbas idan suka ce basu taba ganin abin tsoro da al'ajabi irin wannan ba ba suyi karya ba,ja da baya suka dinga yi cike da tsananin tsoron da basu taba jinsa acikin zuciyarsu ba......
500 only
8061537048
Fatima yusha'u Adam
Opay
[5/9, 3:55 PM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page52``*
Ba kome ne yasa su wannan razanar ba, sai ganin sunduƙi da suka yi cikin yanayin ban tsoro da tsananin wahala,gaba daya rabin jikinsa ci yake da wata irin bakar wuta me tsananin zafi,rabin kuma gaba daya wasu irin bakaken kunamu ne suka baibaye shi,kansa kuwa yayi wani irin girma kunnensa wasu irin kananun kwari ne suka cika kunnen suna shigewa har can cikin tsakiyar kansa,idanunsa kuwa wasu irin hawayen jini ne suke fitowa saboda tsananin azaba, dadin karin tsoro shi ne yana nan da ransa,dan har baki ya bude yana son yi musu magana amma sai ya kasa, babu abinda yake sai juya kansa saboda jikin ma ya kasa motsashi,a hankali a hankali suka dinga ja da baya saboda shi kansa kogon ba zai shigu ba saboda tsananin zafin da ya dauka,Abba Kabir ne ya bude baki cikin tsananin firgita da tashin hankali ya ce"me yake shirin faruwa ne me ya samu sunduƙi?"daga can suka ji wata murya na magana cikin zafi da takaici tana cewa,"haba jaruman duniya ya haka da saurin tsorata, to wannan ai kadan ne da ga cikin irin ikon Ubangiji wannan fa ba kome ba ne iya duniya ne fa ba aje can ba,dan haka kar ku wani damu ku ci gaba da yin kome ba kome ba ne kunji yan samari"daga haka Muryar ta dauke ɗif, cikin tashin hankali Abby ya kama hannunsu dan komawa inda suka fito sai dai kuma sihirin nasu ya ƙi sunyi sunyi amma hakan ya gagara,haka dole suka fara tafiya suna ratsa baƙin dajin da babu kome a cikinsa sai tashin hankali da ababan ban tsoro.
Yau zahida tunda ta tashi take jin wani irin firgici da tsoro a ranta ga shi jikinta har yanzu bai daina radadin ciwon ya yakushin da tasha jiya ba,dan gaba ɗaya jikinta yayi ruɗu ruɗu,zaman falo ta sauko saboda tsoron zama ita kadai da take, gashi asibitin ma ta kasa fita saboda tsoron abinda zata je ta tarar,kowa na gidan sai da yayi mamakin ganin zahida a falo, babu wanda ya tanka mata kamar yadda babu wanda ta tankawa,sai dai kowa ya fahimci tana cikin tashin hankali,daga ƙarshe kuma tunanin zuwa gidansu ta yi ko ta samu sassaucin abinda take ji idan tana kusa da mamanta,dan haka ta dauki key mota ta fita ta bawa m jauro driver akan ya Kaita,bai musa ba dan dama ba su isa musawar ba.
******
Baccin da ya daukesu ba wani me nauyi ba ne,dan shi mus ab ma ba baccin yi ba yana ganinnta samu baccin ya mike ya hau saman kujera ya bude laptop din da ya shiga rage aikin da ya cunkushe masa, daga ɓangaren aminatu kuwa farkawa ta yi cikin mamakin mafarkin da ta yi,duk da cewa ta wani bangaren ba abin mamaki a ne idan tayi la'akari da yadda ta sanya abin a ranta,
Addu'a ta yi kafin ta sanya idanunta akan mus ab da yake ta shigar da wasu muhimman aiyuka ta cikin laptop din, dafe kanta ta yi tana ɗan yatsina fuska alamun dai kan yayi mata nauyi,duk da cewa idanunsa na kan abinda yake yi amma hankalin sa tuni ya koma kan aminatu tun bude idanunta, "what happened?"Ya tambayeta idanunsa na kan wayarsa,tashi zaune ta yi tanà dan cije lips ɗinta, bata ce masa kome ba,rufe laptop din yayi kana ya miƙe a hankali ya dawo kusa da ita tàre da kama hannunta yana ɗan matsa shi ta yadda zata ji daɗi,bude idanunta da suka yi wani luuuu dasu ta yi tana kallon kyakkyawar fuskarsa me cike da kwarjini da haiba."mafarki"?ya fada yana kallon fuskarta da kyau,kwantar da kanta ta yi à kafadarsa tana ji wani irin rauni à ranta, babu abinda take bukata a yanzu sai zuwa ga abban mus' ab,duk da cewa a afarkin da ta yi ba wai ya sanar dà ita kai tsaye inda yake ba ne,to amma tana jin yadda da zuwa inda matar mafarkinta ta gaya mata da ta je,in sha Allah zata je Kuma zata dawo dashi duk da cewa bata san garin ba kuma bata taɓa zuwa ba,amma tunda garin sananne ne tasa ba zata sha wahala ba tunda Allah ne ya nufeta da zama sanadi tasan ba zai barta ta wahala ba zai dafa mata wajen cimma burinta,shafa fuskar ta da ƴayi ne yasa ta jan dogon numfashi tana dora hannunta akan nasa hannun da yake saman fuskarta,shafa cikinta ta yi tare da dan tura karamin bakinta ta ce"daddy yunwa nake ji?"bai ce komai ba yajanyeta daga jikinsa yana miƙewa tare da barin dakin gaba daya,yana fita ta janyo littafin ta ajiyesa gefe guda da niyar ko cikin dare ne zata farka ta ci gaba da karantawa ko Allah zai sa ta ci karo da abinda ya shafi babin nata rayuwar.
******
Su Abby sun sha matukar wahala kafin su fito daga cikin ƙungurmin dajin nan,zuciƴarsu ta wahala matukar wahala kuma sun ji jiki iyakar jin jiki,sai da suka gansu a cikin motar da zata kaisu cikin garin gwambe Sannan hankulansu suka fara dawowa jikkunansu,duba daya zaka yi musu kasan cewa sun ji jiki,babu wanda ya tanka ko da da karamin tari ne sai dai maganar zuci, ko wannensu da abinda yake saƙawa wanda yake ganin zai zama mafita a gare su baki ɗaya, a cikin wannan yanayin suka karasa garin inda suka umarci me motar da ya kaisu gidan gonar su,kasancewar daukosa suka yi drop.yana ajiyesu suka shige ciki daddy n zahida ne ya dawo hànnunsa dauke da bondle kudi yà mikawa me motar sannan ya koma ciki,haka mé mota yàja ya tafi yana murna yau kakarsa ta yanke saƙa,sai da su kayi wanka suka ɗan ci abinci sama sama sannan suka zauna mittin ɗin yadda zasu ɓullowa a al'amarin tunda komai ya riga ya kwaɓe dole sai dai su sake sabon shiri.