← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 57

Sashe 49

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A cikin kwana na uku da faruwar al'amarin ne Aminatu ta tashi da niyar yin wani abu guda da ya rage mata cika shi a duk cikin wasiyun da aka bata,dan haka tunda ta shi ta fada kichin tana hada kayan ciye ciye tun daga kan abinci har zuwa kan abin sha,mus ab tashin kanshi kawai ya jiyo,bai wani damu ba saboda tun da suka zama daya da aminatu bata wasa da duk abinda ya shafe shi, dan haka bashi da damuwa ta bangaren abinci dan kullum da salon girkin da yake ci a gidan, a hakan ma ɗan hankalinsu bai gama kwanciya ba ne,jinta yayi a ruwan cikinsa tana cewa daddy ka tashi ka shirya mun yi baki"cikin biyayyayyan yanayinsa ya kalleta wanda ita kuma tuni ta karbi jirginsa wato dai yana mamaki ne ammahakan bai bayyana akan fuskarsa ba bare kuma ya furtawarsa,yadda ta damesan har hakan na son SA masa danuwarta yasa ya muke tare da ita a jikinsa suka shige bathroom din,suna shuga ya hade bakinsa da nata yana mata shan yunwa dan hakika ya jigata da rashinta a tare shi, dauriya kawai yake ta yadda babu wanda zai fahimci feeling dinsa akan rashin aminatun,dakayr aminatu ta samu ta kwafi kanta ba dan komai ba sai dan muhimmancin bakin a tare da su,cikin rashin kuzarin da ya bayyana a yanayin rashin hanzarinsa suka gama shiryawa,aminatu rike kugu ta yi tana kallonsa kafin ta kai masa kyakkyawar sumba da ta zo masa a bazata tana cewa kayi kyau yariman aminatu"daga haka ta kama hannunsa suka fice daga dakin.

Suna fitowa falon yaja ya tsaya cak yana kallon mutumin da hotonsa ba zai taba dacewa a cikin kwakwalwarsa ba,mahaifinsa farincikinsa Alhaji sulaiman,zaune cikin kyakkyawar shiga ta kamala da lafiya me kyau duk da cewa kana kallonsa zaka ga tsananin ramar da ta bayyana a jikinsa,a hankali ya maida kallonsa kan aminatu da take ta zabga murmushi me dauke da wani irin zallar farinciki, dage masa gira ta yi kana ta hade hannuwanta waje daya tana cewa sorry yariman aminatu kaina bisa wuya na so yin bazata da kyauta Mafi daraja ne a cikin rayuwarka,hannunsa ta kama ta karasa dashi gaban Abba sule sannan taja gefe tana kallon yanayinsu da ba zai iya fasaltuwa ba,mus ab ksa cewa komai yayi baya ga wata irin hadamammiyar runguma wadda ke cike da zumudi da ya kaiwa abban nasa, mus ab jarumi ne da wiya kaga abinda zai shi kuka dan haka yanzu ma bai bari ya zubda hawayensa gaban yara ba, tunda har bai zubda hawaye ba lokacin da yake karanta labarinsu me cike da rudani ba to tabbas ganin mahaifinsa a gabansa ba zai sa ya zubdq hawaye ba,duk da cewa koda yayi to ba komai ba ne sai na zallar farinciki, hankali anita da Ahmad suka sulale suka bar falon aminatu na shirin ficewa taji Abba ya kira sunanta, wamda hakan yasa ta tako a hankali ta dawo gabansu,kallonta mus ab kawai yake yi ya rasa ta inda zai fara nuna mata godiyarsa da kaunarsa a gare ta,ga kuma.tambayiyin da suke cunkushe a kansa na yadda a kayi duk haka ta faru ba tare da saninsa ba,tsaf aminatu ta karanci zuciyar jaruminta dan haka sai ta kuma.hade hannunta tana mai karya kanta kafin cikin taushin muryarta da ya ji kamar an kara mata zaki ta ce.

"Dan Allah Daddy kayi hakuri wallahi tausayinka nake ji shi yasa na yi hakan ba tare da saninka ba,bana son damuwarka saboda halin da ka tsinci rayuwarka a ciki"shiru bai ce komai ba yasa ta ci gaba da cewa,tun ranar da muka gama karanta littafin nan na kuma yin mafarki da Abba, kuma acikin mafarkin ya sanar dani garin da yake wato garin Kano,na fara tunanin sanar da kai kenan sai bafulatanar baffana ta bayyana a gareni cikin kyakkyawan yanayi da suffa irin ta dattijan mutane,ban razana da ganinta ba kuma hakan baya rasa na saba da yanayin da tazo min acikinsa, a lokacin ta kwantar min da hankali ta ce mun kar na fada maka kuma duk abinda su Abby suka umarce mu da yi mu yi musu kai tsaye ita zata taimaka mana kuma in sha Allah sai su Abby sun girbi abinda suka shuka,ta gaya min cewa da kanta zata dauko Abba ba tare da wata cutarwa ba,na gamsu da abinda ta gaya min dan haka na bata kwarin gwiwa ta hanyar saka yarda ta a kanta, washe gari ta dawo min da kyakkyawan labari akan ta dauko Abba ta kuma kaisa inda ya dace wato ta barsa a hannun a nita saboda ya samu kyakkyawar kulawa, daga nan ne kuma ta shirya mana duk abinda take son mu yi akansu Abby da zahida,Abba sule da Ahmad da kuma Anita duk a matsayin matattu suke a idon su Abby dan haka da su za mu yi amfani wajen sa su Abby su gayawa duniya abinda suke aikatawa, ni ban san komai akan Anita da dan ladi ba kuma ban san alakarka da su ba,bafulata ce ta haɗani da su tarw da sanar da ni komai akansu da labarinsu,kuma a wajen su na san kai br ne,wannan dalilin shine yasa zaka ga ina yawan yin waya a boye,kuma ina yin video call da Abba,duk abinda mu ka yi mun yisa ne domin sauran rayukan da basu ji ba basu gani ba,amma a yanzu haka tuni muka daina razanasu saboda mu fahimci cewa hakkin mutanen da suka dauka da kuma hakkin ran da suka dauka ya fara bibiyar rayuwarsu dan gaba dayansu babu wanda yake cikin natsuwa",shiru ta yi tana kallon fuskar mus ab da yake yi mata wani irin kallo me kumshe da sakonni iri daban daban,Abba ne yayi gyaran murya tare da cewa "Allah yayi muku albarka mus ab kaima naji duk irin gwagwarmayar da kayi da rayuwar aminatu Allah ya shirya mu ya gyara mana bayanmu,yasa al umma su amfana da darasin da yake cikin rayuwarmu"Amin suka amsa.

Daidai lokacin Anita da Ahmad suka dawo falon,addu'a Abba yayi musu doguwa Sannan suka shafa,dubansu yayi yana cewa to a taimaka a karasa lada akaini wajen zinariyata,dariya su kayi gana daya har mus ab sai da ya murmusa,kanne masa ido aminatu ta yi tare da yin solut dinsa kana ta yiwa hannunta kiss ta hura masa,tashi Abba yayi yana cewa mu wuce kar a samu tsaiko kuma kun samu ku huta gaba daya dan naga kuna neman mantawa dani a wajen".dariya suka kuma yi daga haka kuma suna rankaya a mota suka nufi estate din mus ab.....

Zahra✍🏽
[5/16, 2:32 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page59``*

Anne na zaune ita kadai abin duniya ya isheta saboda gaba daya gidan ya hargitse, na farko dai halin da danta ya shiga ga kuma na zahida da suke kamanceceniya,sai kuma Nana da har yanzu bata san inda take ba,ga isma shima da baya nan ko wayarsa ta kira baya shiga,a wajen suhaima kawai take samun sauki, itama suhaiman bata san me yake faruwa ba, dan mus ab tuni yayi mata biza ita da Khalid suka bi mijinta Faransa inda yake aiki, shi kuma Khalid aka nema masa makaranta a kasar Dubai, kwanansu biyu a Faransa Khalid din ya wuce makaranta bayan ya samu yayi waya da masoyansa baddonsa da kuma nanansa,Mahaifiyarsa kuwa ko tunaninta baya yi,sai lokaci lokaci abinka da uwa ko wace irin ce akwai soyayyarta a cikin zuciyar danta,mus ab yayi haka ne saboda baya son Suhaima da Khalid su san abinda yake faruwa, Khalid kuwa cikin farin ciki uncle sule ya taresa a Dubai daga nan kai tsaye makarantar su ya wuce da shi, inda anan zai yi karatunsa tun daga kan haddarsa ta alkur ani har zuwa bokonsa,karatun addini kuwa sai inda Allah yayi zai tsaya domin wannan shine burin mus ab yaransa su tashi da ilmin sanin Allah da duk wani hukunci da Ubangiji ya tanadarwa mai barinsa,wanda hakan shi kadai ne zai taimaki mutum wajen kare kansa daga sabawa ubangiji.
Chapter 49 · 0% Book details