← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 57

Sashe 51

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka sosai zahida take yi, kafin ta ce"larai tabbas na tafka babban kuskure a rayuwata wanda kuma har da rashin ilmin sanin Allah da yadda zan bauta masa,da ace ina da ilmi da nasan zan dinga gudun aikata wasu abubuwan ko kuma idan na tuna da lahira nadama ta dinga zuwarmin,nifa gaba daya bana tunawa da mutuwa saboda ban san irin azabar da Allah ya tanadawa masu irin halinmu ba, wallahi rashin ilmin addini masifa ce, rashin iyaye na gari ma masifa,larai nifa abinda na aikata har da kisan kawuna ba daya ba ba biyu ba duk dan saboda neman duniya da arzikin da sai yanzu nasan cewa bani ce zan yiwa kaina ba,dan duk inda nakai ga nemana idan Allah bai sako ni cikin jerin hamshakan masu kudi ba ban isa na zama ba,yanzu gashi ina ganin sakamakon abinda na aikata wai ma a hakan a duniya ne,wayyo me zan gani kenan a lahira ?"anne da jikinta yayi mugun sanyi ta dafa zahida tare da cewa Allah gafururrahim ne ki tuba ki koma makaranta ki nemi ilmin addini ki ci gaba da istigfar Allah zai dubeki"cikin kuka saboda ta kuma.cewa wayyo ann3 lokaci yakure min baku ga nasarar da nake ciki ba ne,a rediyo fa lokacin ina zaman hostel wata calasmate dina naji tana jin wa azi a wayarta, akan cewa Ubangiji baya yafe hakkin wani akan wani,a lokacin har fada sai da mu kayi da ita akan ta saka min wa azi,to anne ta yaya kuke ganin Allah zai yafe min hakkin dubban ran mutanen da na dauka ,bayan a yanzu ma hakkin nasu ne yake neman kasheni"?shiru su kayi gaba dayansu suna jimamin wannan rayuwa.

Sallama suka ji daga can kasa,laraice ta mike ta sauka dan dubawa,larai ta yi farin cikin ganin bakin sai dai kuma razana da ganin ubangidanta Alhaji sulaiman Ja'afar, da gudu ta koma sama ta janyo Anne har zahida da take cikin tashin hankali,dan ita yanzu ko zama ita kadai bata son yi.

Da sauri Abba sule ya rike anne da take neman faduwa,idamunta gaba daya a waje,ganin ya rike ta yasa ta fara nustuwa duk da cewa tana cikin matukar firgici na ganinsa,"sule baka mutu ba kenan ko dai nima na fara yin gane ganen da su zahida ke yi?"zaunar da ita yayi akan kujera yana cewa nine Anne ban mutu ba Allah yayi da sauran kwanaki a gaba".

"Ƙarya ne ka mutu kai fatalwa ne, kuma ko da kake fatalwa ba zan kyale ka ba sai na kasheka,kai bari na fada maka sule ko da zan kashe ka sau dari ka dawo sau dari to sai na kuma kashe ka sau dari,ba kai ba har sauran fatalwun da suke binmu duk sai mun kara kashe su ko Kabiru "Abby ya fada tana kallon abba Kabir da jikinsa ya shiga wata irin tsuma, dama gaba daya a firgice suke dan ga sunan ne dai su ba masu hankali ba su kuma ba masu Lafiya.

Gaba daya duka mutanen da suke cikin falon suka juya suna kallonsa,daidai nan kuma suka ji murya daga cikin television din da take kunne tana hasko shirye shiryenta,ta hasko Daddy Garba dake kan gadon asibitinsu na gjk a jigace a kuma firgice yana cewa,dole ce tasa na nemeku domin sanar da duniya halin da muke ciki, saboda ba mu sani ba ko yin hakan zaisa mu samu sassaucin halin da muke ciki sannan mu samu wasu daga cikin mutanen da muka cuta da suke raye su gafarta mana.....rairai ya fara bada tarihinsu kamar dai yadda ku ka ji daga bakin aminatu da mus ab lokacin da suke karanta littafin sirrin su Abby.....

Zahra✍️

Ar u ready to payment

8064537048 opay

Fatima yusha u Adam

Decomment is 1k
[5/17, 4:33 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page60``*

Lokaci daya aka shiga kallon kallo a falon,kafin kuma su tsinkayi Muryar zahida tana cewa"wallahi Jamil da ka kasance ubana gwara mutuwata, wallahi tur da halinka,yanzu dama saboda abin duniya zaka iya sallama jininka?kaico kaico, ban dace ba, wallahi gwara nazo a shegiya mara uba da na zo a yarka"ta fada tana rushewa da wani azababben kukan da ya firgita aminatu itama ta rushe da kukan, cikin zafin nama mus ab ya kamata tare da sanyata a jikinsa yana jijjigata da yi mata busa a kunne.

Cikin kuka anne ta ce"tabbas zahida kin yi gaskiya baki dacen uba ba Ni kuma ban yi dacen ƊA ba,tun yana yaro yake sanya mu magana haka mahaifinsa ya mutu da bakincikinsa,ban sani ba wannan ko lefinmu ne ko kuma jarabawa ce?Ni dai nasan cewa munyi iya kokarin mu wajen nunawa jamilu daidai sai dai kuma hakan bata samu ba saboda Ubangiji ya sanya mana shi a matsayin jarrabawarmu, Allah mun gode maka Allah ka bamu ikon cinye jarrabawowinmu na duniya"rungumeta Nana ta yi tana bata baki yayin da kowa yayi jugum jugum yana kallon su Abby da har yanzu idanunsu suke kan tv suna ganin yadda mutane suka yanyame asibitin daga masu jifa sai masu kokarin bankawa asibitin wuta,jin kowa yayi shuru sai kukan anne da na zahida da ya karade falon yasa abby ya juyo yana fuskantar su,kana ya bude baki ya fara magana,kamar haka, "kun gama ?nace kun gama?"ya kuma tambaya cikin tsawa yana zazzare idonsa, babu wanda ya tanka masa, dan haka ya ci gaba da cewa "sule wai ma ya a kayi ka kubuta daga mutuwa dan yadda fuskarka ta koma awannan lukacin ko ka rayu sai dai canja maka fuska dan dai wannan ta tashi daga aiki,ka fara fada min abinda ya faru kafin na fara tunanin ta yadda zan ɓullo da al'amarin dan wallahi ba zan taba barin dukiyata ta salwanta ba akan wani banzan shirmenku ko da zan yi yawo tsirara sai na tabbatar da na kare dukiyata "Abba Kabir ne ya tari nunfashinsa da cewa "A'a Jamil ya isa haka mu bari haka iya ishara mun ganta zuwa yanzu ya kamata mu nemi yafiyar wanda muka zalunta ta bakin Garba, Ni dama tun da al'amuran mu suka fara rikicewa na fara shiga babin nadama dan dai na rasa goyon baya daga gare ka ne dan na tabbata idan na ce maka na yi nadama zaka iya kasheni"

Mus ab ne ya dubi Abba sule ya ce"Abba ko zamu bar gidan nan ne kaina ya fara ciwo ga Aminatu tana cikin kidima saboda hatsaniya?"cikin sauri anne ta ce "a'a mus ab ya kamata ya fara fada mana abinda ya faru anan daga nan sai ku tafi tunda nima zan so na ji"ta fada cikin karaya dan tasan tafiya za su yi su barta a gidan daga ita sai zahida,gyaran murya Abba yayi sannan ya fara magana cikin nutsuwa.

****

Lokacin da accident din ya faru Allah yafitar da Ni daga cikin motar saboda tsallan da katantanwar da motar ta din ga yi damu, ema driverna shine ya mutu ba Ni ba kuma shi kuka yiwa wanka,kuma na tabbata da Asma'u ta ga gawar zata shaida ba Ni ba ne.lokacin da motar ta yi watsi da Ni ban fada ko ina ba sai cikin wani rami, kaina ne ya bugu jikin dutsen ramin wanda hakan yayi sanadin bacewar tunanina ma ana dai na zama tuburarran mahaukaci,ba zan iya fada muku rayuwar da na yi cikin rayuwar hauka ba saboda bana cikin hankali na amma kowa yasan cewa rayuwar mahaukaci ba rayuwa ce me kyau ba,saboda rayuwa ce ta babu ruwana da sanin wane irin abinci ya kamata naci?da abinda Yakamata nasha ,babu ruwan mahaukaci da wanka, wajen kwana ba'a batunsa dan duk inda ya samu bacci yake koda kuwa a cikin kwatami ne,duka mahaukaci babu ruwansa da wannan, ni dai ban tashi tsintar kaina ba sai a cikin garin Kano kuma tun daga lokacin da na fuskanci halin da nake ciki na fara mafarki da wata yarinya da kamar ana min nuni da cewa ita ce zata taimakeni,bana jin a raina zan koma gida da kaina sabida ban san ta ina zan fara ba, domin tun dawowata cikin hankalina na fuskanci irin rayuwar da na yi da mutane dan haka nasan ko da na nuna na dawo hankalin babu wanda zai yarda Saboda na riga na zama a bin kyama cikin mutanen da na yi shekaru sama da talatin a cikinsu,dan haka sai kawai na ci gaba da rayuwata a haka har zuwa lokacin da bafulatar aminatu ta bayyana a gareni da siffar aminatu,ko da zuwanta gare ni ban firgita ba saboda ban yi zaton ba mutum ba ce.

Bamu baro Kano ba har sai da ta tabbatar ta Kaini asibiti anyi min texts na kwayoyin cututtukan zamani wanda kuma cikin kiyayewar Ubangiji ba'a samu wasu cututtuka masu daga hankali ba,baya ga maleria olsa da kuma matsalar fata wadda kazanta ta haifar min,daga nan na karbi magani da kulawa ta kwana ɗaya, sannan mu ka bar Kano,to a nan dinma ta sanar da ni duk abinda yake faruwa dan haka ta umarce ni da na zauna na huta na kuma samun lafiya da qarfi in yaso sai mu koma gida dan tafi son ahlina su ganni cikin kyakkyawar kama(ya boye musu tsotar da su abby da suka yi a gidan gona da sauran gurare).
Chapter 51 · 0% Book details