Sashe 33
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A can bangaren sunduƙi shima ba a barshi a baya ba,dan lokaci daya kogonsa ya dauki wani irin tururi na tsananin zafin da zai iya kona fatar jiki,cikin gigita ya miƙe daga kan buzun tsafinsa da yake ta gwagwarmaya da aminatu da mus ab, da farko ya fara cin galaba akansu amma lokaci daya yaji komai ya tsaya cak, yana kokarin sake wasu dabarunne, wannan masifar ta rufto , miƙewa tsaye yayi tare da ɗaukar sandar tsafinsa ya haska wani bangare daga cikin kogon inda a take anan su Abby da tashin hankalin da suke ciki suka bayyana,wani irin kara da kururuwa sunduƙi wani irin hayakinna fita wa daga bakinsa tare da wani shegen wari da ya cika gurin, ya ce "kun kashe mu me yasa kuka bari su ka bude littafin nan,to yanzu fa sai yadda rayuwa ta yi damu domin masifun da muka fara shiga ba zasu tsaya ba har sai sun gama karanta shafukan SULAIMAN JA'AFAR LAMIƊO,daga nan ne zamu samu damar kuma wani kokari akansu amma muddin muka barsu suka bude wani shafin to ku tabbatar da cewa bala un da zaku gani sunfi wanda kuka fara gani da wanda zaku gani nan gaba"
Yadda sunduƙi yake kallonsu ta cikin madubin tsafinsa yake musu magana haka suma suke kallonsa da sauraron abinda yake cewa, Abba Kabir cikin tsananin tashin hankali ya ce"yanzu sunduƙi me ye abinyi ya zamu yi mu fita daga wannan masifar da muke ciki?wai ka duk me ya janyo mana wannan tabarbarewar al amuran lokaci daya ?anya kuwa babu sa hannun maƙiya?"ya karasa fada kamar zai rushe da kuka, "babu abinda zan iya yi muku ayanzu ai na fada muku tun ba yau ba,idan bala in ya tashi har dani zai hada dan haka ku nemo hanyar fidda kanku"da sauri Abby ya tari numfashinsa da cewa "sunduƙi kataimaka mana mu gida daga cikin motar nan wallahi masifun da yake cikin motar nan bai kai wanda zamu tarrar a waje ba,har yanzu fa kukan mutane da ihunsu muke ji tamkar dodon kunnenmu zai mutu sunduƙi ka taimaka mana kayi mana rai ba dan halinmu ba"Abby ya karasa da hade hannunsa guri daya alamun roko,sunduƙi ya ce"shike nan zan taimaka muku duk da cewa nima ban kashe tawa masifarba",daga haka suka daina ganinsa, alokacinne kuma suka ji motar ta yi wani irin jan burki,hade da watso su waje kamar wasu kayan wanki, aiko suka ce kafa me naci ban baki ba, kai kace yan tseran gudu ne basu tsaya a ko ina ba sai a dakunansu ko wanne yana tunanin abinda zai kuma biyowa baya.
*****
Zahida kuwa tana tsaka da tunanin hanyar dawo da mus ab hannunta wani irin bacci ya fizgeta me karfi,wanda hakan yasa ta bingire a kasan dakinta tana yinsa babu ji babu gani,kamar a mafarji kamar kuma a gaske ganin kanta kawai ta yi a cikin wasu irin kayoyi suna tsikarinta,daga gefe kuma mutane ne yara da manya suke ya kudi fatar jikinta suna ci tare da cewa sai kin biya mu hakkinku azzaluma me fuska biyu ba za mu taba barin ki ki huta ba saboda kin kashe mu ta hanyar da bai dace ba,kin zama sanadin mutuwarmu ta hanyar da bai dace ba,wasunmu marayu ne wasunmu talakawa ne masu neman cin na yau,wasunmu muskinaine da masu raunin zuciya, amma duk baki duba haka ba kika kashe mu ta hanyar cire mana abinda Allah ya haliccemu dashi saboda neman duniya,to yanzu ga duniyar nan kin sameta kuma kina kan samu se ki zauna zaman jiran duniya tunda ku babu lissafin mutuwa a Yarenku"a matukar firgice ta tashi ta haɗa wata uwar zufa, tsananin zafin da ya ratsa ta ne yasa ta yi saurin duban jikinta,ga tsananin mamakinta sai taga gaba daya fatar jikinta ta kuje wani wajen ya kwashe ga shatin farce Nan ga kuma na kayoyin da suka dinga tsikarinta nan,da gudu ta mike ta shige bathroom tana kuka tana taba fuskarta da lokaci daya ta sauya kama.
****
Sosai suka maida hankalinsu kan rubutun da yake cikin shafin kafin su fara karanta tare da kallon abinda yake kunshe dashi wanda suke ganinsa tamkar a gabansu a kayi.
TSANGAYAR DAMATURU..
Yaro ne ɗan kimanin shekara goma sha biyu yake tafiya hannunsa rike da roba irin ta almajirai,shidinma kana duban kayan jikinsa zaka tabbatar da cewa almajiri ne,kacibus suka yi da wani yaro da bai fi sa an sa ba yana zaune daga gefen kwalbatin babbar hanyar da zata aidakai TSANGAYAR malam auwal yana ta kuka har da tumurmusar kafafunsa,cikin sauri almajirin ya karasa inda yaron yake tare da dora hannunsa akan kafadarsa yana cewa,"waye ya dakeka kake kuka"?ture hannunsa yaron yayi daga kan kafadarsa yana mai hadiye kukansa,rambayarsa almajirin ya kuma yi yana kokarin zama a kusa da yaron,amma ga mamakinsa sai yaga yaron yayi saurin miƙewa yana toshe hancinsa tare da yatsina fuska har da kokarin yin amai,cike da mamaki almajirin ya ke kallon yaron, can kuma ya tsinkayi Muryar yaron yana cewa "kai fa almajiri ne dan me yasa zaka taba Ni har ma ka dinga kokarin zama a kusa dani bayan hakan yana nufin kana son daidaita kanka dani ne"da sauri almajirin ya dubi jikinsa kafin cikin sakin fuska ya ce,"ka yi hakuri na manta ganin kana kuka ne yasa na manta cewa Ni almajirin gidanku ne"yaron gyada kai yayi yana wani hura hanci kafin ya kuma cewa da almajirin, Anne ce ta aikeni na zubda kudin shi yasa nake kuka ko kana da maganin kukan nawa ne talakan almajiri?"girgiza kai almajirin yayi tare da cewa "yau ban samu kudi ba saboda bana jin dadi ban je dako ba"wucewa yaron yayi gaba yana cewa "babu ruwana kai zaka biya Anne kudinta tunda kaine ka jawo aka aikeni har na yar da kudin"almajirin bai ce komaiba sai bin bayansa da yayi ba tare da yayi kokarin jerawa dashi ba.
Suna shiga zauren gidan suka ci karo da Kabiru dan makotansu Jamil yana ta irga kudi yan ashirin ashirin, birki jamilu yayi yana cewa"Kabiru a ina ka samo kudi haka da yawa?"dariya Kabir yayi yana cewa ai na innarmu ne da take sawa a banki na dauko zan je Nima na ji yadda ya'yan masu kuɗi suke ji"tsaki Kabir yayi tare da warce kudin yana cewa"aikin banza wadan nan yan kudadenne zasu yi maka maganin damuwarka to ka ma sake lissafi"daga haka ya cusa kudin a aljihunsa yayi gaba, tura baki Kabiru yayi tare da har SULAIMAN almajiri kamar shine yayi masa lefin,girgiza kai kawai suleman yayi kana ya shige gidan shima.yana shiga ya samu anne na yiwa Jamil fadan dadewar aiken da yaje yayi kuma bai samo abinda aka aikeshin ba,saboda yana shigowa kudin da ya karba a hannun kabiru ya mika mata,tana ganin sule ta washe baki tana cewa a'a sule ka dawo daga dakin ne yaro dan albarka ke nan babu ruwansa da kayan kowa sai dai ya nemi halalinsa"take jamilu ya hade fuska yana cin magani dan yasan da shi anne take wannan habaicin,feee ya fi ce daga gidan yana maganganu ƙasa ƙasa.
Sule kuwa cikin ladabi ya ce "anne ai yau banje dakon ba saboda bana jin dadi"da sauri Anne ta kamo hannunsa tana cewa sannu dan albarka me ya sameka? bari na kawo maka magani kasha kaji,ta karasa fada tana shiga dakinta,binta da kallo sule yayi yana jin daɗin irin kulawar da iyayen gidansa suke bashi, gashi dai babu abinda ya haɗa su aike kawai yake yi musu suka jawo shi a jiki suka mai dashi tamkar dansu,shi yasa yake sonsu yake kuma kayuatta musu,yaron su daya tal shine Jamil,sai dai Jamil baya jin magana ko kadan kullum fama suke dashi ko makaranta yaki zuwa, samun sule da suka yi yasasuka rabu dashi tare da yi masa addu'ar fatan shiriya,
Sule dan asalin garin Gombe ne cikin wani kauyen Fulani me suna bingel,tun yana shekara uku iyayensa suka mutu sai ya koma wajen baffansa da zama,saboda tsana da tsangwama da matar baffansa take nuna masa yasa baffansa ya tattara shi ya kaisa DAMATURU karatun almajiranci,sule yaro ne me nutsuwa da hankali babu ruwan shi da rawar kai irin ta almajirai shi yasa yake da shiga rai da kuma farin jini,ko a wajen malaminsu yana da alfarma, yaro ne me hazaka da neman nakansa dan shi ko bara bai yarda yayi a bashi ba sai dai ya fita yayi aikin karfi ya samu abinda zai sawa bakinsa na salati,a halin yanzu har makarantar boko yake zuwa saboda abin yana burgeshi da bashi sha,awa gashi abin nasa yayi albarka dan yanzu yana ajin daga ke se secondry, shi kuma Jamil yaki karatun babu abinda ya iya sai janyo magana da yan sace sace saboda shi yana da babban buri a zuciyarsa , sosai ya tsani sule da dabi'unsa,shi yasa basa shiri.
Gidansu Kabir yana jikin gidansu Jamil ta hagu shi kuma gidan su Garba yana ta dama,gaba dayansu ukun abokaine da hali da rayuwa suka zo daya shi yasa suke jone suke matukar son junansu.