Sashe 39
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun tana ja da baya har ta kai ƙarshen bango wanda hakan yasa dole ta tsaya tana kallonsa, yana ƙarasowa inda take ya sa hannu ya shaƙe wuyanta yana cewa "tsawon lokaci ina ta bulayin neman inda sule ya kai dukiyarsa ashe ina tare da me dukiyar hannu ban sani ba,ashe tana wajenki munafuka macuciya ,wato kin gwammace ki bawa wani can a duniya ya adana miki dukiyar akan ki bani na juya har zuwa lokacin da mus ab zai buƙaci kayansa,yadda ya shakure wuyanta yasa ta dinga kici_kicin ƙwacewa numfashi ta na fizga tamkar zata mace,magana ta ke son yi amma ta gagara,sai da yaga tana neman mutuwa sannan ya yi wani irin watsi da ita tamkar yayi watsi da shara,sai da goshinta ya fashe amma duk da haka bai raga mata ba ya kuma binta zai taka ta ƙafarsa da take sanye cikin wani arnen coversue, sai kuma ya dakata kamar wanda ya tuna wani abu,hannu yasa ya dagota ta mike tsaye jikinta har bari yake saboda tsoronsa,hijabin Sallah ya dauka ya zura mata sannan ya nuna mata hanya ba tare da ya damu da jinin da yake zuba daga goshinta ba,a hankali take takawa kamar wadda kwai ya fashewa a ciki,bai fita da ita ta asalin kofar falon ba,sai ta can wata kofa da basu taba sanin da ita a cikin gidan ba,a bin mamaki baya karewa dan wata kofar ce Jamil ya kuma budewa wadda zata kaisu har waje ba tare da kowa y gansu ba,kai tsaye ya je fata cikin motar da ya ajiye a wajen tunda babu wanda yasan y dawo gidan saboda tanan ya shiga gidan kuma suka fito tanan,a hankali yaja motar suka bar anguwar gaba ɗaya,Nana bata san me Jamil yake nufi da ita ba, dan bata taɓa tsammanin duk iskancin Jamil zai iya sace ta dan cimma burin sa ba.
Sai da ya tsaya ya sanya kyalle ya rufe idanunta ya daure hannunta sannan ya ci gaba da tafiya,ji ta yi kawai sun tsaya daga nan sai ji ta yi ya janyo ta kamar wata dabbar da za a yanka,bata fahimci komai ba baya ga ƙuntataccen dakin da ya watsata a ciki, alamun tsugunnawarsa ta ji a gabanta sai Kuma sautin Muryarsa da ta ji yana cewa,"zaki zauna anan har zuwa tsawon lokacin da zaki fanshi kanki ta hanya guda biyu,na farko zaki sa danki ya bani duka hujjojin da suke hannunsa kama da daga kan takardu mutane camaras dan nadan ba za a rasa wata a wajen sa ba bayan ta hannun ɗan ladi ba, ina so duk kankantar sheda ta dawo hannunna, sannan ke kuma ki bani duka abinda sule ya baki wanda ya danganci manyan gidaje gonaye da filaye da kuma tsabar kuɗin da ya bari duk ki bani su a hannuna,ni kuma zan barki keda danki, surukarki kuma zai bani ita ta zauna a hannuna har zuwa lokacin da wanda ubanta ya dankawa dukiyarta a hannunsa ya bayyana sai na dawo muku da ita dan ni babu ruwana aurensa da ita,bukatata kawai dukiya daga nan zan fita daga rayuwarku gaba daya,amma muddin kuka ce zaku wulaƙanta ni ta hanyar hanani arziki wallahi sai na kashe ku gaba dayanku yankan rago zan yi muku ba tare da tausayi ko imani ba"daga haka ya miƙe ya cire mata daurin da yayiwa fuskanta da bakinta da hannunta ya juya zai fita amma sai yaji Nana ta kyalkyale da dariya irin ta tura haushin nan,dakatawa yayi tare da juyawa yana kallonta ta cikin dan hasken da ya taso ta wajen dakin,sosai yake mamakin dariyartata kafin kuma ya tsinkayi muryarta tana cewa"jamilu ai kayi sake wallahi ka yi sake,sai yanzu na gane nufinka na kawo mana aminatu cikin gidan ashe kai da mummunan nufinka akansu ita da kakarta wato saboda kakar bata da amfani a wajenku shi yasa ku ka fara kokarin kasheta ta hanyar cire mata zuciya sai kuma Allah ya tsareta domin bai nufi mutuwarta a wannan lokacin ba"wani makirin murmushi ta yi sannan ta dora da cewa, "jamilu ba kanka ka kawowa aminatu ba ,mus ab ka kawowa aminatu, shin baka yi tunanin ta yadda aka yi aminatu ta zama matar mus ab ba?ko lokacin da ka ji baka yi tunanin mus ab zai iya kasancewa shi ne dan birnin aminatu da ta yadda ta shigo birni saboda ta neme shi ba?girgiza kai ta yi tana cewa "Wallahi jamilu kai sakarai ne kwakwalwar ka sam bata ja, to idan baka sani ba daga yau ka sani mus ab shine mijin da uban aminatu ya daura mata aure da shi a can riga tun tana yar shekara bakwai zuwa takwas, kuma shine wanda ya damkawa ragamar dukiyar aminatu idan......marin da ya dalla mata hagu da dama shine ya katse maganarta, rike fuskarta ta yi tana kallonsa ba tare da tsoro ko nadama ba,kafin ta ce "wallahi jamilu idan ka bari ka mutu da wannan babban zunubin akanka ka shiga uku, jamilu ka tuba tun kafin lokaci ya ƙure maka Allah gafururrahim ne zai yafe maka nasa lefin da ka yi masa,daga nan sai ka ji da hakkin rai da ka dauka wannan zai sa ka samu rangwame daga azabar Ubangiji domin shi tuba nasuhan yana da ladansa na musamman da Ubangiji ya tanadarwa me yinsa,shi kadai ya isa ya rage maka zunubin hakkin ran da ka ɗauka,ka ga ko a lahira sun ji kanka sun yafe maka,.amma in dai har baka tuba ba Wallahi ina tausaya maka daga nan duniya har zuwa lahira...."dan ubanki idan ke ki ke bada aljanna sai ki hanani"ya fada yana kai mata hari da ƙafa saboda hankalinsa ya kuma tashi babu abinda yake sai zufa bai taba zaton ko a mafarki zai kasance mus ab shine wanda suke neman dukiyar aminatu a hannunsa ba.
Nana ce ta katse masa tunaninsa ta hanyar cewa "jamilu bani da wuta kuma bani da aljanna sannan Ubangijin da ya halicci samaniya da kasa ya halicci duniya da abinda yake cikinta shi kaɗai yasan ɗan wuta da dan aljanna, Ni dai kawai nasiha nake maka kamar yadda Ubangiji ya umarce mu da yi idan kuma abin ya fi karfinmu sai mu kawar da idanunmu muyi addu'a"cikin wani irin zafin da yake taso masa tun daga kasan zuciyarsa ya ce"tunda kin san da haka ki min shiru,dan baki sani ba sai ki ga ni na shiga aljannar ke kina can kasan wuta "wa'iya zubillah ta fada tana runtse idanunta kafin ta budesu cikin yanayin jarumta ta ce "dama ku yan adam kuna amfani da fadar Allah wajen saɓa masa, kar fa kayi amfani da wannan hadisin da yake cewa (saura taƙi kaɗan ka shiga wuta sai ka kasance kayi aiki irin na yan aljanna sai ka shigeta,kuma saura taƙi kaɗan ka shiga aljanna sai ka kasance ka yi aiki irin na yan wuta sai ka shigeta Allah ya yi mana tsari da ita)kar ka yi duba da haka ka ce zaka sabawa Ubangiji saboda kana taƙamar zai yafe maka, to idan ya kasance mutuwar ta yi maka hanzari fa? kasan fa mutuwa baazata ce babu wanda yasan lokacin da zata daukesa"wani uban tsaki yayi sannan ya fice daga dakin tare da rufe ta, take ta daina ganin haske ko ƙanƙani ko tafin hannunta bata gani,saka kanta ta yi cikin gwiwoyinta tana addu'ar fita daga tsananin musiba,innalillahi wa inna ilaihi raji un, la ila ha illahuwar azimul halim,sai kuma ta ci gaba da karanta Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan wa anta taj'alal huzna Iza ma shi'ita sahlahu.duk tsananin masifar da mutum ya shiga ya karanta wannan addu'o in in Sha Allah Allah zai kawo masa mafita da sauki cikin lamarinsa.
Tunda ya bar dakin ya shiga Mota yayi shuru ya kasa jan motar,saboda maganar Nana ta shigesa kai shi fa ko maganar sanin mus ab ne br unknown bai daga masa hankali irin sanin da yayi cewa shine mutumin da ya jima yana nema ba,dafe kansa yayi kafin yaja motar da gudu kai tsaye gidan ya koma, ko securitys din barka da zuwa kawai suka dinga yi masa, duk atunaninsu lokacin ya dawo gidan,babu wanda ya tankawa haka ya shige gidan zuciyarsa babu dad'i,dakyar ya samu ya ya kice damuwar kan fuskarsa ya duba anne har take masa maganar halin da Nana take da bashi izinin ya duba ta ko asibiti ne suje dan taga kamar bata jin dadi"amsa mata kawai yayi sannan ya fice daga dakin, sai a lokacin ya tuna da isma da halin da yake ciki,dama shi sule karami bai damu dashi ba saboda sunan sule babba aka sa masa,dan haka tunda ya kaisa kasar Dubai karatu bai kara waiwayarsa ba,sai dai yasan mus ab yana kula dashi ta hanyar tarbiyya da abin bukata duk da cewa yanzu ya kama aiki a can dan shima bai damu da dawowar ba, shi da suhaima ne kaɗai Allah ya shirya masa su dan gaba daya halin nana ne dasu basu dauko son zuciyarsa ba,hakan yasa yafi damuwa da zahida da isma, da wannan tunanin ya haura bangarensa yana kuma laluben nomber isma ko zai dace.
********
Yau watan baffa wuro daya a ABM Hospital,idan ka gansa kamar ba shi ba ya warware yayi tsaf da shi saboda tsananin kulawar da ake yi dashi ,an gaya masa kullum akwai wanda yake zuwa yana duba lafiyarsa sai dai bai taba ganinsa ba bai san ko waye ba,amma duk da haka yana shan addu'a a bakin baffa wuro matarsa da yayansa suma suna cikin kula da gata,yau saura kwana biyu a sallame shi amma fata yake mutumin nan yazo ya ganshi ya yi masa addu'a da godiya, likitan da yake kula dashi ya sanarwa yana son ganin bawan Allah da yake kula dashi,likitan ya sanar masa zaizo amma sai a ranar da aka sallameshi.
******