← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 57

Sashe 47

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A bangaren zahida kuwa tana farkawa ficewa ta yi daga dakin, ba tare da ta damu da kallon da mutane suke Binta da shi ba,kai har ta kai ga an fara nunata da yatsa, kallon kanta ta yi a jikin wata mota me bakin glass dake fake a harabar asibitin, sai da ta rufe idanunta ganin yadda lokaci daya ta koma kamar wata mabaraciya me neman na abinci,bude idanunta ta yi tana kokarin sauke ajiyar numfashi,kit numfashin ya tsaya kwayar idanunta kuwa tamkar zasu fado kasa, kafin ta fara ja da baya da baya tana nuna saitin glass din motar da hannu, ihu ta saka tana durkushewa a wajen tare da cusa kanta cikin cinyoyinta,take mutane suka taru akanta ana tambayarta lafiya wasu ma saboda tsegumi suka zo dan kowa mamakin ganin zahidar cikin wannan yanayin yake yi.duk wanda ya taba ta turesa take yi tana nuna motar gami da cewa,"fatalwa ku taimakeni fatalwa nake gani"tsaki wani dattijo yayi yana cewa "fatalwa ba ai yanzu kuka fara ganin fatalwa tun da ku jurinku kashe mutum"dakyar wasu daga cikin likitoci da suka yi ragowa suka tayar da zahida tare da tambayarta abinda ta gani,bude idanunta da tun dasu suke a rufe ta yi tana kallon inda motar take,motar na nan kuma a rufe glass dinta yake kamar yadda ta gansa tun farko, sabanin ganin da ta yi a karo na biyu,waige ta fara yi tana cewa "Wallahi na ga anita tana kallona ta cikin motar nan"tuni aka nemo me motar ya zo ya bude aka duba cikin motar amma babu wani me kama da Anita ma bare kuma ita da kanta,dan haka sai suka dauki zahidar suka saka a mota aka nufi gida da ita, sai dai wani abin mamakin shine suna zuwa kofar gidan taga wata nefef ta faka a kofar gidan wata makociyarsu tana sauka tare da mikawa me nafef kudinsa, sai dai kuma matar na juyowa su ka yi ido hudu da anita fuskarta duk jini tana kallon zahidar cikin kunar rai,wani irin ihu zahidar ta saka tana nuna musu cikin nafef din da Anita take ciki, sai dai hallau basu ga komai ba, sauri suka yi suka kaita cikin gida suka barota ita da anne da larai suna rarashinta,larai ta ce "wai dama anita ta mutu ne kuma akan me zata dinga zuwan miki a fatalwa tunda bake kika kasheta ba?"har zahida ta bude baki zata yi magana sai kuma ta fasa tana mai girgiza kanta saboda jinsa take kamar zai rabu da kwakwalwarta.

******

Suna zuwa gida aminatu tun daga falo ta tsare mus ab da tambaya,fuskantar sa ta yi bayan ta tare kofar shiga bedroom dinsa, tana cewa dan Allah daddy ka fada min wai me yasa kasa na jewa zahida a haka, kuma me yasa ka ce musu nice me ABM ?to ma abm din na waye?"naki ne"ya bata amsa kai tsaye tare da shigar da idanunsa cikin nata,dafe kirjinta ta yi, tare da cewa"daddy ta yaya ya zama nawa naji fa ance Abm din nan suna da yawa Ni ina na ga kudin da zan iya mallakar su?"dage kansa yayi tare da nuna mata alamun ya gaji tabarsa ya huta da magana,make kafada ta yi tana mai kuma tare hanyar ta hanyar riƙe ƙugunta tana yin fadi, sannan ta ce "aradun Allah daddy banni barinka hutawa sai ka fede min buri har wutsiya"cikin rarraba kalmomin da zai fada ya ce "dukiyarki da baffa ya bani ita ce ta zama abms"ware manyan idanunta ta yi kafin ta kai masa wata dimautacciyar runguma tana cewa "wayyo ni Aminatu MATAR ƊAN BIRNI Allah ka barni da hamma mus ab dina,namiji guda a cikin miliyoyin maza,nagartaccen namiji me amana jarumi kuma gwarzon BODDO rayuwa babu kai gawa ina sonka da dukkan zuciyata ina sonka da dukkan rayuwata kai din kayi kuma na musammanne kamar yadda komai naka yake na musamman, wallahi mus ab din aminatu ba duk kai ba,daddy mus ab ya zama ƘADDARA SANADIN HASKE NA bayan KUDURAR ALLAH da ta riga ta haɗa mu,wani irin juyi ta yi ajikinsa tare da sumbatar labbansa ta na ci gaba da cewa MUS'AB dina me kyau ne jarumi ne domin jarumtarsa ta wuce ta BOYAYYIYAR RAIHAN kuma kyawunsa ya fi na hamma wazeer , shi yasa nake da yakinin cewa insha Allah zan haifa masa yarinya me kyau kamar ZAHRA YAR GIDAN YARBAWA"jan dogon hancinta yayi tare da girgiza kansa kana cikin karamin sauti me dauke da wasu irin zafafan sinadaran karya lagon jarumar mace ya ce" a'a na fiso ki haifa min me kama da AMINATU MATAR ƊAN BIRNI"daga haka ya daga ta cak bai direta a ko ina ba sai a bathroom.....

****

Gidan gona da ya fara daukar haramin manyan kusoshin masu kudi masu fada a ji da kuma yan mata hadaddu da kayan shaye shanye na musamman,duk wanda ka kalla zaka ga fuskarsa cikin farin ciki da walwala hira kawai ke tashi ta ko ina , ga kuma tattausan kida da yake tashi a hankali.

Karfe takwas na daren guri ya kuma dinkewa da jama a, babu abinda ake sai shagali,iyayen biki kam ba zan iya ce muku komai akan su ba, dan su din sun fita da ban cikin dubban mutanen da suke makare a wajen,su daddy harba tuni an shiga harka da mata abin nema ya samu,Abba Kabir kuwa kwalaben giya ne a gabansa yake ta durawa cikinsa,shi kuwa dama Abby kudi ne butinsa dan haka baya ko daya daga cikin wadannan dabi un,idan ka cire zallar rashin imani,ana tsaka da shagali wuta ta dauke gaba daya gidan take komai ya tsaya.......

Wanda bai karanta wannan littafan nawa ba zai iya tuntubata dan bayarwa akan farashi me sauki✍️

Zahra.....

8064537048 opay Fatima yusha u Adam

De comment is 1k only
[5/15, 4:54 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page58``*

"Kai me ye haka? maza kuje ku tada jen"Abby ya fada yana kokarin kunna wayarsa,duk wanda ka gani da haske a gun to wayarsa ya kunna,Garba kuwa yana can yana sharholiyarsa da mata har uku, a cewarsa yau fa sai yayi kara i,zagawa baya abby yayi da wayarsa yana mita,"me za a yi da harka da talaka daga an dauko ku kuyi aiki amma gaba daya kun lalata mana sabga, me za a yi da rashin haske" daidai lokacin da ya zo inda jen din yake yana haske wajen, cikin zafin rai ya ke cewa "au guduwa kuka yi kuna ina ne wai?"ya fada yana kara haske wajen da wayarsa amma bai ga kowa ba, tsaki yayi tare da juyowa wajen da jen din yake dan ya duba da kansa ya ga me yake damun injin, abinda ya gani ne ya haifar masa da rawar kafa hannunsa kuwa tuni ya saki wayar dake hannunsa yana haskawa mararsa kuwa wani irin daurewa ta yi, bakinsa banda karkarwa babu abinda yake yi, a hankali ya dinga juyawa har sai da ya bawa abinda ya gani zaune akan injin baya,rayawa yayi a ransa cewa shine fa me shiga daji duk duhunsa me hawa tsauni duk tsayinsa shine fa me mu amala da sunduki me sauyawa zuwa duk suffar da ya gadama kuma hakan bai taba girgiza shi ko tsorata shi ba,sai yanzu dan kawai wani mutum da ya jima da mutuwa ya zo masa a fatalwa shine zai sauya masa nishadinsa,hakan yasa shi juyawa dan kuma fuskantar sulaiman idan ma wata mutuwar yake bukata shi mai iya kara kashe shi ne a yanzu ba da bata lokaci ba,sai dai yana jiyowa yaga wayam, dan haka sai yayi dariya yana cewa da na tsorata da shike nan na bashi hanyar da zai ci gaba da bibiyata"injin ya kuma sunkuyawa zai tayar,sai kuma ya fasa ya dago kansa dan neman ma aikatan da suke da wannan alhakin,juyawa yayi daniyar barin wajen amma sai yaji kamar an rike ƙafarsa daya ta cikin kasa,kallon kasan kafafunsa yayi, bai san sanda ya kurma wani uban ihu ba, sakamakon ganin dan ladi da yayi kwance a gabansa cikin yanayin da aka turo masa shi a waya, da gudu ya fita daga wajen yana tsalle tsalle da taba kafafunsa da suka ɓaci da jini.
Chapter 47 · 0% Book details