← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 57

Sashe 25

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tamkar wanda aka jefo daga sama haka su Nana suka ga Abby ya faɗo falon tamkar wanda baya cikin hayyacinsa,kafin Nana ta yi wani batu tuni ta ji saukar mari hagu da dama Abby yana mata marin makauniya,yana yi yana wani irin huci tamkar ɓakin kumurci,"jamilu lafiyarka ƙalau kuwa?me Nana Asma'u tayi maka kake mata wannan marin na rashin imani ka zaɓe karfinka,tamkar ba mace kake duka ba?"Anne ce take magana tamkar zata kai masa duka saboda mamaki da taikaici,Nana kuwa tunda ta dafe kuncinta da hannayenta duka biyu bata kuma yin motsi ba bare ta dago ta tambayesa ba'asin marin da yake sharara mata,nuna ta yayi da yatsa tana cewa wallahi yadda kika sa ya auri wannan Aljanar yarinyar to sai kinsa ya saketa ko kuma ke na sake ki ki tafi ki bar min gidana"daga haka ya wuce sashen aminatu bagazan bagazan tamkar zai tashi sama,yana shiga dajin ya shiga birkita komai na dakin kayanta kuwa kaf sai da ya fito da su ya daga kujera da katifar gado, lokaci daya ya futarvda dakin daga hayyacinsa shima ya futa daga hayyacinsa dan ji yake a ransa da ya rasa wannan littafin gwara ace ya bayyana halinsa in yaso sai karfinsa da littafin su kwace shi,ganin bai samu komai ba yasa shi fitowa a fusace kai kace idan ya samu naman mutum zai cinyesa danye.daidai lokacin aminatu da mus ab suka shigo yana rike da hannunta goshinta zagaye da bandeji,cak ta tsaya ba tare da ta kuma daga kafarta ba, sai ƙirjinta da yake wani irin duka gangar jikinta babu abinda take sai rawa,da sauri mus ab ya juya ya kalleta saboda yadda yaji gana dyaa ƙirjinta ya dau karkarwa,waje daya yaga ta zubawa ido hakan yasa ya bi wajen da kallo inda ya zubawa Abby ido na yan sakonni sannan ya dawo da dubansa kan Nana wadda har yanzu hannunta yana biyu suna saman kuncinta,ji yayi an fizge hannun aminatu daga nasa kafin yayi wani yunkuri tuni Abby har ya kai kofar dakinta da ita inda bai yi wata wata ba ya jefata dakin shima ya shiga,kafin mus ab ya karaso tuni ya rufe ƙofar da key.

Da sauri mus ab ya juyo yana kallon Nana dan yana bukatar karin bayani akan abinda Abby yake yi duk da cewa aminatu ta yi masa wata maganar da ya kasa fahimta ,to wane littafi ne aminatu take magana akai?waye kuma mahaukacin mutumin nan da take mafarki dashi akan yana son ta taimakesa?me ye hadin mutumin da su Abby da kuma wannan littafin?tabbas shima yana bukatar littafin nan a hannunsa dan haka ba zai taba bari AMINATU ta bawa Abby littafin ba,gama wannan tunanin nasa ke da wuya ya juya cikin hanzarinsa da zafin nama ya tunkari kofar cikin shirin bude ta ko ta wace irin hanya.

A can cikin dakin kuma, kai tsaye Abby ya tunkari aminatu da idanunsa da suka juye suka koma wata kala tamkar idanun mage,cikin tsoro aminatu ta kuma ja da baya tana girgiza masa kai tare da magiyar kar ya tabata,amma ina Abby bai da wannan imanin dan haka cafka ya kaiwa wuyanta tare da shaƙeta a jikin bango yana cewa"Dan ubanki Yusuf ki dauko min wannan littafin tun kafin na zama ajalinku"kuma ki gata min ta yadda aka yi ki ka auri mus ab ba tare da sanina ba?"kakarin amai ta AMINATU take yi tana jin tamkar ranta zai fita,buga kanta yayi a bangon yana cewa dan ubanki ki fada min yaushe mus ab ya zama mijinki sannan ku fada min ta yadda aka yi jika dauko littagin da kuma inda yake yanzu idan ba haka ba ba zan kuma barinki ki shaƙi numfashi a duniya ba yanzu zan kasheki kamar yadda na kashe U....sai kuma yayi shuru yana kuma matse wuyanta a bango,hannu tasa tana son banbare hannunsa da take da tabbacin ya kuma yin mintuna a wuyanta to zai kasheta ne kamar yadda ta faɗa,gashi kuma ya hanata damar yin magana, dakyar ta samu ya sassauta rikon azabar da yayi mata yana cewa maza fada min yadda komai ya kasance ba tare da sanina ba"cikin azaba aminatu ta ce"Ni Ni Nima ban sani ba sai daga baya ban san shine ɗan birnin da baffa ya bawa aure na ba sai jiya, dan haka ban san komai ba kuma ba laifina ba ne"wani azababban mari ya sharara mata wanda har sai da taga giftin wuta ta fuskarta, sai dai Abby yana jin cewa a wannan duniya a kuma a wannan rana da wannan lokaci babu wani abun halitta da ya fishi shiga tashin hankali,wani irin watsi yayi da ita yana mai jin zuciyarsa zata fito,wai musu abunsa shine mutumin da suke nema ruwa a jallo?shine mutumin da ba da shi ba da yanzu sunnjima da shanye roman aminatu sanadinsa ne aminatuntake raye a dunya har zuwa wannan rana,ke nan duk abinda suke nema na dukiyar aminatu tana wajen mus ab?to ta yaya haka ta faru?"

Tambayoyin da bashi da mai bashi amsa yake ta yiwa kansa,ji yayi zai zauce abu goma da ashirin sun taru lokaci daya sun zo masa a matukar bazata,da wani irin huci da fusata tare da niyar kisa ya juyo kan aminatu dan atunajinsa yadda ta bashi amsar baya haka ta gaba ma zata bashi abinda ya bukata,danƙar gashin kanta yayi yana figarsa tamkar zai cizgoshi da ga ƙwaƙwalwarta tare da cewa"sanar da Ni inda kika kai min littafi idan ba haka ba zan kashe kakarki innawuro dan a halin yanzu tana hannuna"wallahi wallahi wallahi Abby ba zan baka littafin nan ba har sai na karanceshi na ga abinda yake cikinsa koda kuwa zaka kashe ni ko ka binneni da raina"hannu yasa ya kuma kifa mata marin da take jinin habo ya ɓalle mata gefen idamunta shima jini ya taru saboda tsananin maruwar da ta yi,hannu yasa zai kuma kara mata fiye da na baya yaji an yi wurgi dashi da hannun nasa gaba ɗaya,

Yana dago kansa suka yi ido hudu da mus ab tsaye ƙyam yana yi masa wani irin mugun kallo kallon ƙyama da bakin cikin kasancewarsa ubansa, hannu yasa ya ɗago aminatu tare da sata a jikinsa duk da yadda jini yake zuba ta hancinta da bakinta amma hakan baisa yaji cewa zata iya bata shi ba,janta yayi suka shige bathroom ya wanke mata fuska tare da tsayar mata da jinin,dago kanta ta yi a wahalce ta kallesa tana cewa"dan fiyayyan halitta daddy ka ɗauke ni daga gidan nan idan ba haka ba Abby da mukarrabansa zasu kasheni ba tare da na cimma burina na gano sirrinsu da sauke alƙawarin da na dauka ba,dan Allah daddy na rokeka"ta fada cikin wata irin raunanniyar muryar da ta sake karyarwa da mus ab zuciya, rungumeta kawai yayi yana kasa cewa komai kansa kuwa har wani harbawa yake yi saboda tsananin ciwon da yake yi
[5/1, 3:33 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page45``*

Abby kuwa tsananin mamakin mus ab ne ya hanasa miƙewa dan bai taba zaton cewa zai iya yi masa haka ba,wai yau shi ɗansa na cikinsa yake.turewa saboda mace,lallai da dake,ya.fada yana yunƙurawa dan tashi amma sai.yaji wani mugun zafi ya.ziyarci hannunsa wanda hakan ya tabbatar masa xewa ya samu targane ne ko karaya,dakyar ya iya tashi, daidai lokacin mu ab ya fito da aminatu da take ta azabar kuka, da sauri ta koma bayan mus ab din tana cewa'daddy kasheni zai yi fa"wani mugun kallo mus ab din ya sakarwa Abby,yayin da shi Abby din ya dauke kansa ba tare da ya furta komai ba ya fice daga dakin zuciyarsa cike da mugun nufi akan aminatu.

Mus ab kuwa dole sai barin gidan yayi da aminatu dan fafur ta ce bata iya zama,amma fa sai da ta dauki book dinta wanda shi kansa mus ab din bai San sanda ta dauka ba,Nana ma sosai ta bashi goyan bayan ya bar gidan da aminatu dan abinda Abby yayi tun akanta ba karamin tsorata ta yi ba,dan ta dauka itama kashentan zaiyi,sam bata yi tunanin gayawa mus ab din marin da Abby yayi mata ba dan hajann bala I kawai zai tayar dan haka ta rabu dasu suka bar gidan.

Kai tsaye gidan sa na miyatti Allah gra ya nufa, ko da suka zo gidan sai da aminatu ta juyo ta kallesa ta ce"daddy Dan Allah kar ka kaini gidan da Abby zai iya ganoni"hannunta da yake cikin nasa kawai ya ɗan murza cikin sigar lallashi ba tare da ya iya cewa komai ba,gidan ba wani girma ne da shi ba cancan amma yana da tsari da burgewa,dan da abaya ne lokacin tana aminatunta da sai ta tsaya yawan magana kan ta shiga gidan,yana riƙe da hannunta suka shiga har cikin bedroom,kafin ya saketa yana dubanta cikin kulawa ya ce"babu wanda zai san kina nan ki Kwantar da hankalinki yanzu kije ki yi alwala ki yi sallah dan ko azhar bana jinkinyi,Ni kuma zan samo miki wani abu kici,kina jin yunwa ko"?ya karasa maganar da tambayarta yana shafa dan shafaffen cikinta,girgiza masa kai ta yi idanunta suna cika da hawaye,ɗauke hawayen yayi tare da nuna mata hanyar bathroom shi kuma ya juya ya fice tare da rufeta ta waje.

****

Kai tsaye Abby asibiti ya koma,gaba daya binsa da kallo su kayi saboda tashin hankali da damuwar da suka ganina tare dashi ,zama yayi tare da sanar dasu abinda ya faru bai boye musu komai ba,suma a take hankalinsu ya ya nunku cikinsu babu abinda yake sai kartawa,sun shiga cikin tunanin yadda zasu yi da mu ab tunda yanzu sun gano shine wanda yake rike da dukiyar aminatu kuma dama ita ce dalili na barin aminatu da rai da suka yi,dan haka yanzu kai tsaye zasu iya kashe aminatu in yaso sai su ji da mus ab ɗin,Abby da bai san batun fito da dan lardi ba suka sanar dashi kamar yadda. Zahida ta sanar dashi,shima ya gamsu amma ba kamar su ba dan acikin ransa akwai wani lissafi da yake yi.
Chapter 25 · 0% Book details