Sashe 35
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da suka dawo lokacin saura kwana uku auren SULAIMAN,a nan ne ya ɗebe su gaba dayansu ya kaisu gidansa da aka bashi a cikin wata unguwa me kyau da tsari sai dai anguwar akwai kananun talakawa masu rangwamen ƙarfi,tunda suka ga gidan sule sai suka tabbatar ashe duk buda hancin da suke masa wai su sunyi arziki aikin banza suke yi sai ranar suka gane cewa sule fa yayi musu nisan da tarar dashi sun tashi tsaye,saboda a ranar ne suka gano boyayyayun kadarorinsa da bankunan da yake amfani da su,sun dawo kauye cikin tashin hankali da tunanin yadda zasu yi su mallaki abinda yake hannun sule,kwatsam kuma sai wani abun baki cikin ya kuma faruwa, wato daurin auren sule da Nana Asma'u,ai Jamil saboda bakin ciki har sai da yayi kwanan asibiti,tunda ya fito kuma suka fara kulla wadda zata fishshesu,
MAFARIN arzikinsu ke nan handama kwace fili gonaye gidaje , cire zuciya da koda, shine abinda suka mayar halattacciyar sana ar su,daga nan kuma suka samu mata suka aura daidai da rayuwarsu wato yan gayu masu budedden ido,suma sai suka tare a cikin wannan anguwar da sule yake shi da matarsa da su Anne,duk da cewa akwai layi biyu tsakaninsu da layin da sule yake,
A hankali a hankali kauyen su sule ya koma kufai dan sun gaji duk sun gudu sun bar dukiyoyinsu dan kawai su tsira da rayuwarsu,hakan ba karamin farin ciki ya sanya aminan guda uku ba,take suka fara saka gwanjonsu suna sayarwa, a cikin haka ne kuma sule yayi bincike ya gano duk abinda suke aikatawa, ransa ya yi matukar ɓaci tare da yin Allah wadai da su har yana da nasanin barinsu zama a cikin kauyen,daga karshe yayi musu nasiha da tuna musu lahira,a lokacin nuna masa su kayi sun ji kuma sun yi nadama sannan da kansu zasu nemo ragowar mutanen da suka bar kauyen,musamman iyayen Nana da su ne wanda aka fara nema aka rasa, ya amsa musu ne kawai amma ba wai dan ya yarda da su ba,shi yasa ya ci gaba da bibiyarsu tare da sanya musu ido, dan yasha alwashin muddin ya kuma kamasu da lefi sai ya maka su a kotu,a wannan tsukinne kuma mahaifiyar Kabir itama ta koma ga mahaliccin ta, sai ya zama saura Anne kawai a manyan da suka rage musu.
Nana ta samu ciki, kar ka so kaga farin cikin da sule yayi har da su Jamil ma,daga nan aka shiga tattalin Nana har Allah ya sauketa lafiya ta haifi zakin santalelen yaronta me kama da mahaifinsa kamar an tsaga kara,ba karamin murna suke yayi ba dan alokacin sai da ya raba kujerar Makka kusan ashirin saboda murna da jin dadi,talakawan da suke kewaye da shi kuwa ai kaf dinsu babu wanda bai juyawa talauci baya ba, wannan halin sule ne ba sai lokacin Zakka yake fitar da dukiyarsa ba,ajininsa ne san kyautatawa, shi fa bai ki ya baka ya rasa ba, wannan ita ce zuciyar imani,sai da mus ab ya kusa shekara biyu a duniya sannan matansu jamil suka samu ciki,sai dai banda zubaida matar Garba,lokacin da Garba yake sanar dasu irin damuwar da zubaida ta yi , sai kawai Jamil ya bude baki ya ce" ka ce mata itama ta fito a matsayin me ciki kuma ta tabbata duk sanda zata fito cikin mutane ta sanya kwarya a cikinta,a lokacin Garba ya amsa ne kawai ba tare da ya gane manufar Jamil ta yin haka ba, sai dai sun ƙaddara cewa duk abinda Jamil zaiyi yana da manufa kuma ta karuwa a gare su shi yasa duk abinda ya ce suke yinsa kai tsaye,
Kwanci tashi asarar me rai, matar Kabir ce ta fara haihuwa bayan kwana goma matar Jamil ta sauka tana haihuwa ta ce ga garinku nan,cikin jini Abby ya dauki jaririyar ya dankawa Garba yana cewa"maza ka kaiwa zubaida daga yau wannan jaririyar yar zubaida ce da kai halak malak"cikin tsananin mamaki da rudewa Garba ya ce"me kake nufi Jamil?matarka fa ta mutu baka da tabbacin zaka kuma samun wasu yaran,ina ma lefin kace ta shayar da ita zuwa lokacin da za ka samu wata matar"dariya Jamil yayi tare da cewa kar ka damu abokina ai Ni ina da yaro mus ab shine Dana na kuma nasan Nana zata kuma haifa min wasu yaran dan haka kai kaje da wannan bamu da lokaci bana son kowa ya san wannan bayan mu ukun nan har matarka hudu kenan"sake da baki Garba ya bi jamil da kallo zuciyarsa cike da sake sake akan maganganunsa,to ya za ai matar sule ta haifa masa wasu yaran? sannan ya za a yi dan wani ya zama nasa ?" Dafa kafadarsa da aka yi ne yasa shi dawowa hayyacinsa, Kabir ne yayi masa murmushi tare da nuna masa cewa ya yi abinda Jamil ya sashi babu kome a ciki sai karuwa,jinjina kai yayi sannan yaja kafafunsa da suka yi masa nauyi ya fita daga dakin.
Kowa ya gama dauka cewa adawiya matar Abby ta mutu tare da jaririnta,anyi baki cikin rashi kuma an yi farin cikin samu,ran kwana bakwai Abby da kansa ya radawa yarinya suna zahida,sosai Abby yake jin matukar son zahida a ransa sai dai ya riga ya sawa ransa cewa dole sai ka sadaukar da wani abun kake samun wani,dan haka ya dauki hakurin rashin matarsa da yarsa na zuwa lokacin da ya kayyade wa kansa.
Jamil shi kadai yake ta shirinsa na ganin bayan sule,haka ta bangaren sule yana ta ci gaba da cigiyar iyayen nana da kuma bincike me kyau akan su Abby,Jamil bai sanar da su Garba shirinsa ba har sai da ya gama tsara plan dinsa daidai ta yadda ba zai samu wata matsala ba,kamar yadda suka saba sun bashi goyan baya tare da saka hannu wajen cika muradansu,
Jamil ya kullaci sule akan abubuwa da dama,tun na yarinta har zuwa girma,musamman yadda ya kwace masa iyaye da kuma arzikin da ya samu, wanda shi a ganinsa suke bai dace da samun wannan daukakar ba saboda shidin almajiri ne mara gata, amma sai gashi sule ne ya samu abinda shi ya kamata ace yana dashi,kudi ta hanya me kyau matar aure me kyau, sannan ga iyaye daga sama, kai ina ai gatan yayi masa yawa dan haka dole ya kwace komai dole komai ya dawo hannunsa mata kudi da iyayensa dole su dawo hannunsa,amma yasan hakan ba zata faru ba har sai idan sule baya raye, shi yasa ya yanke hukuncin turasa lahira,kafin shi ya turashi magarkamar da yake shirin kaisa,saboda yana sane da duk wani bincike da sulen yake yi akansu saboda ya samu damar maka su a kotu,shi Jamil yasan shirin sule akansu amma shi sule bai san abinda suke shirya masa ba,
A wata ranar alhamis ne,sule ya tashi da rashin kuzari inda ya dauki Nana suka fita ba tare da sanin kowa ba,sai bayan a wa daya suka dawo, itama nanan gaba daya jikinta a sanyaye yake,saboda abinda sulen ya gabatar mata dashi,dukkansu ranar basu wuni da kuzari ba,washe gari kuma ya shirya tsaf suka fito tare da nanan da take ta faman sauke hawaye, ji take kamar ta hanashi tafiyar da yake kokarin yi amma ba hali,gabanta faduwa yake sosai baran idan ta tuna maganarsa ta jiya me kama da wasiyya duk sai jikinta ya kuma mutuwa,da kuka da tashin hankali suka rabu da Nana da mus ab ɗansa daya tilo da yake matukar so.
Tun da ya tafi Nana ta kasa nutsuwa duk mintuna biyar sai ta kirasa taji ya yake,shi fa kansa ya fara yi mata dariya yana tsokanarta da cewa,ko dai takaba kike tsoro ne nanata naga duk kin daga hankalinki,kuka ta saka masa tana cewa "bana son wannan kalmar da take fitowa daga bakinka in dai akan kiran da nake maka ne ba zan kuma kira ba har sai kai da kanka ka kirani"daga haka ta katse kiran taa share hawayenda suka bata mata fuska, sannan ta fara kokarin kawo walwala saman fuskarta saboda kawar da hankalin mus ab.
A firgice nana tafarka tana laluben makunnin dakin, bakinta dauke da salati saboda mummunan mafarkin da ta yi,wayarta da ke kan bedsite drower ce ta fara kawo haske tare da ɗan ƙaramin sauti,cikin sauri ta dauki wayar ba tare da ta duba me kiran ba,dan a ranta yasan cewa sule ne kawai zai yi mata wannan kiran na cikin dare,sai dai a maimakon ta ji muryarsa sai kawai ta ji Muryar wani daban yana cewa,ke ce Nana Asma'u?"cikin rawar baki ta amsa da ey nice Ina me wayar me ya sameshi?"Hajiya kwantar da hankalinki dama cewa yayi ki yi hakuri kar kijisa shuru zuwa da safe zai yi kiranki"haka nan dan sandan ya ji ya kasa sanarwa da Nana halin da mijinta yake ciki saboda yadda yaji ta ba anutsewa kuma da alama ita kadai ce a inda take idan ya gaya mata komai na iya faruwa,zubawa wayar ido Nana ta yi zuciyarta na bugawa da saur da sauri kamar zata bullo ta fito,kasa komawa bacci ta yi , sai sallar da ta kwana tana yi akan Allah ya tsare mata mijinta a duk inda yake..........
[5/7, 7:09 PM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page51``*
Juya wayar dan sandan ya dinga yi a hannunsa na tsawon wasu sakanni kafin ya maida kiran kan sunan Abby da ya gani kafin kiran Nana,wanda yake nuna cewa shine mutum na biyun karshe da suka yi waya da sule,dama Abby a shirye yake tsaf jiran kiran kawai yake yi,hakan yasa ana kiransa suka dunguma suka yo wajen gawar da shi da mukarrabansa, suna zuwa suka samu har an rufe sule da likkafani saboda gaba daya fuskarsa ta yi damege duk sanin da kayi masa baka isa gane shi a wannan yanayin ba,haka suka kwashi gawarsa suka.tafi da ita,driver kuwa shi gaba daya ya kone ko makamashinsa ba a samu ba sai toka.