Sashe 24
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nana tana cikin kiran mus ab din, sai kawai ganin fitowar sa daga dayan daki tayi jikinsa sanye da kananun kaya wanda suka amshi jikinsa yayi wani irin kyau duk da cewa kana kallon fuskarsa a wannan karon zaka fahimci cewa yana cikin mood mara daɗi,sai kuma aminatu da take riƙe da hannunsa tana raɓewa a gefansa saboda tsoron zahida da yashigeta Farad daya,itama sanye take da bakar abaya wadda ya bata ta saka ba tare da ta san ina ya samota ba
Kallonsa kawai Nana take sake da baki dan bata taba tsammanin cewa yana ciki yana jin zahida ba,sai kuma yanzu ta fahimci dalilin wannan haukan ta zahida,Anne kuwa taɓe baki ta yi tare da cewa "gayyar tsiyar ashe duka suna ciki"babu wanda ya kulata dan zahida tuni hankalinta ya koma kan mus ab da aminatu da yake.kokarin fita da ita ba tare da ya tsaya ko Nana ya saurara ba kai tsaye mota ya saka aminatu Sannan shima ya shiga,ba su ankara ba sai ganin zahida suka yi ta fito da gudu hannunta rike da ƙatuwar wuka tana cewa"wallahi da naga wannan mummunar ranar gwara mu yi mutiwar kasko gaba dayanmu"Nana da ta biyo bayanta ce ta tayi saurin shan gabanta tana cewa "haba zahida idan hankali ya bata ai tunani shi yake nemoshi me yasa da hankalin ki amma zaki mayar da kanki mahaukaciyar dole?"wani mugun kallo zahida ta yiwa Nana kafin cikin kunar zuciya da tafasar ruhi ta ce"yi min shuru munafuka ai duk abinda ya faru ke kika jawo dan me zaki rabu dashi ya auri wannan tsinananniyar bakauyiya, to wallahi da ace Ni zahida na yi kishi da wannan abar gwara muyi mutuwar kasko gaba daya dani da ku".
Kafin ta karasa inda suke tuni mus ab ya figiotar dan da bata yi saurin matsawa ba tsaf sai ya takata,suna ficewa ta juyo kan Nana,cikin bakar zuciya ta nuna Nana da wukar hannunta ta ce"wallahi wallahi wallahi Nana ba zan hakura ba dole aminatu ta biya farashin zunubinta da abu mafi tsada a cikin rayuwarta"tana fadin haka ta yi cikin falon da gudu tana wani irin kuka kamar ranta zai fita, tana can tana yaƙin neman soyayyar mus ab ashe yana nan yana yana cin amanar ta,kai ita wallahi da zata ga bokan da yayiwa innawuro aiki akan mus ab da ita ma sai.ta je ya mata dan a yanzu babu wani abunda take buri a rayuwarta sama da samun soyayyar mus ab,sai dai kuma kash hakan ba zata samu ba,wankin hula ne yake neman Kaita dare, wani irin zafi ta ji zuciyarta na yi yayin da duhu ya mamaye ganinta su Nana basu ankara ba sai ganinta suka yi hif a kasa ta zube babu alamun numfashi a tare da ita.
*****
Saboda tsananin tsoratar da aminatu ta yi tuni ta sumewa mus ab ,jikinta kuwa ya yi zafi saboda zazzaɓin da ya rufe ta a dalilin jinin da goshinta yake zubarwa,tana jikinsa yake tukyin a haka tsaf fuskarsa take kuma sosai yayi kokarin daidaita nutsuwarsa domin a wannan lokacin nutsuwarsa ta fi komai muhimmanci,a haka suka ƙarasa ABM hospital,inda a take aka shiga bawa aminatu temakon gaggawa,cikin kankanin lokaci aka yi mata dressing a goshinta sai magani da aka bata saboda zazzaɓin jikinta,kanta yana saman cinyarsa a haka a ka gama yi mata komai ba tare da ya bari wani namiji ya taba ta ba,komai macece ta yi mata duk da cewar ba wai wani abu ne da ya danganci taba jiki sosai ba,bacci ne ya dauke ta amma kana kallonta kasan bana jin dadi ba ne,dan har firgita take yi lokaci zuwa lokaci,wayarsa ce ta fara kawo haske alamun kira na shigowa,daga wayar yayi tare da karawa a kunnensa ba tare da ya ce komai ba,shuru na tsawon minti daya kafin ya ce" ba zan iya barin inda nake ba yanzu amma zuwa anjima zan kiraka sai kazo ka sameni"daga haka ya dauke wayar yana gyarawa aminatu gashinta da ya leko ta cikin hular kanta.
****
Zubewar zahida yayi daidai da shigowar su Abby da gudu suka yo kanta, ba tare kuma da bata lokaci ba suka tarairayeta zuwa cikin mota,Nana ta bude zata shiga Abby ya dakatar da ita da cewa _ki koma kawai itama da an duba ta zamu dawo gidan ba zama zamu yi a asibitin ba in dai har babu wata babbar matsala",yana gama fadin haka ya shuge motar Alh Kabiru yaja abby kuma yana gefensa, sai daddy da yake tare da zahidar a baya,har suka isa gjk hospital basu tankawa junansu ba,suna zuwa likitoci suka yi kan oga kwata kwata Dr zahida me duniya,basu suka samu mutawa ba har sai da suka samu daidaitowar numfashin Dr zahida da yake tsakanin ƙirjinta shi bai fita ba shi bai koma ba,sosai suka kula da ita har ta farfaɗo.
Tana buɗe idanunta da fuskar Abby ta fara cin karo, rufe idamunta tayi ta kuma budewa dan ta tabbatar da cewa su din ne ba mafarki tayi ba,tabbatar da su din ne yasa ta fashewa da kuka tare da kama hannun daddyn ta tana cewa"daddy Abby mutuwa zanyi ku temaki rayuwa ta kada na mutu a sanadin mus ab da aminatu,Abby ku hakura da burinku na kan aminatu ku sadaukar da ita gare ni ma ana ku barni na kasheta da hannuna a kuma wannan lokacin ba na bukatar kara ganinta acikin rayuwata wannan alfarmar nake so ku yi min dan Allah daddy"Abby ne ya ce"wai zahida me yake faruwa ne dawowarmu kenan fa muka sameki cikin wannan yanayin?"take fuskarta ta kuma sauyawa har wani ja take yi saboda tsananin damuwa da kuka,cikin tsananin kukauryarta har ta fara dashewa ta ce"Abby mus ab ya cutar da rayuwata ashe duk halin da ake ciki a gidan nan auren aminatu yayi"what"suka hada baki wajen faɗa yayin da gumin fuska ya fara tsatstsafo musu sai kallon juna da suke yi tamkar wanda basu taba ganin junannsu ba sai.yau,cikin kakkarwar harshe Abby ya jefa mata tambaya da cewa"zahida me kike fada ne ko dai kwakwalwarki ta tabu ne bamu sani ba?"kanta kawai take girgizawa tana cewa wallahi daddy dama nasan baku sani ba tunda ku an san kuna so na ba zaku yarda da wannan auren ba,shi yasa bai gaya muku ba amma tabbas nasan da hadin bakin NANA munafukar mata kawai"ta karasa fada tana dafe kirjinta da take jin zai fashe saboda babbakar da yake yi tamkar ana rura wutar itace a cikinsa.
Juyawa Abby yayi a matukar rude da fusatar da basu taba ganinsa aciki ba,gaba dayansu jikinsu sanyi yayi,saboda sun san cewa watan cin kaniyarsu yayi, in dai har AMINATU tasan wani abu da ga cikin sirrinsu to tabbas mus ab ma zai sani,idan haka ne kenan littafin ma zata iya bashi, wannan tunanin da suka yi ne ya kuma tashin hankalinsu domin sun san muddin mus ab ya karbi littafin nan babin babbakar rayuwarsu ya fara dole su fara lissafin ragowar kwanakinsu a duniya ko cikin farin ciki,to wane farinciki ma ake batu, bayan tuni aminatu ta yi musu shinge dashi yanzu kuma jaruminta zai karasa rusa ragowar kwarin gwiwar da suke dashi na ci gaba da rayuwa kamar baya,jiri daddy ya ji zai yar dashi hakan yasa yayi saurin kama karfen gadon da zahida take kai tare da yin zaman dirshen a wajen,Muryar zahida yaji tana cewa "daddy Ina kuka kai ɗan ladi?ku fito dashi duk ma inda kuka kaisa domin ina bukatarsa hatta da ku zai muku amfani dan muddin mus'ab ya dawo ƙarƙashin ikona to babu abinda zai iya yi mana ko da agabansa zamu ci gaba da aikata duk abinda muke yi"gaba daya su biyun suka juya suna kallonta da alamar neman karin bayani,jinjina kai ta yi bayan ta basu labarin abinda boka ya faɗa mata.
*****
"Innalillahi wa inna lillahi raji'un"aminatu ta faɗa tana yunƙurawa a kiɗime, cikin mutuwarsa da baya rabi da ita a ko yaushe ya kamata ya maidata jikinsa yana tifa mata addu'a saboda fahimtar yayi mafarki tayi,"calm down"ya faɗa yana riƙe fuskarta domin samar mata da nutsuwa,kawar da kanta ta shiga yi tana kokarin tashi ,dan yanzu babu abinda take bukata illa ta ganta a dakinta tare da wannan littafin,ganin ya hanata tashi gashi babu wani karfi a jikinta saboda jinin da ta dan zubar,cikin haki ta bude baki tana cewa "daddy ka barni danjer gida na dauka littafin nan wallahi yanzu na kuma ganinsa yana jaddada min akan temakonsa da na yi alkawarin zan yi, kuma.yace ba zan iya taimakonsa ba har sai na bude littafin nan, to to kuma littafin yana can naga Abby ya dawo,,,,dan Allah daddy ka ɗauke littafin ka boye idan ya san Ni na dauka kasheni zai yi Abby mugu ne bashi da imani dan Allah dan Allah daddy ""ta fada tana fadawa jikinsa tare da kara karfin kukanta.
Shafa bayanta ya shiga yi kafin ya tausasa muryarsa da ta kuma yin laushi da zurfi irin ta mazan da suke a tsaye cak,ya ce"ki nutsu babu abinda zai faru yanzu zamu tafi gidan amma sai kin kwantar da hankalinki"rungumesa ta yi tana shigar da fuskarta cikin wuyansa tare da cewa daddy Ina jin tsoron Abby zai kashe Ni ne kamar yadda baba mahaukaci ya ce ya kashe shi"wani irin dum kirjin mus ab yayi cikin wani irin faduwar gaba ya dagata tare da daidaita mata rayuwa ya sanya mata mayafinta, sannan ya kama hannunta suka fita daga dakin da asibitin gaba daya.