← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 57

Sashe 21

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewa cikin dogon nazari da zuzzurfan tunani yasa baffa wuro kamo bakin zaren inda matsalarsa ta samo asali,tashi yayi tsaye yana ɗan dafe gefan cikinsa,cikin cije baki da karfin hali,sakatar gidan ya zare yana shirin fita, matarsa da motsinsa ya farkar da ita, ta yi saurin miƙewa tana riƙosa da fadin "ina zaka je cikin daren nan malam?"cikin kuka da rashin hankali ya ce"ki sake ni zanje wajen waɗan can azzaluman mutanen ne na tambaye su dalilin da yasa suka ci amanata a matsayina na mutumin da ya kasance yana tare da su yana musu duk yadda suke so,duk abinda suka saka ni sai nayi koda kuwa ya haɗa da kisan kai ne,amma ba su dubi girman amanar dake tsakaninmu ba suka rufe idanunsu suka zalunceni ta hanyar kwakulemun ƙoda ba tare da na sani ba,kuma suka haɗa ni da kudin da ko rabin fansar lafiya ta basu kai ba bare na ƙodar da suka cire,gashi sanadin haka dayar itama ta kamu, kuma idan har ban samu kuɗin siyan wata ƙodar ba to sai dai ina ji ina gani na mutu,kai wallahi zalunci bai yi ba,gashi nan tun kan aje ko ina na fara ganin sakamakon hakkinsu aminatu da hakkin amanar ubanta da naci"ya karasa maganar tare da rushewa da kuka,cikin karfin hali matar ta kamo shi ta mai dashi ciki tana cewa "kayi hakuri ka rabu dasu muji da matsalar dake gabanmu idan kuma har kaje ka samesu to kasan kasheka zasu yi ko?dan haka kawai ka barwa Allah hanya daya ce da kai ta gyara lefukanka a yanzu ita ce neman yafiyar wanda ka cuta ka kuma yi ƙoƙarin ganin ka ciresu daga halakar da ka kaisu"wannan shine burina a yanzu koda zan mutu ina fatan Ubangiji ya a ra min lokaci domin ganin bayansu Alhaji Garba".

"""""Motsin da ta danji daga bayan window ta ne yasa ta, ta yi saurin maida littafin inda yake,tuni jikinta ya fara rawar tsoro,dan ita fa gani take Abby ya ganta rabuwa kawai yayi da ita domin ganin abinda take shirinyi masa da ajiyar da ta dauko wadda ita kanta bata ce ga abinda yake ciki ba,kuma bata san dalilin da yasa take son budewa ba,jin anata taba kofar yasa ta kuma rikicewa tare da saurin hade bayanta da bango tana kallon kofar da idanunta da suka fara zubar da hawaye,ji ta yi kamar Muryar mus ab yana cewa pls ki bude nine mus ab"Jim ta yi tana juya muruar da yaddaya ambaci mus ab din a ranta,girgiza kanta ta yi don kuwa ko a mafarki taji muryar mus ab sai ta ganeta bare kuma a zahiri,cikin kasa da murya aka kuma cewa ki bude mana aminatu nine fa"kamar yana kallonta haka ta ci gaba da girgiza kanta tana kuma jin cewa a ranta wannan ba mus ab ba ne wata ƙila ma abby ne ya canja murya zai yi mata wayo, wannan tunanin da ta yi yasa ta jin wani sabon tashin hankalin yayin da zuciyarta ta farabugawa da karfi tamkar zata faso kirjinta ta fito,cikin hanzari ta koma ta sakewa littafin waje dan tasan ko da zai shigo shine farkon abinda zai fara tabayarta,ita kuma koda kasheta zai yi bazata taba bashi littafin nan ba har sai ta ga abinda ya kunsa.

A gefen isma kuwa abin yazo masa a bazata domin bai taba tsammanin zai sha wahala wajen shiga dakin aminatu ba,da yasan haka ne da da wuri zai ta naji safaya key,sai dai kuma ba ko wanne key ne yake yiwa kofofin gidan ba saboda tsananin security dinsu,ya san cewa yau dai ta wuceshi amma ji yake kamar kar ya bar wajen saboda shi kadai yasan abinda yake ji,to amma fa bari wajen ya zama dole saboda ko da yaushe wani zai iya ganinsa, wannan tunanin ya sashi barin wajen zuciyarsa baki kirin da jin haushin rashin biyan bukatarsa.

Yana barin wajen MUS'AB din gaske ya karaso tare da yin knocked din ƙofar,cikin nutsuwa wanda tashin farko aminatu ta dauke wuta daga sheshshekan kukan da ta fara saboda yadda lokaci daya bugun zuciyarta ya sauya a karo na biyu da ya kuma yin bugun tare da yin magana sai gaba daya gaɓoɓin jikinta suka yi sanyi take ta fara jin sauyi a gaba daya yanayinta muryarsa da ta ji ya kuma tabbatar mata da cewa shi din ne yanzu da gaske,to amma shi din wancan waye? Abby din ne ko kuma wani daban?sautin takunsa da ta ji yana juyawa da barin wajen shi ya dawo da ita hayyacinta ta nufi kofar cikin wani irin zafin naman da bata taba sanin tana dashi ba,bude kofar ta yi lokaci daya tana bin bayansa da ɗan karamin gudu da bai wuce taku daya da rabi ba ta kamo shi,cak ya tsaya tare da sauke boyayyar ajiyar zuciya yana mai sanya hannunsa saman hannunta da ya zagaye cikinsa yayi masa zobe, a gadon bayansa ta kwantar da kanta tana maida numfashi tamkar wadda ta yi gudun ceton rai,cikin nutsuwarsa da yanayinsa na kamewa da BASARWA ya juyo da ita gabansa suna fuskantar juna,dago kanta ta yi tana kallonsa da idanunta da suka kuma girma saboda kasancewa cikin kuka da damuwa,zata yi magana yayi saurin girgiza kai tare da jan hannnunta, da sauri ta kwace hannunta tare da komawa ta rufe dakin har da cire key din sannan ta matso kusa dashi tana kallonsa kallon farko a matsayinsa na dan birninta,bacin rai sosai ya hango a cikin idanunta hakan yasa bai tsaya ba ya kuma jan hannnunta ta suka bar wajen gaba daya.

*****

Lokacin da su zahida suka ƙarasa bukkar bokan ba karamin farin ciki tayi ba,domin sai da hakan ya bayyana akan fuskarta, ji take tamkar ta samu mus ab ta gama,ko da suka shiga ciki sai Anita ta fito acewarta zahidar na bukatar sirri,binta da kallo zahidar ta yi tana jin wani abu me kama da aminci akan anitar a karo na farko saboda wannan abun da ta yi mata,bokan ne ya katse ta da cewa "kema kinga abinda na gani kenan a tare da kawar ki?"da sauri zahida ta dawo da kallonta kan bokan tana cewa kamar yaya?"wani kyalle ya dauko ya mikawa zahidar yana cewa euba nan ki ga Ni" cikin sauri zahidar ta girgiza kanta tana cewa "pls boka duk abinda za ka yi kayi zan baka duk kudin da kake bukata amma dan Allah kar ka nemi na taba wani abu a wajen nan saboda shi kansa zaman da nayi a kyankame nake shi yasa ban saki jikina ba,ba dan ina son mu ab ba da babu abinda zai kawo Ni wajen nan dan Ni sam bana yarda da irinku ,a wannan karon ne kawai naji na yarda kuma na gamsu cewa kai zaka bani mafita,saboda abinda ya faru a wancan karon,dan haka kayi min komai saboda kudina kuma ka sani cewa banzo wajen nan akan ko wace irin bujata ba sai buƙatar mijina da nake ya dawo hannunna karkashin iko na ya zama nice masarrafin rayuwarsa"shuru ta yi tana gyara tsuguno da ta yi a wajen, baki da matsala kuma nada duk abinda ya kawo ki dama wannan kyallen na baki shi ne domin ance gani ya kori ji,to amma tunda kin bani wuka da nama zan yi komai yadda kike so sai dai sharadin biyan bukatarki yana tare da majanuninki wato dan ladi me wanki"kallon mamaki da tashin hankali zahida ta yi masa, kafin ta ce "mene amfanin sako dan ladi a cikin wannan batun kuma?"dariya boka ya sheƙe da ita sannan ya buga kasa yana wasu surutai kafin ya gama ya dago kansa yana wani hade rai da muzurai ya ce"dole ne sai kin nemo dan ladi kafin burinki ya cika saboda asirin jikinsa yana daf da karyewa kuma muddin kika bari yakarye yana nesa dake to aikin da muke yi akan mus ab ba zai taba yuwu ba,dan haka kije ki fara naki aikin kamar yadda nima zan fara nawa yanzu, sannan abinda kike gudu ba zai faru ba saboda zamu toshe duk wata hanya da asirinki zai iya tonuwa a wajan mus ab,har zuwa lokacin da zamu kammala aukinmu AKANSA ".

Sai alokacin zahida ta numfasa tsoron dake dankare a kirjinta ya ragu,duk da cewa tana cike da tunanin hanyar da zata bi dan fahimtar da su Abby dan su yarda su saki dan ladi da kuma tsoron abin da zai biyo baya,sai dai kuma kwarin gwiwarta yana ga tabbacin samun biyan buƙatarta,dan haka ta cake masa kudi duk da ya ce da ita ta bar kudinta har sai an kammala aiki result ya fito,sai dai ba ta sauraresa ba ta fito daga bukkar ta samu Anita tana ta zabga gyangyadi a mota,bata tashi anitar ba da kanta ta shiga ta ja motar suka dauki hanyar barin kauyen.

****

Kai tsaye bedroom dinsa suka shiga,suna shiga ta fincike hannunta daga nasa tana kallonsa cikin jin haushi da takaici,shafa fuskarsa yayi yana ɗan basarwa, bai ce mata komai ba ya wuce ya shiga bathroom Jim kadan ya fito ya sameta a inda ya barta sai dai a yanzu kuka take yi sosai fuskar ta duk ta yi ja,matsawa yayi daf da ita har jikinsu na gogar juna, kasa magana yayi sai daga can ya kokarta ya ce"ar U ok?"wani irin haushu ne ya kuma turnuketa har bata san lokacin da ta shiga kai masa duka akan mayalwacin kirjinsa ba.
Chapter 21 · 0% Book details