← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 57

Sashe 38

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daddy Garba ne yayi gyaran murya tare da fara magana kamar haka,"Ni dai a nawa nazarin gani nake mu nemi wani matsafin tunda sunduki ya gaza ƙarshe dai tasa ta ƙare ko ya kuka gani?"ya fada yana dubansu dan jin amsoshinsu da kuma yadda zasu karbi shawarar tasa,girgiza kai abba Kabir yayi kana yace"gaskiya ku hakura da batun mutanen nan dan Ni gaskiya abinda ya faru da sunduƙi yasa naji rashin yadda akansu, dan ƴadda àbín ya kasance ya bani tsoro matuka , kun dai ina dai kura zàta yi maganin zawo to kantà ya kamata ta fara yiwa kuna ganin yadda sunduƙi ya ƙasance ya kasa yiwa kansa taimakon kome aƙan halin da yake ciki kun ga kuwa taƴaya mu zai iya taimaka mana,shi yasa na dawo daga rakiyarsu idan zamu nemawa ƙanmu mafita mu nema idan kuma muka nace sai matsafa ne zasu taya mu to wallàhi muna cikin matsala babba,dan wallahi ni yanzu ma nake jin cewa kamar duk abinda ya ke fada mana karya ne"sai a nan Abby ya numfasa tare da amsar maganar da abba Kabir yake yi da cewa,"tabbas ƙabir maganarka na kan hanya amma fa duk a binda ßunduki ya fada gaskiya ne,ƙawai dwi wannan abin da ya faru dashi ne yasa muka gane cewa ba zai iya taimakonmu akan wannan bala in da muke ciki ba,kunga kenan dole mu sanja salo da taku muyi da karfin mu da dabararmu domin ceton dukiyarmu dà rayuwarmu da kuma gujewa fadawa babbar masifàr TALAUCI wadda shine asalin fadawarmu wannan hanyar"daddyn zahida ya ce "haka ne maganarku amma ni nasan duk abinda ya faru mu muka jawa kanmu dan kuwa da ace mun yi koyi da sule mun tashi mun nema kuma mun yi haƙuri da kaɗan da yanzu mun zama kamarshi,àlókacin nan nasha faɗa muku cewa muma mu dinga gwada yan dabarun da yake yana samun na kashewa ko dako ko aikin leburanci ko wanki da guga ko garuwa, amma ku sài kuka nuna mun fi karfin yin irin wannan sana o in,sabodà alokacin tuni zuciyarmu ta riga ta mutu kuma mun sawa ranmu cewa wannan kananun sana o in ba zasu kawo mana arziki dare daya kamar yadda muke so ba,to kuma abin mamaki sai gashi da sana o in da muka raina din da su sule yayi arziki har ya kere mu dan na tabbata da cewa idan sule bai fi mu ba to muma ba za mu fishi ba, yanzu dai ga abinda girman kai da rainuwa suka jawo mana"yw kare maganar cikin rauni kamar wamda ya fara yin nadamar ABUBUWAN da ya aikata.duk shuru su kayi ba tàre da sun ji haushin maganar Garba ba saboda sun san gàskiya yà fada to amma ya su kayi dole sai ta wannan hànyar ne zasu yi àrzikin amma yanzu tundà sun samu abinda suka samu zasu iya ajiye komai àmma fà sai bayan sun ga bayan makotansu dan kuwa duk wanda yake son sanya shi cikin bala i da wahalar TALAUCI wallahi sai sun kawar da shi a duniya koda ya haɗa da mus ab dinne,tunaninsu daya ne dan haka suka ɗago suka kalli juna a tare tare da jinjina kaii.
Abby ne ya gyara zama tare da cewa,"yanzu dai duk ba wannan ba, me ye mafita?"Kabir ya ce "ai kai muke sauraro tunda kai ne uban tafiya kasan tun muna yara kai ne me kawo shawara mu kuma mu bi"cikin jin dadin maganar abby ya ɗan murmusa kana ya dora da cewa "idan har muna son dakatar da duk abinda yake faruwa to fa lallai sai mun samu kan mus ab ma ana dole sai mun karbe duk wata sheda dake hannunsa na farko dai littafi sai kuma camara da kuma takardun da anita ta debo,duk da nasan cewa ba su kadai ba ne amma wann6sune masu muhimmanci a wajen mu bamu da matsala ta bangaren shedun mutane tunda dan ladi yana hannun mu,waccan matar kuma har yanzu baku san inda take amma fa ji a raina tana tare da wancan tsinannan yaron,kun ga kenan idan har muka yi garkuwa da abu mafi soyuwa a gareshi duk zamu fanshi kanmu"abba kabir ne yayiwa Abby wata junjinar ban girma kafin ya ce "wannan shawara ta yi sosai ma kuwa sai dai kuma kasan waccan aljanar yarinyar ce kadsi zamu sace mus ab ya gigice gashi kuma bamu da zarrar dauke aminatu na farko dai itama aljanar kanta ce sannan kuma tana tare da mus ab wanda shima wata babbar kariya ce a gare ta"wata banzar dariya Abby yayi tare da jingina da kujerar da yake kai, yana cewa"idan har kun amince da shawara ta to ku zuba min ido ku bi ni kuga yadda wasan zai kasance"ya fada yana dora hannunsa akan table din da yake gabansa,babu mata lokaci daddy Garba ya dora nasa a saman na abby sannan shina Abba Kabir ya dora nasa.daga nan suka mike kowa ya dauki mota daya daga cikin motocinsu da suke zube a gidan kowa ya nufi hanyar gida.

Tana ajiye littafin ta muke ta shiga bathroom ta dauro alwala tana cikin sanya hijab ya shigo hannunsa dauke da leda me tambarin zababs restorent, kowane fuska ta yi tana kallonsa cikin tuhuma,sarai ya gane me take nufi amma sai ya basar ya wuce ya ajiye ledar shima ya fada bathroom din Dan dauro alwalar magriba,tsayawa ta yi tana jiransa fuskarta kuwa har yanzu a shagwabe take,yana fitowa ya ja musu sallar bayan sun idar suka yi addu'ar su da karatun shafi Daya na alkur ani,daga nan ya janyo ledar ya bude ya dauko mata abincin da yake ciki tare da budewa, spoon ya dauka ya shiga bata abaki bai kyaleta ba har sai da yaga ta kawar da kai daga nan ya bata madara tasha, sannan shima ya dan ci kadan dan baya jin text din bakinsa ko kaɗan, yana ajiyewa yaga ta maida hannunta cikin abincin ta kuma debowa bakinsa ta kai tana yi masa alamun haaa irin yadda ake wa yara dai,kafada ya makale alamun ya a'a,turbune fuska ta yi ta kuma dauke hannunnata, dole haka ya bude bakin ta zuba masa abincin,loma daya biyu a ta uku ya rike hannun tare da lashewa, karkatar da kanta ta yi kafin cikin sanyin murya ta ce"Daddy ina son ganin Nana"jan ta yayi suka miƙe tsaye bai yi magana ba sai hannunta da ya kama suka shige bathroom,yana ƙoƙarin cire mata kaya dan ta samu ta yi wanka ya fara amsa mata dan janye hankalinta,Nana tana lafiya Bamu jima da yin waya ba itama innswuro suna lafiya babu wata damuwa"ta gansu da abinda ya fada amma a bangaren Nana sai take jin faɗuwar gaba haka nan take ji kamar akwai abinda yake shirin faruwa,sanyin ruwan da ta ji a jikinta ne yasa ta jan ajiyar zuciya me sanyi,ware manyan idanunta ta yi kafin kuma ta yi wani irin tsalle ta rungumesa tana girgiza kanta tare da dukan kirjinsa, kana ta ce"Daddy mintinanka nawa kana kallo na wannan ina da ina ka kalla?"uhum ya fada yana son rabata daga jikinsa,ganin taki yarda yasa shi cewa"dago na nuna miki abinda na gani"rashin wayo irin na aminatu tuni ta dago kanta tana baza ido taga abinds ya gani ɗin,da wannan damar yayi amfani ya hade bakinsa da nata, ya kuma zura hannunsa daya ya kewaye kugunta,daya hannun kuma ya dauki sabulu ya shiga murza mata ajikin...

Kai tsaye Abby bangaren Nana ya wuce,yana daf da shiga dakin sai ya ji kamar ana magana hakan yasa ya ɗan dakata,"kayi hakuri ba wai na ki waiwayar dukiyar mus ab Dan ina sane ba ne sai dan bana hayyacina kai na ma manta da Ni wace ce,amma yanzu in sha Allah kome ya zo karshe me abu ya kawo girma da hankalin da zai iya rike dukiyarsa dan haka zan sanar dashi kome, tunda shi kansa bai san komai ba,"bum ta ji an bankado kofar an shigo,tana daga ido ta ga abby tsaye yana sheka mata wani irin kallo,karasowa ya fara yi gabanta hakan yasa ta yi saurin goge nomber da ta yi kira, tana mai ja da baya dan gani ta yi abby ya dawo mata asalin jamilun da ta sani.........

8064537048

0pay

Fatima yushau adam

500 only

Zahra✍️
[5/10, 12:14 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page53``*
Chapter 38 · 0% Book details